A ranar 29 ga Mayun 2025, shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai cika rabin wa’adin mulkinsa na shekara hudu, kasancewra ya karbi mulki daga hannun tsohon shugaban Muhammadu Buhari ranar 29 ga Mayun 2023.
Cikin shekaru biyun da ya yi yana mulkin Nijeriya, Shugaba Tinubu ya kaddamar da tarin manufofi da shirye-shirye, tare da daukar wasu muhimman matakai da suka yi babban tasiri a ciki da wajen Nijeriya.
Matakan sun hada da wadanda suka shafi tattalin arziki, da siyasa, da diflomasiyya, da ilimi, da dalibai, da kuma nade-naden manyan jami’ai da jagororin hukumomin gwamnatin kasar. Ga wasu manya guda biyar daga cikinsu sauye-sauyen da suka faru.
Cire tallafin man fetur
Tun a filin da aka gudanar da bikin rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayun 2023, matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauak na farko shi ne sanar da cire tallafin man fetur, wanda gwamnatocin baya suka dade suna kokarin yi.
A jawabinsa na kama aiki, Shugaba Tinubu ya ayyana kawo karshen tallafin da gwamnatin tarayya ke biya kan duk litar man fetur da ake sha a kasar. Ya ce ya yi hakan ne don rage kashe kudin gwamnati.
Tsarin tallafin mai yana aiki a Nijeriya tun shekarun 1970. Don haka dakatar da tallafi ya haifar da hauhawar farashin mai, da sauran kayayyaki a kasuwannin kasar.
Nijeriya ita ce ta fi samar da mai a Afirka, amma matakin tashin farashin mai ya sa gwamnati ta fito da wani shiri na mayar da motoci su koma aiki da gas na CNG.
Shugaba Tinubu ya sanar da cewa’yan kasar suna da zabin sayan man fetur a kan farashin da yakan kai Naira 1,000, ko kuma su koma amfani da makamashin iskar gas wato Compressed Natural Gas (CNG), wanda ake sayar da mita daya kan Naira 200.
Shugaban ya ce gwamnati ta samar da wani tsari da za a rika mayar da motocin haya da suke amfani da man fetur, zuwa masu amfani da iskar gas na CNG wanda yin sauyin kyauta ne.
Da ma dai ’yan kasar sun shafe tsawon rayuwarsu ne suna amfani da man fetur, a matsayin babban makamashin da ababen hawa da injunan janaretonsu suke amfani da su.
Sai dai Mayun 2024, gwamnatin Tinubu ta haramta wa ma’aikatun kasar sayen sabbin motoci masu amfani da man fetur, inda ta bayar da umarnin su koma sayen motoci masu amfani da gas din CNG, wadanda ba sa gurbata muhalli sosai.
Karya darajar Naira
Wani gagarumin mataki da shugaban Bola Tinubu ya ɗauka shi ne na karya darajar naira har karo biyu. A baya gwamnati na zuba biliyoyin daloli a kasuwar canjin kudade don kare kudin kasar daga faduwa yayin gogayya da kudade kamar dala da fam.
Bayan dakar da tallafa darajar naira, kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje a Nijeriya sun nuna yadda kuɗin ƙasar ya yi rasa daraja idan an kwatanta shi da dallar Amurka.
An kai munzalin da darajar Naira ta yi mummunar faɗuwa, har sai da ta kai ana musayar kowace dala daya a kan Naira 1,900, lamarin da ya yi matuƙar tayar da hankali, tare da yin tasiri sosai kan farashin kayayyaki.
Sai dai ganin haka, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki tsauraran matakai a ƙoƙarin ceto darajar Naira, ciki har da tsare shugabanni biyu na kamfanin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto, wato Binance, - waɗanda ake zargi da yin amfani da manhajar wajen karya darajar Naira da zumman durƙusar da tattalin arzikin Nijeriya.
Sannan babban bankin kasar, CBN ya biya wasu kamfanoni kasar waje basussukan biliyoyin daloli da suke bin bashi, domin rage giɓin da ake samu a farashin dala a kasuwannin bayan-fage da kuma farashin gwamnati.
Sakamakon wannan sabon tsarin kudi, kamfanin zuba jari na duniya, Goldman Sachs, ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta farfaɗo, har ma ta koma ana musayar dala daya a kan Naira 1,200.
Sai dai zuwa tsakiyar shekarar an ta 2025, farashin dala da naira ya tsaya ne a wuraren naira 1600 duk dala guda. A 2025, Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Nijeriya zai samu haɓaka da kashi 3.6.
Biyan bashin IMF
Nijeriya ta kammala biyan bashin dala biliyan 3.4 da ta karbo daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya, (IMF) tun a Afrilun 2020, kuma a yanzu an cire kasar daga jerin ‘yan bashi a asusun.
Kasar ta ciyo bashin ne don magance radadin tasirin annoban COVID-19, bayan da a lokacin farashin gangar mai a duniya ya karye, wanda ya illata harkokin tattalin kudade a Nijeriya, kasancewar tattalin arzikinta ya dogara sosai kan kudin-shiga daga sayar da danyen mai.
Ranar 8 ga Mayun 2025 IMF ta tabbatar da cewa zuwa 30 ga Afrilun 2025, Nijeriya ta “kammala biyan tallafin kudin da ta karba.” Kuma a yanzu babu bashi a kanta.
Wasu bayanai daga Ofishin Harkokin Bashi na Nijeriya, ya nuna cewa a 2024, kasar ta kashe dala biliyan 4.7 wajen hidimar basukan kasashen waje. Daga wannan adadi, dala biliyan 1.6 ya tafi wajen IMF.
Sai dai, wakilin IMF a Nijeriya, Christian Ebeke ya ce, “Ana sa ran Nijeriya za ta biya wasu karin kudaden da ake caji kasa don cika ka’idar damar fitar da kudin ajiyarta daga asusun, wato Special Drawing Rights ko SDR, wanda ya kai kusa dala miliyan 30 duk shekara.”
Tsaro kan manyan hanyoyi
Hanyar Kaduna zuwa Abuja a a arewa maso yammaci wata hanya ce mai matukar muhimmanci a Nijeriya, inda dubban motoci ke bin hanyar a kullum don safarar mutane da kayayyaki.
Tun a zamanin Shugaba Muhammadu Buhari, hanyar ta fuskanci hare-haren masu garkuwa da mutane, wadda ta yi kamari sosai da hana walwalar jama’a.
Amma cikin rabin zangon gwamnatin Bola Tinubu, jama’a sun shaida samun nasara kan matsalolin tsaron a wasu yankunan kasar, ciki har da titin Kaduna-Abuja, duk da ta’azzarar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a wasu yankunan.
A kwanan nan ana ambato mashawarcin shugaban Nijeriya kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, yana cewa gwamnatinsu ta kyautata tsaro a kasar da daƙile ta’asar kashe-kashen jama’a da lalata wurare da sace-sacen jama’a.
Kalaman na Ribadu sun nuna cewa cikin shekara biyu da hawan Shugaba Tinubu kan mulki, an kashe ‘yan Boko Haram fiye da 13,543, sannan an ƙwato makamai fiye da 11,000 da kuma lalata su a hannun ‘yan ta’adda.
Cikin matsalolin da ya ce an ci karfinsu, akwai na ta;addancin Boko Haram a arewa maso gabas, da ‘yan fashin daji a arewa maso yamma, da ‘yan awaren IPOB/ESN a kudu maso gabashin Nijeriya da yankin Neja Delta, da rikicin manoma da makiyaya a arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Dakatar da gwamnan Rivers
A tsakiyar watan Maris, shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, bayan dambarwar siyasar da aka yi ta yi a jihar tsakanin ofishin gwamna da majalisar jihar.
A wani jawabi na musamman da ya gabatar ga al’ummar kasar ta talabijin a ranar Talata 18 ga Maris, Shugaba Tinubu ya bayyana dakatar da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da da dukkan 'yan majalisar jihar na tsawon watanni shida.
Daga nan ya sanar da nada Vice Admiral Ibokette Ibas mai ritaya, a matsayin kantoman jihar da zai jagoranci al’amuran jihar na tsawon watanni shida na farko.
Da ma dai an yi watanni ana cece-kucen siyasa tsakanin gwamnan da toshon mai gidansa, kuma toshon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, wanda shi ne ministan babban birnin tarayya Abuja, kan kula da tsarin siyasar jihar mai arzikin man fetur.
Dab da dakatar da gwamnan, an samu fashe-fashen bututun mai a jihar ta Rivers, yayin da rikicin siyasa ya yi kamari. Sannan ma’aikatan gwamnati sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar adawa da shugabancin majalisar jihar karkashin Martins Amaewhule mai biyayya ga Wike.