Fafaroma Francis, sanannen mai kare muradun Falasdinawa
DUNIYA
6 minti karatu
Fafaroma Francis, sanannen mai kare muradun FalasdinawaMarigayin babban malamin Kiristocin ya fita daban wajen kare muradun Falasdinawa saboda ya rayu da shaida yakin Isra’ila da ya janyo mummunan yanayi a Gaza.
Fafaroma ya tsaya sosai wajen kare muradun Falasdinawa. / Photo: AP
21 Afrilu 2025

Fafaroma Francis, shugaban darikar Roman Katolika ta mabiya Addinin Kirista da yake shugabanta tun 2013, wanda aka sani da kare manufofin Falasdinawa, ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 88, in ji Kevin Ferrell, Sakataren Harkokin Kudi na Fadar Vatican.

A safiyar yau, Shugaban Kiristoci a Roma, Francis, ya koma ga mahaliccinsa. Ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimta wa Ubangijinsa da Cocinsa,” in ji Farrell a sanarwar.

A matsayin shugaban addini ga mutane kusan biliyan 1.4 ‘yan Roman Katolika, wadanda ke daya daga manyan darikun Kiristanci uku, Francis ya sanya kaunarsa a zukatan Musulmai a duniya saboda kiran da ya dinga yi na a tsagaita wuta a a kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda ya kashe sama da mutane 51,200, mafi yawan su mata da yara kanana a tsakanin Oktoban 2023 da Afrilun 2025.

“An san shi da nacewa sosai wajen mai maita wannan kira na a tsagaita wuta, saboda kawo karshn rikicin, don bayar da dama a kai kayan gajin jinkai Gaza.

Ya ci gaba da riƙe matsayin cewa Falasdinawa na da ‘yancin samun adalci da amincewa da kokarin kai,” in ji Dr Jordan Denari Duffner, wata kwararriya kan addinai da ke Amurka da ta rubuta litattafai kan tattaunawa tsakanin Musulmai da Kiristoci, Kyamar Musulunci da nuna wa Musulmai wariya.

“Fafaroma na da muhimmanci da murya mai kiran a yi gyara, yana mai tunawa mabiya Katolika abinda addininmu ya fada game da neman a yi adalci a zauna lafiya,” ta fada wa TRT Worls.

Tun bayan da Fafaroma Freanis ya zama shugaba a Vatican, ya sha neman a warware rikicin ta hanyar samar da kasashe biyu. Misali, Fafaroma St, John Paul, d ya jogaranci Vatican daga 1978 zuwa 2005, ya yi tsit game da nuna tausayi ga Falasdinawa.

Cocin Roman Katolika ta amince da Kasar Falasdin duba ga iyakokinta na 1967, matakiin da ya bakantawa ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila.

Duffner da a yanzu haka take rubuta littafi kan Fafaroma Francis da Musulunci, ta ce marigayi malamin na addinin Kirista na aiki da abinda ya yi imani da shi inda ya ce Falasdinawa a shan wahaka kuma suna bukatar daidaito kamar makotansu Isra’ila.

Yawanci Fafaroma na yin taka tsan-tsan game da yin magana kan rikicin duniya, amma Francis bai taba saurara wa ba idan aka zo maganar bayyana ra’ayi kan hare-haren bam kan mai uwa da wabi a Gaza tsawon watanni 16.

Yana yawan bayyana bacin ransa game da Gaza “na irin zalunci, zuwa ga kashe yara kanana da manyan bindigu, zuwa ga jefa bam kan yara kana, bam a kan makarntud d asibitoci - \Wanne danyen aiki ne haka!”

A farkon fara kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Gaza, Francis ya yi kira ga tsagaita wuta nan da nan. “Ku dakata da kai hare-hare da mayar da makamai,” in ji shi, yana mai kara wa da cewa “Yakin na janyo shan wahala da mutuwar wadanda ba su ji ba ba su gani ba.”

“Yaki a koyaushe asara ne! Kowanne yaki rashin nasara ne!”

A lokacin da hare-hare ta sama na Isra’ila suka fada kan Cocin Orthodox a Gaza a ranar 19 ga Oktoban 2023, tare da kashe Falasdinawa 18 da suka fake a wajen, Francis ya bukaci Isra’ila da ta kawo karshen yakin nan da nan.

“Ina tunanin mummunan yanayin dan adam da aka shiga a Gaza… Ina sake maimaita rokona na bude hanyoyi, don a samu damar kai kayan agajin jin kai…”

A yayin da Isra;’ila ke yin ruwan bama-bamai a Gaza, Fafaroma Francis ya dauki matakin kulla sadarwa ta kai tsaye da Kiristocin Gaza da aka yi wa kawanya. Ya kan kira Babbar Cocin Gaza duk dare don yin addu’a da kalaman kwarfin gwiwa ga Kiristoci da Musulmai da ke fake wa a Cocin.

Gabriel Romanelli, babban malamin coci a Gaza, ya ce mutanen da aka yi wa kawanyar na samun karfin gwiwa daga Fafaroma da goyon bayan da yake bayarwa a lokacin d aake fama da karancin ruwa, abinci da magunguna.

Kimanin mutane 500 ke neman mafaka a Cocin ciki har da manyan malamai uku, iyaye mata biyar da masu nakasa su 58. Mafi yawan mutanen da suka zauna a wajen Musulmi ne da kananan yara da ke neman taimako na musamman.

Duffner ta kara da cewa Francis a kowacce rana Fafaroma na kiran wayar babban malain cocin gaza “har ma a lokacin da yake gadon asibiti”.

"Koyarwar Katolika ta bayyana karara cewa a duk lokacinda ake harar ‘yan ba ruwana, a lokacin da aka rike abinci, babu isasshen wajen zama, a looacin da ake rusa kayan kula da lafiya, to akwai alhakin mu fito mu yi magana don kare wadanda suke shan wahala,” in ji ta.

“Ina tunanin Fafaroma Francis ya nuna hakan ta hanyar mayar da martani ga halin da ake ciki a Gaza, sannan da ma rashin adalcin da muke gani karara a Gaza da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa,” in ji ta.

Ko Francis ya ba da mamki saboda goyon bayan Falasdin

Fafaroman ya kuma hadu da makusantan Falasdinawa da aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza. “Wannan ba yaki ba ne, wannan ta’addanci ne,” in ji Fafaroma a wani taro da aka gudanar.

Shireen Halil, Bafalasdinawa kuma Kirista daga Bethlehem wadda na daga wadanda suka kira malamin, ta fada wa ‘yan jaridu cewa ita da wasu sun “yi mamaki” da irin bayanan da Fafaroma ke da shi kan rikicin Gaza.

Duffner ta ce akwai “cigaba da yawa” ta hanyar Francis daga 2013 zuwa 2025 da ma a lokacin wanda ya gada Fafaroma Benedict na XVI da ya yi jagoranci daga 2005 zuwa 2013, Fafaroma John Paul II da ya yi jagoranci daga 1978 zuwa 2005 da Fafaroma Paul VI da ya yi shugabanci daga 1963 zuwa 1978 - kan batun Falasdin.

“Tun 1940, Vatican na da ra’ayin Falasdinawa sun cancanci samun kasaru ta kansu. Ina tunanin wannan wani abu ne da ake gudanarwa ba wai a lokacin Francis kawai ba, har ma a zamanin wadanda suka gabace shi,” in ji ta.

Sai dai kuma, marigayin babban malamin Kiristocin ya fita daban wajen kare muradun Falasdinawa saboda ya rayu da shaida yakin Isra’ila da ya janyo mummunan yanayi a Gaza.

“A wasu hanyoyin, matakan Francis sun zama mafiya karfi a amo sama da wadanda suka gabace shi, saboda yanayin da muke ciki.”

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us