Abin da ya sa Kabul zai iya zama babban birni na farko da zai fuskanci matsalar rashin ruwa a duniya
RAYUWA
6 minti karatu
Abin da ya sa Kabul zai iya zama babban birni na farko da zai fuskanci matsalar rashin ruwa a duniyaIdan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, to Kabul tana fuskantar "mummunan bala'in jinƙai".
Experts say the international presence in Afghanistan brought in billions of dollars, yet little of it went into long-term water infrastructure. / AP
23 Yuli 2025

Birnin Kabul yana fuskantar babbar matsala. Rahoton da Ƙungiyar Agaji ta Mercy Corps ta fitar kwanan nan ya bayyana cewa babban birnin Afghanistan na iya zama birni na farko a duniya da ruwansa zai ƙare gaba ɗaya cikin shekaru biyar masu zuwa.

Shafin intanet na Mercy Corps, ya ce “kungiyar agaji ce ta duniya” da ke aiki don taimaka wa mutanen da suke cikin mawuyacin hali su gina al’ummomi masu tsaro, adalci da wadata.

Abin da ke faruwa yanzu

Matakin ruwan karkashin kasa a Kabul ya ragu da kusan mita 30 cikin shekaru goma da suka gabata, wanda hakan ya tilasta mutane su ci gaba da haƙa rijiya mai zurfi sosai.

A yanzu haka, birnin na amfani da kubik miliyan 44 na ruwa fiye da yadda yanayi ke iya maye gurbinsa a kowace shekara. Idan wannan ya ci gaba, ruwan karkashin kasa da ke shayar da birnin zai iya ƙarewa nan da shekarar 2030, wanda zai tilasta wa mutane miliyan uku yin hijira.

Kusan rabin rijiyoyin da aka haƙa a Kabul sun riga sun bushe. Sama da rijiyoyi 120,000 aka haƙa ba tare da wani tsari ba, kuma masana’antu da gonaki da dama suna ci gaba da amfani da ruwan karkashin kasa ba tare da wani kulawa ba.

Mutane yanzu suna haƙa rijiyoyi masu zurfi fiye da da, wasu ma suna kai wa har mita 300 karkashin kasa — wanda ya kai tsawon hasumiyar Eiffel.

Fiye da rabin gidajen da aka bincika sun ce dole ne su sake haƙa rijiyoyinsu aƙalla sau ɗaya cikin shekaru biyar, wasu har sau biyar.

Ruwan da ake samu yanzu yawanci ba shi da tsafta. Har zuwa kashi 80 cikin 100 na ruwan karkashin kasa a birnin yana dauke da datti daga najasa da ɓurɓushin sinadarai kamar arsenic da nitrates.

A wasu yankuna na Kabul, najasa daga gidaje da masana’antu na shiga kai-tsaye cikin kasa ko kuma cikin magudanan ruwa a fili, wanda ke ƙara gurbata ruwan sha.

Mutane da dama suna korafin cewa ruwan yana wari, yana da dandano mara kyau ko kuma yana jawo rashin lafiya.

Me yasa wannan yake da muhimmanci

A yau, kashi 20 cikin 100 ne kawai na gidaje a Kabul ke samun ruwa ta hanyar bututun ruwa.

Kabul ya kasance cibiyar sojojin haɗin gwiwa na Amurka, waɗanda suka mamaye Afghanistan tsawon shekara ashirin. An kashe biliyoyin daloli wajen kokarin kayar da Taliban, waɗanda yanzu suke mulki.

Rahoton ya nuna yadda cin hanci da rashawa ya mamaye gwamnatocin da Yammacin Duniya suka goyi baya a Kabul.

A shekarar 2006, wani shiri na Bankin Duniya na dala miliyan 40 ya yi niyya don haɗa rabin birnin da bututun ruwa zuwa shekarar 2010, amma ba a cim ma wannan burin ba.

Yanzu yawancin mutane suna dogaro da rijiyoyi ko kuma suna sayen ruwa daga masu sayarwa masu zaman kansu. Wasu iyalai suna kashe har kashi 30 cikin 100 na kudin shigarsu kawai don siyan ruwa.

A unguwar Khair Khana, farashin ruwa ya zarce na abincin da wasu gidaje ke saye. Motocin ruwa suna cajin har zuwa $5 a kowace cubic metre, wanda ya ninka farashin tarihi sau 12.

Wannan matsalar ba kawai ta muhalli ba ce, har ma ta shafi al’umma, tattalin arziki da siyasa. Rashin ruwa ya riga ya tilasta rufe wasu makarantu da asibitoci.

Amfanin gona yana lalacewa saboda ƙaruwar gishiri da raguwar ruwan karkashin kasa.

Farashin alkama ya karu da kashi 40 cikin 100 tun daga shekarar 2021, kuma har ma da ayyukan noma 500,000 suna cikin haɗari. Iyalan da dama suna shiga bashi kawai don siyan ruwa.

Tarihin matsalar

Birnin Kabul yana dogaro da dusar ƙanƙara daga tsaunukan Hindu Kush don biyan bukatun samar da ruwansa. Amma matsalar sauyin yanayi ta rage zubar dusar ƙanƙara da kusan kashi 20 cikin 100 tun daga shekarar 2014, kuma gajerun lokutan sanyi suna nufin ƙarancin dusar ƙanƙara.

A lokacin hunturun 2023-2024, ƙasar ta samu kusan rabin ruwan sama na yadda aka saba samu kawai.

Karancin ruwa na baya-bayan nan, wanda ya ɗauki lokaci daga 2021 zuwa 2024, ya shafi mutane sama da miliyan 11. Kulawar gwamnati tana da rauni. Dokokin da suka shafi haƙa rijiyoyi ba su da kyau kuma ba a cika bin su ba. Wasu kamfanonin haƙa suna aiki ba tare da izini ba, yayin da wasu suka ce yana da sauƙi a samu izini idan mutum yana da alaƙa da gwamnati.

A halin yanzu, yawancin kayan aikin ruwan birnin suna lalacewa ko kuma ba a kammala ba. Wani babban wurin tace ruwa a Baghrami, wanda aka gina da tallafin Amurka, bai taɓa aiki da cikakken ƙarfin sa ba. Duk da haka, wani ƙaramin shiri a gundumar Surobi, wanda aka kammala a shekarar 2024, yanzu yana samar da tsaftataccen ruwa ga gidaje sama da 1,200, wanda ke nuna cewa hanyoyin magance matsaloli a matakin al’umma na iya aiki.

Amma wannan ba shi ne kawai ba. Asalin matsalar ruwan Kabul ya wuce karancin ruwa da yanayin ƙasa; yana kuma da alaƙa da shekaru na rashin tsari da kuma gazawar tallafin ƙasa da ƙasa.

Masana sun ce kasancewar ƙasashen duniya a Afghanistan bayan 2001 ya kawo biliyoyin daloli, amma kaɗan daga ciki aka saka a cikin kayan aikin ruwa na dogon lokaci.

Yawancin tallafin ya mayar da hankali kan ƙoƙarin wucin gadi ko kuma waɗanda ba su haɗu ba, waɗanda suka yi watsi da buƙatun tsarin ruwa na Kabul.

Bugu da ƙari, wani rahoto na 2020 daga US Special Inspector General for Afghanistan Reconstruction ya gano cewa kusan dala biliyan 19 — kusan kashi ɗaya bisa uku na duk tallafin sake gina ƙasa — sun ɓace saboda zamba, ɓarna ko kuma rashin amfani, wanda ya ƙara nuna gazawar dabarun ci gaba na baya.

Me za a yi gaba?

Manyan ayyuka sun tsaya cik. Madatsar Ruwa ta Shahtoot da aka jima ana jira wacce za ta iya samar da ruwa ga mazauna miliyan biyu amma har yanzu babu kuɗi, kuma tana fuskantar matsalolin siyasa da makwabciyar ƙasar Pakistan.

Wani bututun ruwa da aka shirya daga Kogin Panjshir na iya rage dogaro da ruwan karkashin kasa, amma yana jiran amincewar gwamnati da saka hannun jari.

Raguwar tallafin ƙasashen duniya ya kara ta’azzara lamarin. Tun bayan dawowar Taliban kan mulki a shekarar 2021, an dakatar da tallafin WASH na kusan dala biliyan 3 na tallafin ruwa da tsaftar muhalli.

Fiye da kungiyoyin agaji 50 sun rage ko dakatar da ayyukansu a kasar. Sannan dan dakatar da wani muhimmin dandali na haɗin gwiwa mai suna ReportHub saboda rashin kuɗi.

Ba tare da ɗaukar matakin gaggawa ba, Kabul na fuskantar “babbar matsalar jinƙai da ba a taɓa gani ba,” in ji rahoton Mercy Corps.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us