Mutane a ƙasashen Musulmai sun yi bikin Maulidin Annabi, wato murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), ta hanyoyi daban-daban bisa aƙidunsu.
A ƙasashe kamar Turkiyya, Falasɗinu, Masar, Somaliya, Iraƙi da sauran wurare, an yi tarukan Mauludi ta hanyoyi da dama, inda wasu suka gabatar da addu'o'i da lakcoci ko tattaki don murnar wannan rana mai muhimmanci.
Ga wasu daga cikin hotunan yadda bikin Maulidin ya kasance:
Turkiyya
A biranen Ankara, Istanbul da sauran wurare, Musulmai sun taru don yin addu'o'i duk don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Falasɗinu
Duk da tsananin mamayar Isra'ila, Falasdinawa ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen murnar wannan rana, inda suka tafi Tsohon Birnin Ƙudus a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, don yin biki a Masallacin Ƙudus.
Masar
Musulmai Sufaye a Masar sun cika titunan birnin Alkahira da sauran manyan yankuna don murnar wannan rana ta hanyar al'adunsu na Sufanci, wanda ya haɗa da rera waƙoƙin addini.
Yemen
Dubban mutane sun yi tattaki a babban birnin Yemen, Sanaa, a wani biki na gangamin murnar tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Somaliya
A Somaliya, mutane sun hau dawaki suna ɗaga tutoci don murnar wannan rana a babban birnin ƙasar, Mogadishu.
Iraƙi
Mutanen Iraƙi ma sun yi bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), inda suka yi addu'o'i tare da yin kaɗe-kaɗe a matsayin hanyar murnar wannan rana.
Siriya
Mutanen Siriya sun shirya kayan zaƙi na gargajiya, Mlabas, a yayin bukukuwan da za a yi a Birnin Tsohon Dimashƙ.