Kowace safiya, Zeina Awad mai shekaru 45, tana baje gurasar da ake kira kisra, gurasar dawa da take gasawa da hannu, a kan wata tabarmar roba a kasuwar Hay al-Nazir da ke unguwar el-Obeyd a yankin Kordofan na Sudan.
Mahaifiyar yara hudu da ta gudu daga garin Ghubeish saboda rikicin da ake ci gaba da yi, Awad na samun fan 5,000 zuwa 6,000 ne kacal na Sudan a rana, kwatankwacin dalar Amurka 8.30 zuwa dala 10, kuɗin da da ƙyar ke iya sayen kilo guda na garin fulawa.
Don samun abin biyan bukata, tana ƙara kuɗin shiga ta hanyar sayar da dawa da kayan lambu da take nomawa a bayan gidanta don biyan wasu buƙatun iyalinta.
"Babu kudi, babu gari, kuma babu taimako," ta shaida wa TRT World. "Mu kadai ne kawai."
A yayin da Sudan ta shiga shekara ta uku a rikicin da ake yi, samarwa da rarraba kayayyaki sun durkushe, farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi, ga karyewar darajar kudi ta mayar da kokarin samar da abin kai wa bakin salati a kowace rana zama wata babbar gwagwarmaya.
Sudan ta sha fama da rikici karfin iko tsakanin sojojin kasar da dakarun sa kai da ake kira RSF.
Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye 150,000, tare da raba fiye da miliyan 10 da matsugunansu. Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ta bayyana lamarin a matsayin "mafi girman rikicin jinƙai a duniya".
Shirin Bai Daya na Nazari Kan Kashe-Kashen Abinci (IPC), wani shiri na duniya wanda ke yin nazari kan amincin abinci da abinci mai gina jiki don sanar da yanke shawarwari, ya bayar da rahoton cewa sama da rabin al'ummar Sudan na fuskantar matsalar abinci.
A Kudu da Arewacin Kordofan kaɗai, mutum kusan 755,000 ne ke fama da matsananciyar yunwa, mafi muni da aka gani a baya bayan nan.
Lamarin dai ya yi muni musamman ga mutanen da suka rasa matsugunansu da mazauna yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula, yankunan da aka takaita samun agajin gaggawa da tallafi.
Yankin Kordofan na daya daga cikin yankuna 14 da za su fi fuskantar barazanar yunwa, matukar dai tashin hankalin ya kara tabarbarewa ko kuma kai taimakon jinƙai ya ci gaba da fuskantar cikas.
Bankin Raya Kasashen Afirka ya kiyasta cewa tattalin arzikin Sudan ya durkushe da kashi 37.5 cikin 100 a shekarar 2023.
Rahotanni na cikin gida na cike da labarai na hauhawar farashin kayayyaki. Buhun dawa mai nauyin kilo 100 a yanzu ya kai fan 240,000 na Sudan (kimanin dalar Amurka 400), an samu karin kashi 73 cikin 100 tun daga shekarar 2022.
Ana sayar da man girki akan fan 16,000 na Sudan ($26.65), garin fulawa kan fan 7,000 ($11.66) kowane kilogiram, sabulu na yau da kullun ya kai fan 5,000 ($8.33) kowace lita.
Kasa kaya a gefen hanya ne zabin da ya rage
Awad na daya daga cikin dubban 'yan Sudan da aka bar su ba tare da wata hanyar rayuwa ba, kuma yanzu saye da sayarwa a unguwanni ne kawai ke tsakanin su da yunwa.
A fadin yankin Kordofan, a birane kamar Kadugli, El-Obeid, da Al-Mujlad, kasuwannin sayar da kayayyaki na mako-mako sun bayyana, inda mutane 700 zuwa 3,000 ke halartar kowace.
A kasuwannin, ana kasuwancin kayan masarufi irin su kuɓewa, wake, dawa, gurasar kisra, da sabulu ba tare da kuɗi ba.
Waɗannan kasuwanni na yau da kullun, inda ake shimfida haja a kan tabarmin da aka shimfida a kan kwalta, sun bayyana a wajen birane. Yanayin na da wahala, kuma tsaro ya yi wuya.
Yawaitar zuwa ko dawo wa daga wadannan kasuwanni na karewa da cin amana sakamakon fadan da ake yi tsakanin dakarun RSF, da sojojin Sudan, da kuma matsanancin karancin man fetur da kuma rufe tituna.
A unguwar Hajr al-Nar da ke Kadugli, Mohamed Ibrahim dan shekara 30 ne ke shirya cin Kasuwar Sitr a duk ranar Juma’a, wanda ke taimaka wa mutane kusan 1,500 kayan bukatar yau da kullum.
"Na gudu daga Dalang bayan an sace motata a shekarar 2023. Na rasa aikina a matsayin direba, amma na ji ina da alhakin na taimaka," Ibrahim ya shaida wa TRT World. "Mun fara wannan kasuwa ne don tsira daga kawanya da yunwa."
Karancin mai ya sa kusan ba zai yiwu a iya jigilar kayayyaki ba, kuma ana iya samun barkewar rikici ba tare da wani gargadi ba, in ji Ibrahim.
Ba tare da wani tallafi daga kungiyoyin jin kai ba ko gwamnati, rike kasuwar da kasancewar ra tana aiki koyushe ya zama abu mai wahala.
Masu talla, mafi yawan su mata, za a ga suna kasa kubewa da wake, da man girki da sabulu a kan titi. Amma duk da haka kasuwar na fuskantar barazana a koyaushe, barazanar rikici da rashin kula.
A cewar Hukumar Kula da Mata ta Majalisar Dinkin Duniya, kashi 53 cikin 100 na mutanen Sudan miliyan 12 da yakin basasa ya raba da muhallansu mata ne manya da kanana.
Hukumar ta bayar da rahoton cewa, fiye da kashi biyu bisa uku na gidaje da mata ke jagoranta na fuskantar karancin abinci.
Ibrahim ta ce matan da mazansu suka mutu da kuma iyaye mata da suka rasa matsugunnansu ne mafi yawan masu sayar da kayayyaki a kasuwar.
Wadannan mata su ne kashin bayan sabbin matakan dogaro da kai d aake samarwa, duk da cewar suna jure tsangwama, ƙyama, da tashin hankali ba tare da wata kariya ta doka ko ta zahiri ba.
Irin wannan labari ya faru a Kasuwar Tiba da ke kusa da su, inda Nidal Koko, ‘yar shekara 25, tsohuwar daliba a Jami’ar Kordofan, ta ke sayar da burodi a wani gidan burodi da ke yankin don tallafa wa iyalinta mai mutane shida. Ta bar makaranta bayan yakin da ya barke a shekarar 2023.
"Ina samun kusan fan 7,500 a rana ($ 12.49), amma farashin fulawa da rashin dahir din samun kayan ba su da tabbas," in ji ta a yayin tattauna wa da TRT World.
"Dole ne in yi kasuwanci na efen hanya don in ciyar da iyalina. Yin aiki tare da maza, musamman gadin gurasar da safe, na kawo damuwa."
Duk da kalubalen, ta kasnace mai samun karfin gwiwa da azama.
"Yawancin mu a nan mata ne. Mun gaji. Burina shi ne in sake yin karatu, amma a yanzu kubuta da rai shi ne abind muka ba wa fifiko," in ji ta.
A yankin Al-Mujlad, Mona Musa, ‘yar shekara 33, na yin wani abu saboda wahalar da ta fada ciki. Ta kammala karatunta a Jami’ar Dalanj, inda ta gudu daga kauyensu a shekarar 2023, kuma a yanzu haka tana karanar sana’ar yin sabulu na ruwa, wanda take sayar da duk lita daya kan kudi fan 5,000 a kasuwar Ajib.
"Ina samun tsakanin fan 10,000 zuwa 20,000 a kullum ($ 16-33), amma farashin mai, fan 16,000 ($26.65) kowace lita, na tilasta min cinikin kayayyaki don samun sayen kayan hada sabulun," ta fada wa TRT World.
"Ina fuskantar karancin abinci, kuma tafiye-tafiye na da hatsari saboda rikicin. Rabin masu sayar da kayayyaki a nan duk ‘yan gudun hijira ne kamar ni da aka raba da matsugunansu. Babu taimako daga gwamnati ko ko wasu kungiyoyi masu zaman kansu."
Duk da haka, ta jajirce. “Yaƙin ya lalata burina na neman ilimi mai zurfi, amma ina gwagwarmaya ne don in tallafa wa kaina da kuma bunƙasa kasuwancina,” in ji ta.
A kurkusa da wadannan matan akwai Hajj Adam mai shekaru 56, wanda ya shahara da saye da sayarwa a kasuwar mako-mako ta Um Duror.
Ya kwashe shekaru yana kawo garin fulawa da sikari a fadin yankin, har zuwa lokacin da aka daka wawa kan kayansa a shekarar 2023.
"Na yi ƙoƙarin kawo kayayyaki daga Jihar White Nile ta bayan fage," kamar yadda ya shaida wa TRT World. "Duk da biyan haraji, amma mayakan RSF na hana mu wuce wa."
A yanzu, yana taimakawa wajen shirya wurin sayar da kayayyaki na wucin gadi da ake kira Souq al-Shams, ko Kasuwar Rana, kasuwar da ke ci na ‘yan awanni a kowace rana.
"Da wahala muke samun kayayyaki. Kilo daya na garin fulawa ya kai fan 7,000 ($ 11.66), sukari kuma ya kai fan 10,000 ($16).
Irin wannan kasuwa ta baje haja a gefan hanya ce kawai mafita. Amma babu tsaro, kuma rikici na iya lalata komai a kowane lokaci ba tare da tsammani ba. Har yanzu ina mafarkin sake fara kasuwanci, bayan an samu zaman lafiya," in ji shi.
Yunkurin magance durkusher da aka tsara
Masanin tattalin arziki Haitham Fathi da ke birnin khartoum na da ra’ayin cewa wadannan kasuwannin na wucin gadi, ko abin da ya kira “kasuwannin ban gishiri in ba ka manda na kauyuka”, sun zama mafita daga rugujewar da ake fuskanta a hankali.
"Lokacin da buhun dawa yake fan 240,000, kuma man girki ya yake kan 16,000 a kowane fan ($26.65), kasuwancin gefen hanya ya zama dole, ba wai zabi ba," ya shaida wa TRT World. "Amma idan ba tare da samun daidaiton siyasa da tsaro ba, halin da ake ciki ba zai dore ba."
Fathi na bayar da shawarwari ga shirye-shiryen kananan kasuwanci da ke da manufar tallafa wa mata da kafa tsarin taimakon kai da kai, musamman a yankunan karkara, don saukaka matsin tattalin arziki.
Amma kuma ya yi gargadin cewa babu yiwuwar farfadowa a nan kusa.
Mafi yawan matan da ke cinikayya a irin wadannan kasuwanni na rayuwa a gidaje masu hatsari, wadanda ka iya fuskantar sata, fyade da cin zarafi, inda ba su da hanyoyin samun kariya ko tallafin kudade.
Yawancin matan da ke aiki a kasuwannin sayar da kayayyaki suna zama a cikin gidaje masu wahala, suna fuskantar sata, cin zarafi, da cin zarafi, ba tare da samun damar samun sabis na kariya ko tallafin kuɗi ba.
A yayin da babu sanya idanu daga bangaren gwamnati, wadannan kasuwanni za su ci gaba da kasancewa masu rauni ta fuskar tattalin arziki da cin zarafi a zahiri.
“Sai dai kuma a yanzu, kasuwannin sun zama shaidar nuna tirjiyar jama’a,” in ji shi.
Amma a wajen mata irin su Awad, nauyin na a matukar wahalar dauka. Rayuwa a cikin wadannan yanayi, ta zama kamar mutum ya ji “yana rayuwa ne a cikin wani kulli”.
Da wahala kudaden da ake samu su biya bukatun yau da kullum, kuma a yayin da rashin tsaro ke kara girmama, fatan da jama’a ke da shi na kara gushewa,” ta fada.
An wallafa wannan makalar da hadin gwiwar Egab.