A ranar 25 ga Mayun kowace shekara ake gudanar da bikin ranar Afirka tare da wasannin gargajiya da nuna kayan tarihi da yin waiwaye irin na siyasa.
Biki ne mai tarihi da ake gudanarwa a duk shekara. A 1958 a Gana, shugabanni daga kasashen Afirka da suka samu ‘yancin kai suka taru a karon farko tare a gudanar da Babban Taron Kasashen Afirka. Taro ne mai muhimmanda aka bayyana manufofin nahiyar da ba su ta’allaka da ‘yan mulkin mallaka ba.
Wakilan a sula halarci taron sun bayar da shawarar a samar da “Ranar ‘Yancin Afirka” don girmama ci gaba da samun ‘yancin kai da ake yi da karfafa gwiwar kasashen da har a sannan suke karkashin ‘yan mulkin mallaka.
Wannan kokari ba wai kawai a yi taro a tashi ba ne, na dauke da sakon aniyar bai daya ta auya fasalin makomar Afirka ta hanyar hadin kai da himmatuwa.
A yayin da kasashe da dama suka samu ‘yancin kai a shekarun da suka biyo baya, an samu habakar lamarin. Sannan ne aka cim-ma matsaya a ranar 25 ga Mayun 1963.
Kasashen Afirka talatin da biyu sun gana a Addis-Ababa, Ethiopia, suka kafa Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka (OAU), inda shugabanni da suka hada da Kwame Nkruma, Julius Nyerere, Haile Selassir, Gamal Abdel Nasser, Abubakar Tafawa Balewa, Sekou Toure, Leopols Senghor suka jagoranci kaddamar da kungiyar.
Tun wannan lokaci, ranar kafa OAU ta 25 da Mayu ta zama Ranar Afirka.
Tarayyar Afirka ta ce Ranar Afirka ba wai lokaci ne na waiwayen baya ba kawai, bigire ne na gina makoma.
Tana bikin tuna wa da sadaukarwa da aka yi a lokacin gwagwarmayar neman ‘yancin inda a gefe guda kuma suke duba ayyukan zaman lafiya, hadin kai da yalwa a nahiyar. Babbar manufar da ake da ita ita ce Burin 2063, wani kudiri na burin da Tarayyar Afirka ta kira “Afirka da Muke So.”
Shugaban Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya ce “A wannan Rana ta Afirka, Shugaban Tarayyar Afirka Mahmoud Ali Youssouf, ya bayyana cewa “A wannan Rana ta Afirka, muna murnar Kishin Afirka,gadonmu na bai daya, kuma karfin hadin kanmu. Muna sake sabunta aniyarmu ta tabbatar da adalci, gyare-gyare, da yalwata,Afirka ta kowa da kowa da ma ‘yan Afirka da ke kasashen waje.”
Taken Ranar Afirka ta 2025 na magana kan gwagwarmaya mai girma: Farfadowa da Adalci.
Masu fafutuka na cewa har yanzu ayyukan ‘uan mulkin mallaka na ci gaba da tasiri a tsakanin 'al’umun Afirka a yau, daga tattalin arziki mai rauni zuwa ga tsarin ilimi rugujajje.
A wajen wasu da dama, farfadowa ba iya bayar da kudade ba ne kawai - sun shafi amincewa. waraka, dawo da daraja da kima da kuma dora wa kasashen Yamma laifin ta’annatin da suka yi kan ‘yan Afirka.
A siyasance, mafarkin mulkar kai ya zama gaske, amma ‘yancin tattalin arziki ya zama a mafarki kawai.
Ba a cikin nahiyar Afirka kadai ake gudanar da bikin Ranar Afirka ba. ‘Yan Afirka a kasashen waje ma na bikin agayowar ranar a kasashen da suke.
A Turkiyya, wata kungiya mai zaman kanta ta Kungiyar Abokan Afirka a Turkiyya (TADD), ta shirya taro a istanbul kan lakar da e tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka, ta hada masana suka tattauna kan dangantaka da cigaban Afirka.
“Muna magana game da tarihin Afirka, sabon salon mulkin mallaka da ma komai. Yau, na yanke hukuncin kawo sauyi da yin magana kan fasahar kere-kere, sadarwar zamani da zamanantar da komai a matsayin jigon cigagan nahiyar Afirka,” in ji Mustafa Aminu Tukur, daya daga cikin masu magana a wajen taron Ranar Afirka da aka yi a ranar 24 ga Mayu, yayin tattaunawa da TRt Afrika.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Turkiyya ke kara karfafa alaka da kasashen Afirka a fannoni daban-daban da suka hada da tattalin arziki, tsaro, ilimi da huldar diflomasiyya.
Faroukou Mintoiba ya ce "Kasancewa a nan wani abu ne da ke da matukar kyau saboda a zahiri muna samun dama da kuma tattaunawa kan batutuwan da suka shafi 'yan Afirka a Turkiyya da sauransu, tare da murnar nasararmu da al'adunmu a kusan yanayin Afirka," in ji Faroukou Mintoiba.
Kasashen Afirka da dama na ci gaba da fuskantar kalubalen tsarin kamar basussuka, rashin daidaiton ciniki, da karancin masana'antu.
Dangane da martani, yawan ƙasashe suna neman sabuwar haɗin-gwiwa fiye da ƙawancen Ƙasashen Yamma da aka saba da shi, suna komawa ga ƙawaye masu tasowa kamar Turkiyya da Rasha.
Misali, huldar da Turkiyya ta yi da Afirka ta ci gaba da habaka tun bayan da ta ayyana shekarar 2005 a matsayin "Shekarar Afirka."
Ƙasar ta kara yawan aikin diflomasiyya, inda ta bude ofisoshin jakadanci da dama a fadin nahiyar, kuma a shekarar 2008, an ba ta matsayin mai sa ido a kungiyar Tarayyar Afirka.
Har ila yau, al’ummar nahiyar Afirka na halartar bukukuwan murnar zagayowar Ranar Afirka a kasashen da suka karbi bakuncinsu irin su Turkiyya, inda wata kungiya mai zaman kanta da aka fi sani da Association of All Friends of Africa (TADD) ta shirya wani taro.
Wani muhimmin fanni na Turkiyya shi ne inganta dangantakarta da kasashen Afirka ta hanyar ilimi, inda dubban 'yan Afirka ke karatu a Turkiyya ta hanyar tallafin karatu.
Dalibai na da matukar kima wajen gina sabuwar "Afrika mai karfi" da kuma kara dankon zumunci tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka, in ji Bilgehan Güntekin, shugaban kungiyar duk abokanan Afirkaa hirarsa da TRT Afrika.
Yayin da ake neman wasu abokan hulda a cikin sauya yanayin siyasa, tsaro, da tattalin arziki na duniya, kasashen Afirka sun yi ta kira da a samu karin wakilci a fagen duniya.
Ana ci gaba da yin kiraye-kirayen neman kujeru na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ga kasashen Afirka da kuma ƙarin faɗa-a-ji a cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, da nufin tabbatar da cewa nahiyar na da ra'ayinta kan shawarwarin da suka shafi makomarta.
Yayin da ake bikin Ranar Afirka, ya rage lokacin yin tunani kan gwagwarmayar da aka yi a baya, da tantance kalubalen da ake fuskanta, da kuma jaddada aniyar nahiyar ta tsara makomarta.
Manazarta na fatan bukukuwan da ke kunshe da jawabai masu kayatarwa da al'adu za a yi ƙoƙarin tabbatar da faruwarsu zuwa zahirin gaskiya don Afirka da al’ummarta su amfana ta fuskar bunkasar tattalin arziki, zaman lafiya, da cikakken 'yancin kai.