GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Isra’ila ta kashe shugaban rundunar juyin juya hali ta Iran
Tuni dai rahotanni suka ce Iran ta tura jirage mara matuƙa zuwa Isra’ila domin mayar da martani.
Isra’ila ta kashe shugaban rundunar juyin juya hali ta Iran
Jagoran addinin ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya mayar da martani game da hare-haren da kakausar murya / AA
13 Yuni 2025

A wasu jerin hare-haren da ta kai Iran, Isra’ila ta kashe shugaban rundunar juyin juya halin Iran, Hossein Salami, tare da wasu manyan jami’an soji masu ilimin kimiyya a Tehran da sauran sassan ƙasar.

A cikin hare-haren da Isra’ila ta kai Iran ta harba makamai 330 sassan ƙasar.

Iran kuwa ta sha alwashin rama hare-haren da Isra’ila ta kai mata.

Tuni dai rahotanni suka ce Iran ta tura jirage mara matuƙa zuwa Isra’ila domin mayar da martani.

Yayin da ƙasar Jordan take gargaɗin ka da a ƙeta hakkin sararin samaniyarta, ƙasar Saudiyya ta yi Allah Wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai kan “yar’uwa [ƙasar] Iran.”

“Masauratar tana bayyana Allah Wadanta da wannan miyagun laifukan jerin hare-haren da kan ‘yar’uwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Iran ta wallafa a shafinta na X.

Ma’aikatar ta harin rashin tausayin Isra’ila kan Iran “ya keta ‘yancin kanta kuma keta dokokin ƙasa da ƙasa.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us