Ali Bukar Dalori: Ƙalubale biyar da ke gaban sabon shugaban APC na riƙo
NIJERIYA
4 minti karatu
Ali Bukar Dalori: Ƙalubale biyar da ke gaban sabon shugaban APC na riƙoBayan saukar Ganduje daga shugabancin jam'iyya, hankalin magoya bayan APC da sauran 'yan Nijeriya ya koma kan magajinsa Ali Bukar Dalori domin ganin irin rawar da zai taka da kuma irin jerin ƙalubalen da ke a gaban shi.
Dalori zai ci gaba da jagorancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron jam’iyyar domin zaɓar mata sabon shugaba. / Others
28 Yuni 2025

A wani al’amari da ya girgiza fagen siyasar Nijeriya, Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya Dakta Abdullahi Ganduje, ya ajiye mukaminsa a ranar Juma’a, wanda hakan ya kawo ƙarshen jagorancinsa na jam’iyyar mai cike da ce-ce-ku-ce.

Yanzu hankalin 'yan jam’iyya da 'yan Nijeriya ya koma kan wanda ya gaje shi a matsayin sabon shugaba na riƙo wato Ali Bukar Dalori domin ganin rawar da zai taka bayan kaucewar Ganduje.

Dalori zai ci gaba da jagorancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron jam’iyyar domin zaɓar mata sabon shugaba.

A halin yanzu dai jam’iyyar APC mai mulki tana fama da ƙalubale iri daban-daban tun daga kan rikice-rikicen cikin gida, matsin lamba daga jam’iyyun adawa, da kuma ƙaruwar bukatun jama’a na kyakkyawan shugabanci.

Waɗannan sun sa abubuwan da ke kan wannan sabon shugaban jam’iyyar suka zama masu nauyi matuƙa.

Bari mu yi nazari kan wasu abubuwa biyar da ya kamata sabon shugaban ya mayar da hankali a kansu.

Sulhu da haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya

Jam’iyyar APC ta jima tana fama da rikice-rikice na cikin gida daga matakin jihohi har zuwa na tarayya.

Yadda ake samun rarrabuwar kai tsakanin jiga-jigan jam’iyya da kuma masu yi musu biyayya na ƙara kawo koma baya ga jam’iyyar.

A halin yanzu ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne sulhu tsakanin ‘yan jam’iyya.

Idan ba a samu sulhu da fahimtar juna tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ba, APC ɗin za ta yi ta fuskantar ƙalubale iri daban-daban ta kuma zama abin dariya ga masu adawa da ita.

Haka kuma wannan shi ne tsayayyen lokacin da ya kamata ta ɗauki wannan matakin ganin cewa zaɓe na ƙaratowa.

Saita alƙiblar jam’iyyar

Jam’iyyar APC a ‘yan kwanakin nan na yawan shan suka a cikin gida da waje kan zargin kura-kuran da ake yawan tafkawa wanda ake ganin sun samo asali ne sakamakon rashin alƙibla a jam’iyyar.

Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar a kwanakin baya sun koka kan yadda aka rinƙa jan ƙafa kafin aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda aka gudanar a Fabrairun 2025, watanni 18 kenan bayan zaman Ganduje shugaban jam’iyya.

A halin yanzu, sabon shugaban APC na da nauyin ɗora jam’iyyar kan miƙaƙƙiyar hanya da za ta bambanta jam’iyyar da sauran, ba wai kawai a baki ba, har da aiki da manufofi.

Gamsar da jama’a kan manufofin Tinubu

Wani babban lamari da ke gaban sabon shugaban na APC, shi ne neman jama’a su sake amincewa da jam’iyyar sakamakon yadda wasu manufofin gwamnatin tarayyar ƙasar suka sa wasu suka yanke ƙauna da jam’iyyar.

Duk da cewa Shugaba Tinubu ya bayyana wasu manufofin gwamnatinsa irin su cire tallafin man fetur a matsayin wasu manufofi da za su amfani ‘yan ƙasar a nan gaba, jama’ar ƙasar da dama na buƙatar su gamsu da hakan ta hanyoyi daban-daban.

Hakan ne ya sa ake ganin shugaban jam’iyyar na da rawar da zai taka wurin ganin jama’ar ƙasar sun sake aminta da jam’iyyar.

Inganta dimokuraɗiyyar cikin gida

Ɗaya daga cikin manyan ƙorafe-ƙorafen da ake yi a kan APC shi ne rashin dimokuraɗiyya a cikin gida.

Waɗannan sun haɗa da zargi rashin gaskiya da adalci a zaɓen 'yan takara da kuma yanke hukunci kan muhimman abubuwa a cikin jam’iyya.

Misali a zaɓen ƙananan hukumomi, an ga yadda aka rinƙa kokawa a wasu jihohin inda aka yi ta zargin ɗauki-ɗora kawai aka yi a matakin jam’iyya.

A Jihar Legas kaɗai sai da aka rubuta takardar koke fiye da 100 kan wannan matsalar.

Ƙalubale ne ga shugaban jam’iyyar ya yi tsayin daka wurin magance siyasar ubangida da danniya da kuma aikata son rai a harkokin jam’iyyar.

Tunkarar zaɓen 2027

Babu wani babban ƙalubale ga kowace jam’iyya da ya wuce cin zaɓe. Tunanin ko wane ɗan siyasa da wanda ya fito takara shi ne ta yaya zai ci zaɓe?

Tuni dai za a iya cewa aka kaɗa gangar siyasa a Nijeriya inda aka fara ganin yadda ‘yan siyasa ke fitowa suna shirin haɗaka domin samun nasara a zaɓe mai zuwa.

Wannan ya kasance babban ƙalubale ga Ali Bukar Dalori domin ya fito da hanyoyi da kuma dabaru ta yadda jam’iyyarsa za ta kai ga nasara a zaɓen 2027.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us