Ministan Tsaron Ghana Edward Omane Boamah da Ministan Muhalli, Kimiyya da Fasaha Ibrahim Murtala Mohammed sun rasu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu tare da wasu mutum shida.
Babban hafsan hafsoshin kasar Ghana Julius Debrah ya sanar a ranar Laraba cewa helikwaftan ya yi hatsarin ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Obuasi da ke kudancin Ghana daga Accra babban birnin kasar.
Hadarin ya afku a gundumar Adansi Akrofuom da ke yankin Ashanti mai tazarar kilomita 270 a arewa maso yammacin Accra.
Jirgin ya kama da wuta, inda har yanzu ba a san musabbabin hatsarin ba.
Manyan jami'an gwamnatin sun yi tafiyar ne don su halarci taron ƙaddamar da shirin haƙo ma'adinai na hadin gwiwa.
Rundunar sojin Ghana ta sanar a safiyar yau Laraba cewa jirgin mai saukar ungulu na rundunar sojojin saman Ghana ya tashi ne da misalin karfe 9:12 na safe agogon kasar, amma jim kadan bayan hakan sai aka daina jin ɗuriyarsa.
Jirgin dai yana ɗauke da ma'aikata uku da fasinjoji biyar, ciki har da ministocin Ghana biyu da kuma tsohon Ministan Noma Mohammed Muniru.