Rai baƙon duniya! Kuma dukkan mai rai wata rana mamaci ne.
Ranar Talata 1 ga watan Yulin 2025 ne aka yi jana’iza tare da binne hamshaƙi kuma mashurin attajirin nan na Nijeriya, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, bayan da Allah Ya karɓi rayuwarsa ranar Asabar, 28 ga watan Yunin 2025 a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Bango ya faɗi! Rumfa ta rushe!! Su ne kalaman da al’ummar Nijeriya, musamman na jihar Kano, inda nan ne asalin marigayin, suka dinga faɗa bayan sanar da rasuwar tasa.
Aminu Dantata ya kafa tarihi a fannoni da dama. Dan siyasa ne, domin an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai tun a Jamhuriya ta farko. Sannan ya yi aikin gwamnati, domin har mukamin kwamishina ya rike a gwamnatin Kano, sannan a fannin kasuwanci wanda ya gada a nan ne ma ya fi shuhura.
Ga dai wasu abubuwa biyar da tarihi ba zai taɓa mantawa da marigayin da su ba.
Binne shi a Madina duk da ba a can ya rasu ba
Alhaji Aminu Dantata, wanda aka fi sani da Aminu Dogo, ya rasu yana da shekara 94 a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Lawabawa.
Sai dai wani abin ban sha’awa shi ne yadda iyalansa suka yi ƙoƙarin tabbatar da burinsa da ma wasiyyarsa ta son a binne shi – a Makabartar Baki’a inda a nan ne ake binne sahabbai tun zaman Manzon Allah SAW – a birnin Madina (Garin Manzo) na Saudiyya a duk lokacin da ya bar duniya.
A bisa al’ada abin da aka sani shi ne za a binne ka a Madina ne kawai idan a can ka rasu. Amma a tarihin Nijeriya ba a taɓa samun wanda ya rasu a wata ƙasa daban ba sannan a kais hi Madina a binne shi sai a kan Aminu Dantata.
Lallai tarihi ba zai manta da wannan al’amari bai ƙayatarwa ba.
Yawan iyali/zuri’a
Zuri’ar Dantata ta yi shuhura ne tun a zamanin mahifin Aminu Dogo, wato Alhassan Dantata, wanda a lokacinsa aka yi ittifaƙin yana daga cikin mutane ƙalilan da suka fi kowa kudi a Kano.
Ita wannan zuri’a ta Alhassan Dantata ita ta samar da Aminu Dantata, da Sanusi Dantata, wanda shi kuma ya kasance yaya ga Aminun kuma mahaifin Hajiya Mariya sannan kakan mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, wato Aliko Dangote.
Ke nan wannan zuri’a za a daɗe ana jin labari da tarihinta a duniya ba ma Nijeriya ba kadai.
Kazalika, Alhaji Aminu Dantata yana da tarin ‘ya’ya da jikoki da tattaɓa-kunni, waɗanda sun kutsa wurare daban-daban ana damawa da su a duniya. Yawan iyalansa kaɗai abu ne da zai sa tarihi ba zai manta da shi ba.
Yi wa addinin Musulunci hidima
Wani abu da kowa ya yarda cewa Aminu Dantata ya tsaya a kansa tsawon lokaci shi ne yi wa addinin Musulunci hidima ka’in-da-na’in.
Ya gina masallatai, ya gina islamiyoyi, ya gina rijiyoyi, ya ba da zakka, ya yi sadaka, ya girmama malamai, ya, ya, ya..... har ba sa ƙirguwa.
Jim kaɗan bayan da aka sanar da rasuwarsa, an ga yadda malaman addini da ma sauran al’umma suka dinga yabonsa da yi masa addu’o’i da faɗar irin alkhairai da hidimar da ya yi wa addini a tsawon rayuwarsa.
Bashir Hayatu Jantile, wani ɗan jihar Kano mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, wanda kuma ya san Aminu Dantata sosai, ya shaida wa TRT Afrika cewa babu wani attajiri da ya kai Aminu Dantata yi wa addini hidima a Kano
“Ko da ƙarya ka yi da sunan addini ka nemi taimako a wajen Aminu Dantata sai ya ba da taimakon nan,” in ji Bashir Jantile.
Haƙiƙa tarihi ba zai manta da Aminu Dogo ba ko don yawan sadakatul jaariya (sadaka mai gudana) da ya yi a tsawon rayuwarsa.
Arziki na ban mamaki
Duk wanda ya tashi a jihar Kano ba zai yi inkarin ɗumbin arziki da dukiyar da Alhaji Aminu Dantata ya mallaka ba.
Sunansa ya shahara ya karaɗe ko ina a faɗin Nijeriya. Zai yi wahala a ce babu wani gida da ya mallaka a duk unguwannin birnin Kano.
A wata hira da aka taɓa yi da shi a kafar watsa labarai ta Trust TV, da bakinsa ya ce bai san iya dukiyar da ya mallaka ba.
Aminu Dantata yana da kuɗaɗe lakadan, da gidaje da fiyale da kamfanoni da gonaki da hannayen jari da sauran manyan kadarori a ciki da wajen Nijeriya.
A waccar hirar tasa, ya bayyana cewa kusan babu wani babban birni a duniya da ba shi da gida.
Haka kuma da kansa ya bayyana cewa ya fara mallakar jirgin sama na ƙashin kansa tun shekarar 1966.
Ko wannan ɗumbin arzikin kawai ya isa a ce tarihi bai manta da Aminu Dogo ba.
Kyauta da kyautata wa mutane
Wani ƙarin abu da babu mai inkarinsa a tattare da halayyar Aminu Dogo ita ce yawan kyauta da kyautayi da kyautata wa mutane.
Wannan halin kyautar tasa ba a kan iyali da zuri’arsa kawai ta tsaya ba, ma’aikatansa na gida da waje, da maƙwabta da al’ummar gari duk sun shaida yadda ba ya yin ƙasa a gwiwa wajen bai wa mutane kyauta, ko ta kuɗi ko ta abinci ko muhalli da jari da sauransu.
Lallai tarihi ba zai taɓa mantawa da Aminu Dogo ba. Kuma tarihin Kano ba zai kammala cif ba sai an saka Aminu Dantata da zuri’ar gidansu.
Madalla da gamawa da duniya lafiya.