Daga Yahya Habil
A watan Satumba na shekarar 2024, Burkina Faso ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tare da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran domin zurfafa hadin kai a fannin bincike da horo kan makamashin nukiliya.
Wannan yarjejeniya ta nuna sabon buri na Burkina Faso a fannin nukiliya, wanda ke zama wani mataki na musamman da ba a taba gani ba a tarihin kasar.
Wannan ita ce kasar da ta fuskanci juyin mulki a shekarar 2022, inda aka kifar da gwamnatin da ke samun goyon bayan Ƙasashen Yamma, wanda daga bisani ya kai ga korar sansanonin sojojin Faransa da ke kasar.
Saboda haka, sabon burin Burkina Faso ba abin mamaki ba ne, domin matsayinta na adawa da mulkin mallaka yana tura ta neman 'yancin siyasa daga tasirin Ƙasashen Yamma.
Burkina Faso ta fahimci cewa daya daga cikin hanyoyin da za ta iya tsayawa tsayin daka ga tasirin Ƙasashen Yamma shi ne ta mallaki karfin soja.
Sai dai, kamar yadda take ganin abin da ya faru da Iran a halin yanzu, Burkina Faso ta san, ko kuma ya kamata ta sani, cewa burin cim ma irin wannan shirin nukiliya ba zai zama mai sauki ba.
A gaskiya, idan akwai wani abu da Burkina Faso da sauran kasashen Afirka za su iya koya daga rikicin da ke tattare da shirin nukiliyar Iran, shi ne cewa Ƙasashen Yamma da abokan hulɗarsu za su yi duk mai yiwuwa don hana wata ƙasa daga cikin ƙasashe matalauta na duniya damar samar da shirin nukiliya.
Shin barazana ce mai tasiri?
Shirin nukiliyar Iran ya kasance babban misali a wannan fanni. Iran ta dage cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne kawai, ba don ƙera makamai ba.
Sai dai Isra’ila, Amurka, da kuma gaba daya Ƙasashen Yamma sun dage kan ganin an kawar da shirin nukiliyar Iran da burinta.
Ba wai saboda ikirarin da suke yi na cewa “Iran ita ce babbar mai daukar nauyin ta’addanci a duniya” ba, amma saboda gaskiyar cewa Iran kasa ce ta Musulunci a Gabas ta Tsakiya, wadda ke da nisan kusan kilomita dubu daya daga Isra’ila.
Barin Iran ta ci gaba da shirin nukiliyarta har ta samar da makamin nukiliya zai zama barazana ga wanzuwar Isra’ila a idanun Ƙasashen Yamma.
Za a iya tambaya, mene ne alaƙar hakan da Burkina Faso da burin nukiliyar Afirka?
Burkina Faso dai ba ta kusa da Isra’ila. Bugu da ƙari, za a iya cewa kusanci da Isra’ila shi ne dalilin da ke hana Iran samun burin nukiliyarta, domin kasancewar Iran kasa ce ta Musulunci ko mai tasowa a duniya ba zai zama dalili ba, tun da Pakistan, wata kasa ta Musulunci kuma cikin ƙasashe masu tasowa, ana tsammanin tana da makaman nukiliya fiye da Isra’ila kanta!
Sai dai, yin amfani da misalin Pakistan a matsayin hujja ba zai yi karfi ba, saboda lamarin Pakistan ya bambanta sosai.
Pakistan ta samu damar mallakar makamin nukiliya ne saboda Indiya ta riga ta samar da nata.
Manufar Ƙasashen Yamma ita ce tabbatar da cewa Pakistan ta kasance mai hana Indiya, wadda ta samu goyon bayan Tarayyar Soviet a lokacin, samun rinjaye.
Amma yanzu da Tarayyar Soviet ta gushe, kuma Indiya ta zama abokiyar Ƙasashen Yamma, ba su ga amfani da karfin nukiliyar Pakistan ba.
Duk da haka, za a iya cewa Afirka ta Kudu ta taba samun damar samar da makamin nukiliya, don haka ba zai zama abu marar yiwuwa ba ga wata kasa ta Afirka ta samu irin wannan damar a yanzu.
Tsohon shirin nukiliyar Afirka ta Kudu
Ko da yake gaskiya ne cewa wannan ba zai yiwu ba, tabbas zai kasance da matukar wahala, kuma don tantance ko wannan gaskiya ne ko a’a, dole ne a tambayi dalilin da ya sa aka rusa shirin nukiliyar Afirka ta Kudu kafin a kawo karshen mulkin wariyar launin fata.
Wannan ya kasance kyakkyawan lissafi daga bangaren Ƙasashen Yamma, domin abin da suka ji tsoro a lokacin ya tabbata.
A yau, gwamnatin Afirka ta Kudu tana daga cikin masu sukar Isra’ila mafi tsauri, kuma ita ce ta kai Isra’ila gaban Kotun Duniya kan zargin Tel Aviv da aikata kisan kare dangi a Gaza.
Abin da za a iya fahimta daga wannan shi ne cewa babu wata kasa ta Afirka da za ta samu sauki idan ta shirya kafa shirin nukiliya. Dole ne ta yi gwagwarmaya sosai.
Daga karshe, babu wata kasa ta Afirka da ke da dukkan abubuwan da ake bukata kamar Koriya ta Arewa, wato kasancewa mai nisa daga Isra’ila, sannan ba ƙasar Musulunci ba, kuma ba daga cikin ƙasashen duniya matalauta ko masu tasowa ba.
Wadannan abubuwa uku, tare da taimakon Tarayyar Soviet, sun bai wa Koriya ta Arewa damar samun makamin nukiliya.
Sai dai, gaskiya mai ɗaci da zaƙi a lokaci guda ita ce cewa kasashen Afirka bai kamata su damu da wannan ba.
Kasashen Afirka, ko Burkina Faso ko wasu, bai kamata su dogara da burin nukiliya ba na tsawon shekaru masu zuwa, amma maimakon haka su mai da hankali kan abin da suke bukata a yanzu - ilimi da ci gaban ɗan’adam.
Game da marubucin: Yahya Habil, dan jarida mai zaman kansa daga Libya wanda ya mayar da hankali kan al’amuran Afirka.
Togaciya: Ra’ayoyin da marubucin ya bayyana ba lallai su kasance suna wakiltar ra’ayoyi, manufofi, ko tsare-tsaren edita na TRT Afrika ba.