Firaminista kuma Ministan Kuɗi na Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Asusun Ba Da Lamuni na IMF da ta kai ziyarar aikin ƙasar Nijar ranar Laraba domin tattaunawa kan harkokin kuɗi da tsimi da tanadi.
Tawagar ta ƙwararru ta kai ziyarar ne a ƙarƙashin jagorancin Ms. HA VU, babbar masaniyar tattalin arziki a ɓangaren kuɗi da haraji na asusun a IMF.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar, ANP ya ambato wata sanarwa na cewa, "Nijar a matsayinta na mamba a Asusun Ba Da Lamuni na IMF, ta nemi wannan taimakon na ƙwararru daga IMF domin inganta da kuma ƙarfafa ayyukan gwamnati."
Ms. HA VU ta bayyana cewa "wannan ziyarar na da zummar taimaka wa hukumomi gano abubuwan da suka fi muhimmanci ga ƙasar."
A watan Yulin shekarar 2024 ne Asusun Ba Da Lamuni na IMF ya amince da bai wa gwamnatin Nijar bashin dala miliyan 71.
Kuma a watan Mayun shekarar 2025 ne wata tawagar IMF ta gana da Firaministan ƙasar game da garambawul kan tattalin arzikin ƙasar.