Mahajjata Musulmi na gudanar da ɗaya daga cikin manyan ibadu na Aikin Hajji wato jifan shaiɗan, inda alhazan suke jifar shaidan da duwatsu a wurare uku da ke wakiltar shaidan a Mina kusa da Makkah, yayin da aka fara shagulgulan Bikin Sallah a faɗin duniya.
Wannan ibada, wadda ake kira 'jifar shaidan', tana tuna yadda Annabi Ibrahim ya ƙi yarda da ƙoƙarin shaidan na hana shi bin umarnin Allah.
Fiye da mahajjata miliyan 1.6 ne ake sa ran za su halarci wurin jifan shaiɗan ɗin a ranar Juma’a, inda kowannensu zai jefi shaiɗan da duwatsu bakwai a kan bango uku na Jamarat da ke Mina.
Hukumar Kididdiga ta Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata 1,673,230 ne suka halarci Aikin Hajjin 2025. Daga cikin wannan adadi, 1,506,576 sun fito daga ƙasashen waje, yayin da 166,654 suka kasance maniyyata cikin gida, ciki har da 'yan ƙasa Saudiyya da mazauna ƙasar.
Jifar shaidan wata alama ce da Musulmi ke nuna kawar da sha’awa da tunanin duniya, tare da tabbatar da imaninsu ga Allah.
Ɓangarorin Jamarat uku, waɗanda maniyyata ke jifa, suna wakiltar shaidan. A nan ne shaiɗan ya yi ƙoƙarin yaudarar Annabi Ibrahim.
An ga jami’an tsaron Saudiyya suna kula da taron mahajjata Musulmi yayin da suka isa Jabal al-Rahmah, wanda aka fi sani da Dutsen Arafat, a lokacin Aikin Hajjin wanda ake gudanarwa a duk shekara.
Mahajjatan sun haɗa sallar Magariba da Isha a lokacin Isha, inda suka kwana a Muzdalifah inda kuma a nan suka tattara duwatsunsu na jifan shaiɗan