Kalmar da ta fi kowacce juyawa a harshen Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ita ce - “tariff” (haraji) - kuma na da tushe da ya haura katangar Fadar White House.
Tarihin kalmar da Trump ke amfani da ita wajen nuna kishin tattalin arzikin kasarsa ya samo asali ne daga Daular Usmaniyya, nazarin harshen Larabci, da karni da dama na kasuwanci tsakanin al’ummu.
A lokacin da Trump ya tsaya a gaban Fadar White House ya bayyana kalmar “tariff” a matsayin ‘kalmar da ya fi kauna’ kuma ma “wadda ta fi so kyau”, ‘yan tsiraru ne suka san irin gwagwarmayar da kalmar ta sha da ma daga ina ta fito.
Ta yi balaguro cikin dauloli, yaruka, da kasuwanci - inda a karshe ta sadar da Washington ta yau da tsarin kasuwanci na Istanbul na zamanin baya.
“Amfani da kalmar “tariff” da Trump ke yi na iya zama kamar kalmar Amurka ce ta musamman,” in ji Dr Canan Torlak, wata mai binciken tarihin tattalin arziki da ke Istanbul, “amma asalin tarihinta na koma wa ga falsafar tattalin arzikin zamanin Daular Usmaniyya.”
A yau, “tariff” na nufin harajin da ake saka wa kan kayan da ake shiga da su wata kasa ko fitar da su daga wata kasa.
Amma asalin kalmar na bayar da labarai babba. Malamai na bayyana asalin kalmar daga Larabci ta ke wato ta’arif (تعريف) ma’ana “bayar da ma’ana” ko “a sanar.”
Daga Larabci ta gangara zuwa yaren fasha, sannan zuwa Turkancin zamanin Daular Usmaniyya, kafin daga bisani ta shiga yarukan kudancin Turai - Italiya na kiran ta (tariffa). Turancin Faransa kuma (tarif), sannan sai Turancin Ingilishi.
“A yayin da kasuwanci ke tashi daga Asiya tahanyar amfani da tashohin jiragen ruwan Daular Usmaniyya zuwa Turai, haka ma yare,” in ji Torlak. “Kalmar ta’arif - da ke nugin jerin wasu kudade da za a biya na fito - an dinga amfani da ita daga Istanbul zuwa Iskandariyya. ‘Yan kasuwar Turai sun dinga hadu wa da wadannan takardu.”
Wasu kwararru da masana tarihi sun kawo wani kauli na daban game da kalmar inda suke alakantata da Tasha Jiragen Ruwa ta Spaniya mai suna Tarifa, wadda aka baiwa sunan kwamanda Tarif bin Malik.
Wannan tasha ta taka rawa sosai wajen karfar haraji daga jiragen ruwan da ke shiga Spaniya ta Musulmai; akwai yiwuwar hakan ya tasiri kan samuwar kalmar.
Har ila yau, masana harshe na ta tantama. Ra’ayin da ya fi rinjaya shi ne na Larabci-Daular Usmaniyya, wanda ke jinginuwa sosai ga tasirin habakar salon kasuwanci da harshe.
Tsarin Daular Usmaniyya na kare kasuwancin cikin gida a aikace
Torlak na da ra’ayin cewa tsarin yau na kare kasuwancin cikin gida da kasashe ke amfani da shi ta hanyar lafta haraji, ya samo asali ne daga tsarin cigaban tattalin arziki na Daular Usmaniyya.
“Bayan an ci Constantinople (Istanbul) da yaki a 1453, Usmaniyawa sun rufe tekun Bahar Maliya ga manyan kasasen duniya,” ta fada wa TRT World. “Wannan ya yi tasiri da mayar da wajen kasuwar usmaniyya.”
Daular ta kuma soke alfarma dadaddiya da aka baiwa garuruwan Itliy irin su Genoa da Venice. Ya zuwa karni n 16, an daidaita haraji: ana karbar harajin kashi 5 zuwa 6 daga ‘yan kasashen waje, mazauna yankin da ba Musulmai ba kashi 3 zuwa 4, Musulmai ‘yan asalin yankin kuma kashi 2 zuwa 3, in ji Dr Torlak.
“Sun saka haraji da yawa kan ‘yan kasuwar kasashen waje inda suka fifita kasuwancin cikin gida. Tsari ne da aka kawo shi da gangan,” in ji Torlak. “Wanda ya fito da fifikon siyasa da karfin iko da mulki.”
Ta kara da cewa: “Usmaniyawa sun kasance manya a kan gaba a kasuwancin kasa, duk da ba su da babban kasuwancin teku, amma sun yi nasara, sau da yawa ta hanyar dogaro kan abkan mu’amalar su da ba Musulmai ba.”
Asali dai, daular ta yi amfani da yawaitar jama’arta inda ta yi amfani da anufofin tattalin arziki wajen rike iko da kasuwanci kan nahiyoyi uku.
Tsarin sanya haraji na yau
Zai zama kamar azanci a ce kalmar da shugaban kasar Amurka ke amfani da ita a karni na 21 don warewa da habaka tattalin arziki ta samo asali ne daga alakar kasuwanci da wata duniyar ta daban.
“A dukkan lamarin biyu - Usmaniyya da na Amurka - amfani da haraji ba don tattalin arziki ba ne kawai. Na da manufar cim ma bukatar siyasa,” in ji Torlak.
“Kuma idan kalubale suka taso, dukkan suna waiwaye zuwa baya. Daular Usmaniyya sun kaddamar da sauye-sauye a karni na 18 don dawo da martabarsu ta baya.
A yau muna jin kalamai irin su ‘Dawo da Karfin Amurka.’ Ra’ayin a bayyane yake karara kuma na da kama da juna.”
A yayinda duniya ke ci gaba da muhawara kan dunkulewar duniya waje guda da yadda tsarin ba ya yi wasu dadi, kalmar “tariff” (haraji) na tunatar da cewa tarihi ba ya bacewa - yana habaka, sauya fasali, da maimaita kansa.
“Tarihi na da ban ta’ajibi,” Torlak ta kara fada. “Kalmar da ake amfani da ita a yanzu don rufe iyakoki, ta taba bayyana a wata duniyar da babu su.”