GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Abin da muka sani game da sabuwar tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza da Hamas ta amince da ita
Hamas ta karɓi sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60 da kuma sakin mutanen da ake garkuwa da su.
Abin da muka sani game da sabuwar tattaunawar tsagaita wuta ta Gaza da Hamas ta amince da ita
Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, yana halartar taron manema labarai a ziyararsu zuwa wurin binciken Rafah tsakanin Masar da yankin Gaza, 18 ga 2025. / AP
18 Agusta 2025

Hamas ta shaida wa masu shiga tsakani cewa ta amince da sabon daftarin tsagaita wuta a Gaza, bayan fiye da watanni 22 na yakin da Isra'ila take yi a zirin, kamar yadda wani jami'in ƙungiyar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar 18 ga Agusta.

Masu shiga tsakani na ɓangaren Hamas a birnin Alkahira sun karɓi sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutan ta tsawon kwanaki 60 tare da sakin waɗanda aka kama a rukunai biyu, kamar yadda wani jami'in Falasɗinu ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Tayin yana matsayin tsarin yarjejeniya don fara tattaunawa kan tsagaita wuta na dindindin," in ji wani jami'in a ranar Litinin, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Tun da fari majiyar ta ce “Hamas za ta gudanar da shawarwari a tsakanin shugabancinta" da kuma tuntubar shugabannin sauran ɓangarorin Falasɗinu don nazarin tayin da masu shiga tsakani suka gabatar".

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke shirin fara mamayar ƙasa a birnin Gaza.

Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da ƙungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa mamayar Isra'ila a Gaza za ta haifar da ƙaura da tilasta wa dubban Falasɗinawa barin gidajensu.

Tayin ya samu amincewar gwamnatin Trump, wadda aka gani a matsayin dabarar siyasa daga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu don tabbatar da kwanciyar hankali a gwamnatinsa ta hanyar faranta wa Ministan Kuɗi Bezalel Smotrich da Ministan Tsaro na Ƙasa Itamar Ben-Gvir rai.

Kwanan nan Smotrich ya yi barazanar yin murabus bayan Netanyahu ya yi ikirarin cewa Isra'ila tana ba da damar agajin jinƙai shiga Gaza – duk da manufofin yunwa da aka ƙirƙira da gangan wanda ya haifar da yunwa mai tsanani a wannan yankin da aka killace.

Sai dai Smotrich ya janye barazanar tasa a ranar Litinin. Netanyahu ya gayyaci Smotrich da Ben-Gvir zuwa taron majalisar ministoci bayan an cire su daga yanke shawarar bayar da damar shigar da agaji mai iyaka zuwa Gaza.

A makon da ya gabata, ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu ta ce wata babbar tawaga tana Alkahira don tattaunawa da jami'an Masar kan ƙoƙarin tabbatar da tsagaita wuta mai wahala a wannan yaƙin, wanda yanzu ya shiga wata na 23.

Qatar, Amurka da Masar suna cikin waɗanda ke shiga tsakani tsakanin Isra'ila da Hamas. Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, yayin ziyarar da ya kai kan iyakar Rafah da Gaza a ranar Litinin, ya ce "a halin yanzu, akwai tawagogin Falasɗinu da na Qatar a ƙasar Masar suna aiki don ƙara ƙoƙari don kawo ƙarshen kisan gilla da yunwa."

"Muna ƙin duk wata ƙaura ta Falasɗinawa daga Gaza," in ji Badr Abdelatty a wani taron manema labarai yayin ziyarar da ya kai kan iyakar Rafah tare da Firaministan Falasɗinu Mohammad Mustafa.

A makon da ya gabata, Abdelatty ya ce Alkahira tana aiki tare da Qatar da Amurka don cim ma tsagaita wuta na kwanaki 60 "tare da sakin wasu waɗanda aka kama da kuma wasu fursunonin Falasɗinu don bayar da damar agajin jinƙai da na lafiya zuwa Gaza ba tare da wani cikas ba."

Masar ta kuma jaddada goyon bayanta ga ƙoƙarin diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Gaza, tana mai jaddada buƙatar ci gaba da tattaunawa da za su kai ga mafita.

Alkahira ta yi gargadin cewa ci gaba da tashin hankali da maganar faɗaɗa burin ƙasar Isra'ila na iya lalata kwanciyar hankali a yankin da kuma tsawaita rikicin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us