Daga ranar Laraba 8 ga watan Zul Hijja da ya yi daidai da 4 ga watan Yuni miliyoyin Musulmai daga sassan duniya suke fara aikin Hajjin bana, ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar.
Ga wasu daga daga cikin ayyukan da mahajjata ke yi a lokacin aikin Hajjin.
Ihrami/Niyya
Kafin a fara aikin Hajji ya wajaba mahajjata su ɗau harami. Ana fara wannan ne da ɗaura niyyar yin aikin hajji kuma maza su saka fararen ƙyallaye biyu, kuma mata su saka kaya da zai rufe musu jikinsu. Waɗannan fararen kayayyakin na bai-ɗaya suna cire duk wani bambanci tsakanin masu kuɗi ko mulki da talakawa, lamarin da ke nuna daidaiton mutane a gaban Allah.
Rana ta 1-Fita Mina
8 ga watan Zul-Hijja ne ake fara aikin Hajji, inda mahajjata za su sanya ihrami su kuma ɗauki niyyar fara aikin, sannan su nufi Mina, da ke da nisan kilomita 8 gabas da birnin Makka, inda za su kwana suna ibada da addu’o’i.
An fi sanin Mina a matsayin wani “birnin tantuna” saboda tantuna 100,000 da ke wurin inda miliyoyin mahajjata za su shafe wasu kwanaki.
Rana ta biyu- Tsayuwar Arafa
A rana ta biyu ta aikin Hajji ne alhazai za su yi sammako zuwa filin Arafa, kimanin kilomita 15 daga Mina. Za su yini a filin har zuwa faɗuwar rana suna ibada da addu’o’i da neman gafara.
Tsayuwar Arafa ita ce mafi muhimmancin ayyukan Hajji, duk wanda bai samu tsayuwar Arafa ba to ba shi da aikin Hajji.
Alhazai suna haɗa sallar Azahar da La’asar kuma su yi su ƙasaru a Filin Arafa, sannan suna shagala da yin addu’o’i har zuwa faɗuwar rana.
Rana ta 2-Kwanan Muzdalifa
Bayan faɗuwar rana, mahajjata za su kama hanyar zuwa Muzdalifah, da ke da nisan kimanin kilomita 9 daga filin Arafa. A wannan filin, za su yi sallar Magariba da Isha kafin su tsinci duwatsu domin jifan da za su yi washe gari.
Rana ta 3 - Ranar jifa/Sallah
A rana ta uku da fara aikin Hajji ne mahajjata suka fi gudanar da ayyukan ibada da yawa a rana guda. Abubuwan da ake yi a ranar su ne kamar haka:
Jifa a al-Jamarat al-Kubra
Mahajjata za su koma Mina daga Muzdalifa, inda za su yi jifa da ƙananan duwatsu bakwai. Suna jifan ne a wajen jifa mafi girma, wanda wasu ke cewa ‘Babban Shaiɗan’.
Jifan, kwaikwayon abin da Annabi Ibrahim ya yi ne lokacin da Shaiɗan yake ƙoƙarin ruɗinsa daga gudanar da abin da Allah ya yi masa umari da shi a jarrabawar da Ya yi masa ta yanka ɗansa Annabi Isma’ila.
Yanka
Alhazai ko kuma wakilansu za su yi yankan hadaya domin tunawa da yadda Annabi Ibrahim ya yi na sadaukar da ɗansa domin biyayya ga Allah, wanda Ubangiji ya fanshi ɗan da wani rago mai girma.
Aski
Maza suna aske ko kuma rage gashin kansu, su kuma mata sukan yanka kaɗan daga gashin kansu. Wannan na nuna sabunta rayuwa ta imani.
A wannan rana, Musulmai daga sassan duniya za su yi bukukuwan babbar Sallah ko kukuma sallar Layya, inda suke yanka dabbobinsu domin kyaukwayon abin da alhazai suke yi.
Ɗawaful Ifada
Alhazai za su koma Makka inda za su gudanar da ɗawafi da kuma tafiya tsakanin Safa da Marwa sau bakwai. Ana yin sa’ayi ne domin tunawa da yadda Nana Hajara ta yi ta fafatukar nema wa ɗanta Annabi isma’il ruwa, wanda ke nuna imani da haƙurinta.
Rana ta 4 zuwa 5
Alhazai za su koma Mina inda za su ci gaba da jifa a dukkan wuraren jifa uku a ko wace rana.
Wasu alhazan suna zama tsawon kwana biyu, yayin da wasu su kan cika kwana na uku a Mina domin cika jifan.
Daga nan ne kuma alhazai ke kammala aikin Hajji, inda wasu suke fara barin birnin Makka tun daga wannan rana.
Ɗawafin Bankwana
Kafin Alhazi su bar Makka, suna gudanar da ɗawafi na ƙarshe da aka fi sani da ɗawafi na bankwana, abin da ke nuna bankwana da wuri mai tsarki.
Baya ga waɗannan ayyuka na ibada, alhazai suna zuwa birnin Madina domin yin ziyara a ƙabarin Manzon Allah SAW da yin sallah a Masallacinsa, wanda shi ne masallaci na biyu mafi daraja a wajen Musulmai bayan Masallacin Ka’aba da ke Makka.