AFIRKA
1 minti karatu
Shugaba Mahama na Ghana ya ba da umarnin bincike kan cinikin filayen ƙasar
Mista Mahama ya nuna damuwa game da kasancewar mace ɗaya tilo a cikin sabbin shuwagabannin hukumar da aka rantsar.
Shugaba Mahama na Ghana ya ba da umarnin bincike kan cinikin filayen ƙasar
Shugaba John Mahama na Ghana / Getty
3 Satumba 2025

Shugaba John Mahama na Ghana ya bai wa Ma’aikatar Filaye da Albarkatun Ƙasa, tare da hukumar da ke kula da filaye su gudanar da bincike nan take kan duk filayen gwamnati da aka bayar ko ba da aro ko kuma aka sayar, musamman tsakanin shekarar 2017 zuwa shekarar 2024.

Da yake magana wajen bikin rantsar da shugabannin hukumar filaye ta ƙasar a ranar Talata, shugaban ya ce za a soke duk wani cinikin fili da aka bankaɗo, kuma filin zai koma hannun gwamnati kamar yadda dokata ta tanada.

Ya ƙara da cewa kwamitin sayar da filayen gwamnati ya riga ya fara aiki kuma zai miƙa sakamakon bincikensa nan ba da jimawa ba.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ya ɗauke takunkumi kan cinikin filayen gwamnati na wucin gadi.

Ya jaddada cewa daga yanzu, duk filayen da aka bayar ko aka ba da aronsu ko kuma aka sayar dole a yi ƙeƙe da ƙeƙe a cinikin a kuma sa ido sosai.

Mista Mahama ya nuna damuwa game da kasancewar mace ɗaya tilo a cikin sabbin shugabannin hukumar da aka rantsar.

Ya yi kira da a ɗabbaka dokar da ta ware wa mata kashi 30 cikin 100 na kowace hukumar gwamnati.   

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us