Daga Firmain Eric Mbadinga
A sararin samaniyar Kamaru, jirage marasa matuka na Tagus sun dinga shawagi irin na jiragen sama da aka sani.
Suna lulawa sama sosai, za a iya zaton irin tsuntsayen nan ne masu karo jirage a kololuwar sama.
Sai mutum ya kula sosai zai iya gano cewa wadannan ba tsuntsaye ba ne, a’a karfafan jiragen sama maras amatuka ne da ake juya su daga nesa da suke bayyana fasahar kere-kere da basira ta Kamaru.
Biyem-Assi Camtel, daya daga yankunan masu karamin karfi a Yaounde, nan ne wajen da aka haifi Tagus.
Yau, sunan ya zama abin alfahari da sanya mutane karsashi a duk lokacin da wadannan jiragen drone suka tashi sama don yin gaji.
A shekaru hudu da suka gabata, kamfanin Drone din Tagus na kan gaba wajen tsara wa da sayar da wadannan kayan fasahar zamani da ake amfani da su a fannoni daban-daban da suka hada da tsari, noma, inshora da nishadi.
Borel Taguia ne ya kirkiri wannan, dan kasar Kamaru mai shekaru 30 da ke da basirar fasahar kere-kere da warware matsaloli, kuma yake da burin samun nasaraa rayuwa sama da gina kai kawai.
Buri ya tashi sama
Fasahar drone, wadda ke habaka cikin hanzsri a duniya, na kawo babban sauyi a fannoni da dama daga tsaro zuwa ayyukan noma, sufurin kayayyaki zuwa kula da lafiya.
Musamman, jiragen da suke marasa matuka ne leken asiri na UAV da masu dauke da makamai na UCAV sun samu babban matsayi a fannin tsaro da ayyukan bincike a leken asiri.
A ‘yan shekarun nan, Turkiyya na daya daga cikin kasashen da suka yi fice wajen zuba babban jari a wannan fanni, inda ta ja hankalin duniya da drone din ta masu karfi.
Wannan salo na duniya ya zama masamar ilhama ga matasa da dama da suka fahimci fasahar a Afirka, kamar Borel, wanda ke da manufa da burin bayar da gudunmawarsu wajen cigaban kasarsu.
Shirin Borel ya faro ne da aniyarsa ta taimakawa rundunar tsaron kasarsa wajen karfafa ayyukan leken asiri ta yadda za su mayar da martani ga barazanonin ‘yan ta’adda.
Babban abinda ya aingiza shi kirkirar shi ne irin hare-haren da ‘yan ta’addar Boko Haram ke kai wa a arewacin kasar mai nisa.
“Na fara tunani kan wacce irin gudunmawar da zan bayar ga sojojin Kamaru? Na yi mafarki: wai ina samar da wani inji da ke tashi sama mai amfani da makamashin hasken rana,” ya fada wa TRT Afrika.
“Domin ganin tunanina ya samu wanzuwa, akwai bukatar kudi da kayan aiki. Tom, sai na shiga wata gasa da ake kira ‘Graine d’inbenierie’, inda aka zabi aikin da na yi a matsayin daya daga cikin uku mafiya kayatarwa a Kamaru. Wannan ya ba ni damar samun kudade don samar da jirgin drone na farko. Na kuma samu tallafin kudade daga iyayena.“
Kokarin Borel a makaranta ma na da kayatarwa - ya kammala digiri makarantar nazarin fasaha da sana’o’i ta kasa da ke Maroua da sakamako mai kyau na 18.05/20 a fannin makamashi mai sabuntuwa, wanda ya samar masa babbar daraja. A yayin da yake kammala rubutunsa, ya samu daraja ta daya.
Fasahar da aka yi wa rajista
Borel ya samu damar ganin an yi rajista a karon farko ga jirgin tagus drone na zamani da kamfanin ya samar.
Buri da manufarsa sun janyo hankalin masu zuba jari na kasa da kasa, wanda ya bawa kamfanin damar amfani da iliminsa wajen samar da jiragen don biyan bukatun fannoni da dama a Afirka, ciki har da na kula da lafiya, ayyukan noma, sufuri, da duakar hoto.
“Mun samar da drone da ake amfani da su a bangarori daban-daban,” in ji Borel. “Tun daga samfura manya zuwa kanana, mun samar da nau’ika ga dukkan bukata.
“Na baya bayan nan da muka saki shi ne T24 drone, yana da kyau ga yaran da ke son zama matukan jiragen sama.
“Ana sayar da shi kan kudi CFA 25,000 ($39.9), kuma kudaden na isa har ga CFA 1,300,000 ($2,076). Manufar ita ce a ga koya ya iya mallaka.”
A shekaru hudu da kafa kamfanin, Tagus Drone ya samu ribar dala miliyan 1.95, kimanin sama da CFA biliyan 1.3.
A kowace shekara, muna bayar da riba ga wadanda suka sayi hannayen jarin kamfaninmu,” in ji Borel, fuskarsa na bayyana tunani.
Siffa ta musamman
A yayin da darussa da dama suka bayyana yadda ake samar da drone, kamfanin Tagus Drone ya yi fice da zabi
Masu sayen kayan kamfanin na cikin Kamaru da ma wajen kasar, kuma a bangarorin gwamnati da ‘yan kasuwa, wanda shaida ce da ke tabbatar da ingancin jiragen da aka samar a cikin gida, da kuma bukatar a ci gaba da kirkirar sabbin kayan fasaha.
Ga wadanda suka shaida daga kurkusa yadda Tagus Drone ke tashi sama, za su gane wannan ba wai zuba jari a fasahar kere-kere kawai ba ne.
Labarin matashi injiniya da ya yi bajinta da samar da kyakkyawan abu daga kasar ta Tsakiyar Afirka.