Daga Kudra Maliro
Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da rikici ya addaba ta daga jan kati ga wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya - Arsenal, Bayern Munich da Paris Saint-Germain - saboda daukar nauyin gangamin “Visit Rwanda”.
Babu ruwan wasanni da zubar da jini; amma kuma wasannin masu kyau sun tsinci kawunansu a tsakiyar rikicin jin kai da tawayen ‘yan M23 ya janyo a gabashin Jumhuriyar Kongo, ciki har da garuruwan Goma da Bukavu.
Rikicin ya faro ne daga zargin da gwamnatin Kongo ta yi wa Rwanda na goyon bayan ‘yan tawayen M23, zargin da Kigali ta sha watsi da shi. Rwanda ta yi zargin cewa sojojin Kongo na hada kai da ‘yan ta’addar Hutu da ke da alhakin kisan kiyashin da aka yi wa Tutsi a 1994.
Wadannan batutuwa sun janyo damuwa a fagen kasa da kasa, suna fito da rashin zaman lafiyar yankin da irin tasirin da zai yi.
Daukar nauyin harkokin wasanni da ke kawo miliyoyin daloli ga Gasar Premier ta Ingila, Bundesliga ta Jamus da Lique 1 na Faransa, na daga cikin al’amuran da rikicin ke shafa.
Kira ga Kungiyoyi
Ministar Harkokin Wajen Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Thérèse Kayikwamba Wagner, a baya bayan nan ta yi kira ga Arsenal, Bayern Munich da PSG da su sake duba yarjeniyoyinsu da Hukumar Cigaban Rwanda.
Taken “Visit Rwanda” na bayyana rigunan ‘yan kwallon Arsenal tun 2018. PSG da Bayern Munich ma sun bi sahu a shekarun da suka biyo baya. A yayin da aka yi wa Arsenal alkawarin dala miliyan 40 a shekaru uku, gangamin ya ce zai baiwa PSG dala miliyan 8 zuwa 10.
Bayern ta sanya hannu na shekaru biyar da Rwanda a 2023 don tallatawa da habaka kwallon kafa da yawon bude ido.
Shirin da aka fara cikin murna don habaka yawon bude ido a Afirka ta hanyar shaharar kwallon kafa a duniya baki daya, a yanzu ya zama rikici.
Kalubalantar hadin kan Rwanda da manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya da Jumhuriyar Kongo ke yi ba iya kan kwallon kafa ya tsaya ba.
Jami’an gwamnatin Kongo sun roki shugaban Formula One Stefano Domenicali, suna mai mika mas abukatar sake duba batun Kigali ta dauki nauyin gasar Grand Prix, suna masu zargin sojojin Rwanda da da kai hare-haren da suka tsugunar da sama da mutane 700,000 tun farkon wanna shekarar saboda rikicin M23.
Ma’aikatar Lafiya ta Kongo ta bayar da rahoton cewa kusan jikunan mutane 3,000 na nan a mutuware a Goma sakamakon rikicin baya bayan nan da M23 suka tayar.
Matsayin Rwanda
Mai magana da yawun gwamnatin Rwanda Yolande Makolo ta alakanta lalacewar lamarin tsaron ga rashin bin doka da oda a Kongo da gwamnatin kasar ta yi sakaci aka samu ta hanyar kin magance matsalolin ‘yan kasarta.
“Mutane ne da suka cutu daga rikicin kabilanci da ‘yan ta’addar FDLR ‘yan kabilar Hutu ke yi. FDLR wata kungiya ce mai daukar makamai da Amurka ta ayyana a matsayin kungiyar ta’adda,” Makolo ta fada wa TRT Afrika.
Wadanda suka aikata mummunar aika-aikar kisan kiyashi a a1994 ne suka samar da kungiyar don yakar Tutsi kuma ta yi alkawarin dawo wa Rwanda don ‘kammala aikin’ da ba ta iya kammalawa ba a 1994. Rwanda ba za ta taba bayar da wannan abu ya faru ba,” in ji ta.
Makolo ta kuma ce idan gwamnatin Kongo da gaske take game da zaman lafiyar al’ummarta da kwanciyar hankalin yankin, to za ta rusa kungiyar FDLR, sai ta kare jama’arta tare da kawar da barazanar da ake yi wa Rwanda.
A nata martanin, Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta zargi rwanda da amfani da M23 wajen satar albarkatun kasa a yankunan Kongo.
“Dakarun sojin Rwanda na RDF sun yi biris da yarjejeniyar tsagaita wuta da muka cimma da tawakara na Rwanda inda suka jefa bama-bamai kan asibitoci a Goma, wanda ya janyo mutuwar kimanin mutane 3,000, kamar yadda MDD ta bayyana,” in ji ministar harkokin waje Wagner a wasikar da ta aika zuwa ga Formula One.
Shugaban Kasar rwanda Paul Kagame ya sanar a watan DIsamban bara cewa kasarsa za ta shiga takarar neman karbar bakuncin gasar Formula One a babban birnin Kigali.
Rikicin kudade
A wajen Kagame, karbar bakuncin Formula One “daya daga cikin dabarun da kasar za ta yi amfani da su ne don karfafa tattalin arzikinta, yawon bude ido da shahara a duniya.”
Rwanda da aka sani a matsayin Kasa Mai Dubunnan Tsaunuka, na da burin zama kasar Afirka ta farko da ta karbi bakuncin gasar tseren motoci ta Formula One Grand Prix a nahiyar tun bayan 1993. Wasikar da Kongo ta aike na tuhumar inda Rwanda ta samu kudaden daukar nauyin karbar bakuncin Grand Prix.
“Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta yi amanna cewa satar wadannan albarkatun kasa da Rwanda ke yi na ba ta dala biliyan daya duk shekara,” in ji rahoton MDD.
Makolo ta jaddada cewa kawancen wasanni na Rwanda da tallan “Visit Rwanda” na sanya farin ciki ga miliyoyin mutane, baya ga samar da ayyukan yi, jan hankalin karin ‘yan yawon bude ido da samar da kudade.
Ta fada wa TRT Afrika cewa “Lokaci ya yi da jama’ar Kongo za su damar amfana da wannan, amma wannan ba zai tabbata ba matukar Jumhuriyar Kongo ba ta daina zuba jari a ayyukan azabtar da ‘ya’yanta ba da kuma kaiwa Rwanda hare-hare, maimakon a ce ta mayar da hankali wajen samar da kayan more rayuwa da cigaban jama’a a kasar.”
“Wadannan zaege-zarge kokari ne kawai na kawar da hankula daga wadanda suke daukar nauyin wadannan rikice-rikice.”