A makonnin baya ne babban hafsan sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya ba da shawarar ƙasar ta gina katanga da za ta zagaya duka iyakokinta da ƙasashen da ke fuskantar matsalolin tsaro, domin rigakafin kwararowar ‘yan-ta’adda da makamai barkatai.
An samu martani daban-daban game da wannan shawara, ganin cewa ‘ta zo da ba-zata’, musamman saboda yadda babban jami’in sojin kasar ne ya ba da ita.
Duk da amannar cewa matakin gina katangar kan-iyaka mataki ne da ya yi aiki a wasu kasashe, hakan bai hana masu sharhi yin tsokaci kan gagarumin kalubalen da wannan shawara za ta fuskanta tun a matakin shirya ta, da aiwatar da ita, da kuma tasirinta.
A wata hira da aka yi da tsohuwar shugabar hukumar shige da fice ta Nijeria, Caroline Wura-Ola Adepoju, a Satumbar 2023, jam’iar ta ce, “Yana da wuya a ce Nijeriya ta gina katanga a duka iyakokinta da kasashe makwabta”.
Duk da katangar kan iyaka tana yin tasiri a wasu lokuta, cewar jami’ar, abin da Nijeriya ke bukata shi ne cudanya dabarun tsaro, ciki har da amfani da fasaha, da tattara bayanan sirri, da horar da jami’ai, da kuma matakan diflomasiyya.
Tsaka mai wuya
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, wannan ne karo na farko da wani babban jami’in tsaron gwamnati ya bijiro da irin wannan gagarumar shawara ta gina katangar kan iyaka.
Nijeriya ƙasa ce da ke yammacin Afirka, wadda ƙasashe huɗu suka zagaye, baya ga wani yankin iyakarta da ke gaɓar tekun Atalantika.
Cikin gomman shekarun baya-bayan na, ƙasar tana fuskantar matsalolin tsaro a cikin gida, da maƙota, da kuma barazanar rashin jituwa da wasu ƙasashe maƙwabtanta. Sannan ga kwararar masu aikata laifuka, da ‘yan ci-rani, da kuma masu safarar mutane, da makamai, da miyagun ƙwayoyi.
Shekara biyu bayan hawan shugaba Bola Tinubu mulkin Nijeriya, babban jami’in sojin da ya naɗa a matsayin babban kwamandan rundunonin sojin ƙasar, Janar Christopher Musa ya bijiro da shawarar gina katanga a iyakokin ƙasar don kawo ƙarshen matsalolin ta’addanci.
A wani jawabi da ya gabatar cikin watan Yuni a babban birnin Nijeriya, Abuja, Janar Musa ya nemi mahukuntan ƙasar su amince da gina ganuwa tsakaninta da maƙwabtanta huɗu, “domin kawar da shigowar ƙungiyoyin ‘yan bindiga waɗanda ke rura watar rikice-rikice cikin ƙasar”.
Baya ga alfanu wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar jama’a, ingancin iyakokin ƙasa yana da tasiri wajen kula da tattalin arziƙin ƙasa. Akwai lokuta a baya da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rufe iyaka don hana shigowa da shinkafa da wasu kayayyaki cikin ƙasar.
Ko a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, bayan juyin-mulkin da aka yi a Nijar, Nijeriya ta rufe iyakar ƙasarta da Nijar, wanda tasirin hakan ya dogara kan ƙarfin jami’an kan iyaka wajen hana masu satar hanya.
Sai dai akwai batutuwa da dama da ake ganin sai an duba su kafin a iya ganin tasirin tabbata, da kuma tasirin ganuwar tsaro a iyakokin Nijeriya.
Na ɗaya: Batun dacewar ganuwar tsaro
Babban hafsan sojin Nijeriya ya ba da misali da wasu ƙasashe da suka yi nasarar gina ganuwar tsaro da ta shingensu daga maƙwabtansu. Misalin farko da ya ambata shi ne ƙasar Pakistan wadda ta shinge iyakar kilomita 1,350 tsakaninta da Afghanistan. Sai kuma Saudiyya mai shingen kilomita 1,400 da ya raba ta da Iraki.
Nijeriya dai na da iyakoki da ƙasashen Nijar, da Kamaru, da Benin, da Chadi, waɗanda duka suna fama da rikice-rikicen siyasa, da na ta’addanci, da na ƙungiyoyin ‘yan bindiga, muasamman masu alaƙa da yankin Sahel na yammaci da tsakiyar Afirka.
Duk da cewa yawancin rikice-rikicen da Nijeriya ke fama da su daga cikin gida suka fara, gwamnatin ƙasar tana ɗora alhakin ta’azzarar wasu matsalolin kan yawaitar kwararar mayaƙa da makamai daga ƙasashe makwabtanta.
Akwai zarge-zargen cewa matsalar makiyaya masu ɗauke da makamai, da ‘yan fashin daji, da masu tsattsauran ra’ayin addini, da ƙungiyoyin ƙabilanci, da ƙungiyoyin ‘yan a-ware a Nijeriya duka suna samun tallafi daga ƙasashen waje.
Babban misali shi ne safarar makamai daga ƙasar Libya, tun bayan faɗuwar gwamnatin shugaba Mu’ammar Gadafi a shekarar 2011, wanda ya haddasa rugujewar rundunonin sojin ƙasar, da wawaso kan ɗakunan adana makaman ƙasar.
An yi ta fasa-ƙwaurin irin waɗannan makamai a kan iyakokin Afirka, har ta kai ga wasu ƙungiyoyin ta’addanci a Nijeriya suna amfani da waɗannan makamai wajen kai hare-hare kan soji da farar-hula a ƙasar.
Baya ga Libya, akwai rahotannin safarar makamai daga ƙasashen Sahel da ke fama da rikici, kamar Mali da Burkina Faso. Sannan akwai masu fasa-ƙwaurin makamai ta iyakokin hukuma, inda suke ɓoye su cikin wasu halattattun kayayyaki.
Abin tambaya a nan shi ne, katangar iyaka za ta hana safarar mutane da makamai ta sararin samaniya? A zamanin yau, ayyukan soji da ma na mayaƙan sa-kai suna gudana a sararin sama, inda jirage masu matuƙa da marasa matuƙa ke taka babbar rawa.
Na biyu: Batun tsayin iyakokin
A arewa maso gabashi, Nijeriya na da iyaka mai tsawon kilomita 1,975 tsakaninta da Kamaru. Sannan akwai tsawon kilomita 1,500 na iyakarta da Nijar a arewaci. A yammaci kuwa, Nijeriya na da iyakar kilomita 800 da Benin. Sai kuma gajeruwar iyaka ta kilomita 85 da Chadi.
Baya ga sanannun hanyoyin shige da fice zuwa cikin ƙasar, masu fasa-ƙwauri sun samar da haramtattun hanyoyin da suka aikata laifukansu. Sannan mayaƙa da mahara kan shiga ƙasar ta cikin dazuka da tsaunukan da suke da wahalar cimmawa wajen jami’an tsaron ƙasar.
Duk da cewa gina shinge da zai bai wa Nijeriya kariya daga barazanar tsaro zai taimaka mata wajen ɗorewa a matsayin ƙasa mai ‘yanci da iko da iyakokinta, tsayin iyakokin da ya haura kilomita 4,000 wani babban ƙalubale ne wajen samar da kuɗin ginawa da kula da ganuwar.
A wannan zamani, ba a gina ganuwa ba tare da an saka mata na’urorin saka-ido ba, kamar sanso mai ankararwa idan an raɓe ta ko an taɓa ta, da kyamarori masu ɗaukar hoton abin da ke gudana. Sannan dole a saka motocin suntiri da jiragen sama masu shawagi a kewayen katangar.
Wannan na nufin sai an samar da tituna a gefan katangar don samar da hanyar da motocin sintiri za su ringa jigila, da jami’an tsaro masu lura da tsaron kan iyakokin. Kum dole hanyar ta zama mai yalwar da za ta ba da damar zirga-zirga a koyaushe.
Kenan, baya ga gina katanga mai tsayin sama da kilomita 4,000, sai an gina titi mai kwatankwacin wannan zango, tare da na’urorin sadarwa da fasahohin sanya-ido.
Na uku: Batun ƙarancin jami’an tsaro
Bayan an gina ganuwa, to fa akwai buƙatar sanya jami’an da su kula da ita don ganin ba a lalata wani ɓangarenta ba, kuma ba a haura ta ba. Wannan aiki na buƙatar jami’ai da za su yi aiki ba dare-ba rana, da na’urorin zamani kamar jirage da sanso-sanso.
Sai dai, yawaitar rikice-rikice a yankuna da dama na cikin Nijeriya, ayyukan jami’an tsaro musamman na fannin sojojin ƙasar ya yi yawa, kasancewa kusan duka jihohin ƙasar na buƙatar kasancewarsu don daƙile matsaloli.
Rikicin Boko Haram wanda aka shekara 16 ana fama da shi a yankin arewacin Nijeriya, shi ne ya fi ɗaukar hankalin rundunonin tsaron ƙasar, daga sojoji zuwa jami’an shige da fice, da na ‘yan sanda, har ma da ƙungiyoyin ‘yan sa-kai masu taimaka wa jami’an tsaro.
Bayan lafawar hare-haren Boko Haram, cikin shekaru 10 na bayan nan, an samu ɓullar wasu ƙungiyoyin ta’addanci, kamar na Daesh da Al-Qaeda ta yammacin Afirka, waɗanda suke addabar yankin arewa maso gabas da arewa ta tsakiyar Nijeriya.
Baya ga ƙaranci, akwai batun ƙwarewar jami’an tsaron iyakokin ƙasa wajen kare Nijeriya daga baƙin-haure masu hatsari.
Tsohuwar shugabar hukumar ta taɓa kokawa kan ƙarancin kayayyakin aiki na zamani da ake iya gano haramtattun kaya, kamar makamai yayin tantance masu shigowa cikin ƙasar.
Baya ga makamai, hukumar tsaron Nijeriya ta sha ambata cewa tana kama baƙin-haure cikin mayaƙan ƙungiyoyin ta’addanci, kama daga Boko Haram, da ‘yan fashin daji, da makiyaya masu ɗauke da makamai.
Tsohuwar shugabar hukumar shige da fice ta Nijeriya, Caroline Adepoju ta ce, “Ba ma buƙatar katanga, gadoji muke buƙatar ginawa. Ƙaura wani babban ɓangare ne na zamantakewa da tattalin arziƙi. Abin da ya kamata mu yi shi ne dakatar da shigowar ɓata-gari”.
Ta kuma ƙara da cewa, “Nijeriya babbar yaya ce a Afrika. Mu nahiya ce guda mai faɗi da ta haɗa da duka ƙasashen da ke kudu da Sahara. Nijeriya na taka babbar rawa wajen ci gaban Afirka. Bai kyautu mu rufe iyakokinmu ba”.