AFIRKA
2 minti karatu
Nijar za ta kashe dala miliyan biyu don sayo na'urori tare da gina sashen gwajin cutar kansa
Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa Shugaban Ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ne ya ƙaddamar da bikin aza tubalin ginin sashen gwajin ciwon dajin a asibitin ƙwararru na Yamai a ranar Litinin.
Nijar za ta kashe dala miliyan biyu don sayo na'urori tare da gina sashen gwajin cutar kansa
Shugaban Nijar ya ce nan ba da jimawa ba ne za a kammala aikin domin 'yan Nijar su amfana da shi / Nigeria Presidency
5 Agusta 2025

Gwamnatin ƙasar Nijar za ta gina ɓangaren gwajin cutar kansa tare da sayen na’urorin gwajin ciwon daji kan dala miliyan 2,300,000 wato fiye da sefa biliyan 13.

Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa Shugaban Ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ne ya ƙaddamar da bikin aza tubalin ginin sashen gwajin ciwon dajin a asibitin ƙwararru na Yamai a ranar Litinin.

Bayan ya gama aza tubalin, Shugaba Tiani ya ce ɓangaren zai ba da damar gano ciwon daji da wuri da kuma ɗaukar mataki a kansa.

Shugaban ya kuma gode wa ma’aikatan jinyar ƙasar da ma ‘yan ƙasar baki ɗaya game haɗin kansu.

A nasa jawabin, Ministan Ma’aikatar Lafiya ta ƙasar, Kanal-Manjo Garba Hakimi ya bayyana cewa "Nijar, wajen aiwatar da tsarin yaƙar cututtuka mara yaɗuwa ciki har da ciwon daji, tana nuna jajircewarta wajen rage tasirinsu da inganta rayuwar mutane."

Ministan ya ce na’urar wadda ita ce ta farko a yankin za ta taimaka wajen gudanar da ingantaccen gwajin ciwon daji.

Da yake magana game da yadda za a samar da kuɗin aikin, Garba Hakimi ya ce ƙasar za ta samu kuɗin ginin da na’urar (dala miliyan 2,3000,000) ta hanyar yarjejeniya da hukumar makamashin nukiliya ta duniya (IAEA).

Da zarar an kammala aikin, na’urar za ta taimaka wajen iya gano ciwon daji a asibitin ƙwararru na Yamai ta hanya mafi ingancin da za ta ba da damar iya yi wa mara lafiya maganin da ya dace, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us