DUNIYA
2 minti karatu
Koriya ta Arewa ta yi gwajin 'sabbin' makamai biyu na kare sararin samaniya
Rahoton KCNA bai yi cikakken bayani kan sabbin makaman ba, sai dai kawai ya ce "makaman suna aiki ne da sabuwar fasaha ta musamman.
Koriya ta Arewa ta yi gwajin 'sabbin' makamai biyu na kare sararin samaniya
An jima ana zaman doya da manja tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu / AP
24 Agusta 2025

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya jagoranci gwajin harba sabbin makamai masu kare sararin samaniya guda biyu, kamar yadda kafar yada labarai ta gwamnati ta sanar a ranar Lahadi, bayan Pyongyang ta zargi Seoul da tayar da tarzoma a kan iyaka.

Gwajin harba makaman, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya nuna cewa sabbin tsarin makaman suna da "ƙwarewar yaki mai inganci," in ji rahoton kamfanin dillancin labarai na Koriya (KCNA).

Rahoton KCNA bai yi cikakken bayani kan sabbin makaman ba, sai dai kawai ya ce "makaman suna aiki ne da sabuwar fasaha ta musamman." Har ila yau, ba a bayyana inda aka gudanar da gwajin ba.

"Gwajin ya tabbatar da cewa fasahar sabbin makaman guda biyu tsaf za su kakkaɓo duk wasu hare-hare ta sama," in ji KCNA.

Rundunar Sojin Koriya ta Kudu ta ce a ranar Asabar ta harba harsasai na gargadi kan wasu sojojin Koriya ta Arewa da suka ƙetare iyakar da aka tsaurara tsaro sosai tsakanin kasashen biyu a ranar Talata.

Kafar yada labarai ta Pyongyang ta ruwaito Laftanar Janar na Sojojin Koriya ta Arewa, Ko Jong-chol, yana cewa wannan lamari "shirye-shiryen tayar da hankali ne da aka yi da gangan."

"Wannan wata sabuwar matsala ce mai tsanani ne wadda ba makawa za ta jefa yanayin yankin iyaka da ke kudanci cikin wani yanayi da ba za a iya shawo kansa ba, inda dakaru da yawa ke fuskantar juna," in ji Ko.

Sabon Shugaban Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung, ya yi alkawarin inganta dangantaka da Koriya ta Arewa mai makaman nukiliya tare da gina "aminantaka ta soji," amma Pyongyang ta ce ba ta da sha'awar kyautata dangantaka da Seoul.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us