Abin da ya sa farashin kayan abinci ke sauka a Nijeriya
NIJERIYA
5 minti karatu
Abin da ya sa farashin kayan abinci ke sauka a NijeriyaFarashin abinci na sauka a Nijeriya bayan matsalar tsadar kayan masarufi da ta dauki lokaci ta janyo tasiri sosai a kasuwar hatsi, inda 'yan kasuwa ba sa samun masu saye duk da saukar kayayyakin.
Kayan abinci na sakko wa a Nijeriya / Getty Images
11 Maris 2025

Daga Abdulwasiu Hassan

Abubakar Ibrahim ya kasance yana kasuwanci a kasuwar hatsi mafi girma a Nijeriya a iya tunaninsa.

Duk da haka, a yanzu idan ya fita aiki a kowacce ranar kasuwa, babu abin da yake taraddadi illa rashin tabbas din da ke tattare da kasuwancin.

A zahiri, saukar farashin abinci na kwanan nan a kasar ta Afirka ta Yamma ya kamata ya zama sauki bayan rikicin tsadar abinci da rayuwa ta lokaci mai tsayi. Ibrahim ya kira hakan da “Agaji daga Allah”.

Rumfarsa da ke kasuwar hatsi ta kasa da ke Dawanau a Kano ta zama wani wajen kasuwanci da a yanzu babu mutane sosai.

A tsaye yake a tsakanin tarin buhunhunan masara da wake, Ibrahim na raba daya biyu kan dambarwar saukar farashin ba ta janyo bukatar hatsin ba, inda kudi da ma masu saye na kasa da kasa du suka yi ƙaranci.

A kasar da hauhawar kayan masarufi da kashi 40 ya kassara kasafin kudaden gidaje a shekarar da ta gabata, wannan raguwa da aka samu ta zama sauki da rashin tabbas, inda masu ruwa da tsaki ke tunanin me ya janyo hakan - lamarin da ya fara faruwa tun daga tsoma hannun gwamnati zuwa karyewar darajar kudi - ne suka janyo sauyin.

“Buhun masara kilo 100 da ake sayarwa sama da Naira 70,000 a shekarar da ta gabata, a yanzu ya dawo kimanin Naira 50,000 ko ma kasa da haka,” Ibrahim ya fada wa TRT Afrika. “Saukar farashin ya kuma shafi irin su wake, shinkafa da waken suya.”

Dalilan da ake ganin sun janyo hakan

Dr Usman Bello, da ke koyarwa a sashen tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, ya bayyana cewa karuwar darajar Naira kan dalar Amurka na daya daga dalilan da suka janyo karyewar farashin kayan abinci,

Dalar da ake sauyawa kusan naira 1,500, a baya bayan nan ana sauya ta a kan 1,700.

“Gwamnati na shigo da hatsi tana raba wa bashi ga masu saya da yawa. Wannan ya hada da masu samar da abincin kaji, wadanda ke cinye wani bangare da yawa na hatsin,” Dr Bello ya fada wa TRT Afrika.

“Da zarar sun samu ribar da suke so, sai wadannan masu saya su mayarwa da gwamnati bashin da suka karba. Tsarin na ba su dama sosai sama da su je kasuwa su saya.”

Ministan ayyukan noma na Nijeriya, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa saukar farashin kayan abincin sakamakon kokarin da gwamnati ke yi ne wajen kawo kaya kasuwanni ta hanyar noma a cikin gida maimakon shigo da su daga kasashen waje.

“A baya mun fuskanci karancin bukata da kawo hatsi kasuwanni. A 2024. mun samu girbi mai gwabi, wanda ya kawo samun abinci da yawa a kasuwanni sama da yadda aka samu a shekarun baya,” in shi.

“Mataki ne da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na rage hauhawar kayan abinci, kuma muna ci gaba da wannan kokarin.”

Samar da abinci a cikin gida

Kyari ya bayyana nasarar gwamnati ga noman rani tare da bayar da tallafi kafin noman damina.

“Wasu mutanen na cewa mun sayo kayan abinci daga kasashen waje, ba mu yi haka ba. Muna da kofar yin hakan, amma ba a yi amfani da ita ba ma.” in ji shi.

A yayin da gwamnati ta ke da fata nagari game da dabarunta, wasu masu nazari sun yi gargadi da cewa cigaba d akaryewar farashin hatsi na iya karya gwiwar manoma su daina zuba jari, matukar ribar da ake samu ba ta da yawa.

“Gwiwar manoma za ta yi sanyi idan har takin zamani bai sakko ba daga farashinsa na shekarar da ta gabata wanda ya yi tsada sosai,” Dr Bello ya yi gargadi.

Ministan na ayyukan noma na bukatar da a yi watsi da da wannan mummunar fahimta, yana mai tabbatarwa da masu ruwa da tsaki cewa ayyukan tallafi na gwamnati za su mayar da hankali ga bunkasa noma a cikin gida.

“Muna son daidaita farashi. Muna tsara yadda za mu rage farashi nan da makonni biyu masu zuwa ba tare da karya gwiwar manoman cikin gida ba,” in ji shi.

Manoman da ransu ya baci

Dillalan hatsi da suka saya suka ajje tun lokacin kakar shekarar da ta gabata ba sa jin dadin abinda ke faruwa a kasuwanni.

Ibrahim, ya kasa fahimtar me ya sa ba a bukatar hatsin duk da sakkowar farashinsa.

Ministan Ayyukan Noma Kyari ya lura da cewa wasu “masu boye abinci” sun fara bude rumbunansu saboda saukar farashin da ake samu, wanda ya kai ga samun abinci a kasuwanni sosai.

Masu nazari na cewa akwai bukatar gwamnati ta kawo gyara. “Shigo a abinci sosai a wannan lokaci ba abu ne mai dorewa ba, musamman idan farashin suka tashi da damina,” Dr Bello ya shaidawa TRT Afrika.

“Ci gaba da samun wannan ya ta’allaka ne ga tanadin da aka yi a kasafin kudi na 2025, wanda Shugaban Kasa ya sanya hannu a kai a baya bayan nan.”

Akidun kasuwanci mai ‘yanci ga kowa

Sashen samar da abinci na Nijeriya ya sha samun kariya na tsawon lokaci, inda aka haramta shigo da muhimman abinci irin su shinkafa don a kare samar da su a cikin gida.

Sai dai kuma, wannan tsari bai rage farashin zuwa yadda ‘yan Nijeriya za su dinga saya yadda ya dace ba.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ‘yan Nijeriya na kashe kashi 65 na kudaden da suke samu a kan abinci.

A yayin da dillalan hatsi ke jiran kayan abinci su tashi, gwamnati ta ci gaba da taimaka wa wajen samar da karin abinci a kasuwanni.

Su ma masu saye a gefe guda, na fatan samun kasuwa mai saukin kayayyaki. Tare da shekaru takwas na bayar da kariya amma kuma ba a samu saukar farashi ba, wasu na mamakin idan budaddiyar kasuwa mai ‘yanci ga kowa za ta kawo tsari mai kyau.

MAJIYA:Getty Images
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us