Fafutukar da Afirka ke yi don raba matasa da shan shisha mai ɗanɗano da ƙamshi mai daɗi
AFIRKA
5 minti karatu
Fafutukar da Afirka ke yi don raba matasa da shan shisha mai ɗanɗano da ƙamshi mai daɗiAfirka na gwagwarmaya da fafutukar yaki da kayan taba sigari masu dandano mai dadi da suke sanya jarrabar son su a tsakanin matasa da sunan wai ba sa cutarwa.
Shisha / Reuters
12 Yuni 2025

Daga Pauline Odhiambo

Hannayen Adeola sun sake kadawa. Ba wai saboda tsoro ko rawar dari ba, sai dai saboda nuna kaunar wani abu da a yanzu ke juya rayuwarta.7

Mika wuya ga wannan bukata tata na nufin za ta kashe kudin abincinta don sayen kwalin taba maimakon abinci. Abu mafi muni ma shi ne ta san cewar saukin da za ta samu na wani dan lokaci ne.

‘Yar Nijeriya din mai shekaru 17 ba ta shirya wa rayuwarta fama da wannan matsalar ba a lokacin da a karon farko ta sha wata taba sigari mai dandanon kayan marmari na strawberry.

“Dandanon kamar na alawar Candy” ta fada wa TRT Afrika. “Kawayena sun ce ba wai shan taba ne na gaske ba…Ban taba tunanin

Tambayar da ke fuskantar wasu matasan Afirka ba wai ko ta yaya za su kalubalanci sinadarin tabar ba - sai dai neman amsar tambayar har zuwa wane lokaci za a duaktrawaberry din ba daina aii ba.

A Kenya, Jamal mai shekaru 16 na fama da jarabar son shan taba mai dandano d akamshi, kamar dai Adeola.

Ya fara da shan shisha mai dandanon na’a na’a tun yana dan shekara 14, dandano da kamshin ne ya ja hankalinsa sannan ya amince da cewa ba su da illa kamar taba sigari.

“Da fari, na dan fara sha ne don wasa. Sai ya zamana na kasa daina wa,” in ji yaron dan Nairobi. “Zan samu ciwon kai da rashin lafiya idan ban sha ba.”

Amma Jamal ya yi gwagwarmaya. Tare da taimako daga matasan yankinsa da ke yaki da shan taba da dangoginta, ya rabu da sha bayan kalubalantar kansa na tswon watanni shida.

“Rabuwa da shan shisha ne abu mafi waha;la a rayuwata da na taba yi,” ya fada wa TRT Afrika. “A yanzu, ina gargadar abokaina: wadannan abubuwa masu dandano da kamshi mai dadi tarko ne.”

Girmamar annobar

Ranar Yaki da Shan Taba ta Duniya ta 2025, da aka yi taruka a ranar 31 ga Mayu, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kiran gaggawa ga gwamnatoci a fadin duniya do su hana shan taba mai kamshi da dandano wato shisha, don kare matasa data illatuwa daga matsalar da ke girmama.

“Wadannan dandano na kawo jarabar kaunar su don haka dole a hana amfani da su,” in ji daraktan WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus. “Suna zagon kasa ga ayyukan shekaru da aka yi na yaki da shan taba sigari.”

Sama da kasashen duniya 50 sun hana shan taba mai kamshi da dandano, inda sama da kasashe 40 kuma suna hana sayar da taba mai aiki da lantarki.

Amma kayan taba irin su kwayoyin kafsol da ruwan digawa mai kamshi da dandano na yawo a kasuwanni saki ba kaidi.

Wasu kasashen Afirka na kawo sauye-sauye. Afirka ta Kudu, Mauritius da Ethipia sun saka dokoki kan taba mai aiki da lantarki da masu kamshi da dandano, inda Kenya kuma ke duba yiwuwar daukar tsauraran matakai bayan samun labaran yara ‘yan makaranta na amfani da su.

Sai dai kuma, aiwatar da dokokin ne kalubale, a yayin da masana’antun tabar ke amfani da masu mabiya da yawa a kafafen sadarwa na zamani, kunshe tabar a kyakkyawan yanayi da kawo dandano daban-daban don jan hankali matasa.

Rudiger Krech, daraktan cigaban lafiya na WHO, ba ta raba alakar yadda ake kunshe tabar da dabarun talla ba.

“Muna kallon yadda al’uma ke zama jarababbu wajen kaunar tabar da aka yi da dandano da kamashi na musamman,” in ji ta.

“Wannan ba kirkirarren abu ba ne mai kyau, wayo ne da daba da dole ne mu dakatar da shi.”

Tarkon kamshi da dandano

Kwararrun kula da lafiya na kara bayyana damuwar WHO game da yadda ake bayyana taba masu kamshi da dandano na musamman irin sjiha da cewa suna da bambanci da taba sigari da aka sani.

Dr Asha Mohamed, kwararriya a bangaren lafiyar huhu da numfashi da ke Nairobi, ta yi gargadi da jan hankali kan karuwar adadin mutanen da ke fama da cututtukan da shan irin wadannan taba na shiha suka janyo.

Ta fada wa TRT Afrika cewa “Marasa lafiya matasa na zuwa da mummunan ciwon huhu, ba tare da sun fahimci cewa wadannan ‘kayan jin dadin masu kamshi da dandano na zuba cututtuka a jikkunansu.”

Kiran da WHO ke yi a yanzu na bukatar gaggawa. Duk da gwamnatoci da masu fafutuka na kalubalantar dabarun kamfanoni, mutuwar mutane miliyan takwas a kowace shekara saboda shan taba na bayar da alamun yakin na da nesa da samun nasara.

A wajen Adeola da Jamal, yakin na kai da kai ne. Sun fuskanci hatsarin jarabtuwa da shan taba da dangoginta tare da kubuta sabida aniyarsu ta rabuwa da dabi’ar.

Bayan watanni na gwagwarmaya, Adeola ta daina shan shiha. Ta na jin tsoro ga kawayenta da suka kasa daina sha.

"Ba su san hatsarin da wadannan kayan tabar masu kamshi da dandano ke da shi ba,” in ji ta.

Jamal ma ya nuna tirjiya. “Kar ku bari a yaudare ku da da dandanonm” in ji shi. “Dandanon na da dadi, amma jarabar son su na da muni,” ya fada wa TRT Afrika.

* An sauya wasu sunayen don boye su waye mutanen

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us