AFIRKA
2 minti karatu
Nijar ta saya wa rundunar tsaron ƙasa da ‘yan sanda kayayyakin aiki na CFA biliyan 1.5
Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewar Soumana ne ya tarbi kashi uku na kayayyakin da aka kawo.
Nijar ta saya wa rundunar tsaron ƙasa da ‘yan sanda kayayyakin aiki na CFA biliyan 1.5
Kwamandan na soji ya ce da kuɗin ƙasa aka sayi kayayyakin kuma 'yan kwangilan ƙasar ne suka kawo kayayyakin / ANP
19 awanni baya

Babban daraktan da ke kula da kayayyaki a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Tsaron Jama’a ta ƙasar Nijar, Kwamandan soji Hamani Soumana ya karɓi kayayyakin CFA biliyan 1.5 da aka saya wa rundunar tsaron ƙasa da na ‘yan sandan ƙasar ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya rawaito cewar Soumana ne ya tarbi kashi uku na kayayyakin da aka kawo.

Kaso na ɗaya na kayayyakin wanda ya ƙunshi kayayyakin gyara motoci da kuɗinsu ya kai CFA miliyan 600, an sayo su ne saboda motocin rundunar tsaron ƙasa.

Kaso na biyu na kayayyakin kuwa ya ƙunshi kayayyakin gyara motocin cibiyar horarwa na Rundunar Tsaron Ƙasa ne, kuma kuɗin kayayyakin ya kai CFA miliyan 400.

Shi kuwa kaso na uku na kayayyakin ya ƙunshi kayayyakin sakawa (ɗamarori da huluna da kayan sarki da takalma da sauransu), wasu abubuwa da aka keɓe wa waɗanda za a ƙara wa girma cikin ‘yan sandan, wanda kuɗinsu ya kai CFA miliyan 500. 

Yayin da yake karɓar kayayyakin da aka saya da kuɗin ƙasa kuma wanda ‘yan kwangilar Nijar suka aiwatar, Kwamanda Hamani Soumana, wanda ya yi magana a madadin Ministan da ke kula da Tsaron Ƙasa, Janar Mohamed Toumba.

Ya nanata cewa "Shugaban Majalisar Ceton Ƙasa (CNSP), da Shugaban Ƙasa Janar Abdrourahamane Tiani da Mista Ali Mahamane Lamine Zeine, Firaminista kuma Ministan Tattalin Arziƙi da Kuɗi sun ba ba fifiko ga samar wa dakarunmu kayayyaki wajen ƙara musu ƙarfin yaƙar abokan gaba ta kowace hanya."

Ya ƙara da cewa "a lokacin watannin da suka wuce a ƙarƙashin Ministan Ƙasa [mai kula da tsaron jama’a], an yi irin wannan bikin a cikin zauren ofishin rundunar tsaron ƙasa da na ‘yan sanda domin karɓar motoci da tayoyi da kayayyaki."

"A wannan karon, an karɓi kayayyakin gyaran motocin rundunar FSI ne," in ji shi.

Hamani ya yaba wa Ministan Tsaron Jama’a game da yadda yake ruɓanya gine-gine da yadda ake sayen kayayyaki domin dakarun.

Ya yi kira ga shugabannin rundunar tsaron da ‘yan sanda su yi amfani da abubuwan da aka saya yadda ya dace.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us