A ina manyan sansanonin sojin Amurka suke a Gabas ta Tsakiya?
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
A ina manyan sansanonin sojin Amurka suke a Gabas ta Tsakiya?Dakarun Amurka sun kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran, inda suka fuskanci barazana daga Tehran kan ɗaukar fansa, kuma akwai yiwuwar cibiyoyin Amurka a yankin su iya zama wuraren ɗaukar fansar. Ga dai manyan cibiyoyin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta aika da jirgin ruwa mai daukar jiragen sama don bayar da kariya ga ma'aikatanta da ke Gabas ta Tskaiya. / Reuters
23 Yuni 2025

Bahrain

Ƙasar na da hedikwatar jirgin ruwan yakin Amurka na biyar mafi girma, wanda ke ayyuka a tekun Gulf, da Bahar Maliya da tekun Arab Sea da ma wani ɓangare na Tekun Indiya.

Qatar

Sansanin Sojin Sama na Al Udeid da ke da girman kadada 24, na cikin sahara a wajen birnin Doha, kuma nan ne hedikwatar Cibiyar Bayar da Umarnin Sojin Saman Amurka a yankin, wadda ke kula da ayyuka da dama tun daga Masar a ɓangaren yamma har zuwa Kazakhstan a ɓangaren gabas.

Shi ne sansanin sojon Amurka mafi girma a Gabas ta Tsakiya wanda ke ɗauke da dakaru kimanin 10,000.

Kuwait

Akwai cibiyoyin soji da dama da suka haɗa da Arifjan, da Ali Al Salem, da ke da nisna kilomita 40 da iyakar Iraƙi da aka sani da “The Rock” (Babban Dutse” saboda duwatsu da yake da su da suka kebanta da shi.

An kafa sansanin Buehring a 2003 a lokacin yaƙin Iraƙi kuma matattarar sojin Amurka ce inda daga nan ake aika dakaru zuwa Iraki da Syria, kamar yadda shafin intanet na rundunar sojin ya bayyana.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Sansanin Sojin Sama na Al Dhafra, na nan a kudancin babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Abu Dhabi kuma sojojin saman kasar ma na amfani da shi, ya kasnace mai muhimmanci da ya bayar da taimako wajen yaƙi da ƙungiyar Daesh, da ma kai dakaru zuwa yankin, kamar yadda Rundunar Sojin Sama ta Amurka ta bayyana.

Tashar Jiragen Ruwa ta Jabal Ali da ke Dubai, duk da ba sansanin soji ba ne, amma nan ne tashar jiragen ruwa mafi girma da sojojin Amurka ke amfan da ita a Gabas ta Tsakiya da take yawan karɓar baƙuncin jiragen saman yaƙi na Amurka da sauran jiragen ruwa.

Iraki

Amurka ta ci gaba da wanzuwa a Sansanin Sojin Sama na Ain Al Asad da ke yammacin lardin Anbar, yana taimaka wa sojojin Iraƙi da bayar d agudunmawa ga ayyukan NATO, kamar yadda Fadar White House ta bayyana.

A shekarar 2020 makamai masu linzami na Iran sun kai hari kan sansanin, don ramuwar gayya kan kisan Janaral Qasem Soleimani.

Sansanin da ke yankin Kurdawa mai cin gashin kansa a yankin Erbil na arewacin Iraki, Sansanin Sojin Sama na Erbil ya zama wajen aikin sojojin Amurka da kawayenta wajen gudanar da atisaye da shirin yaki.

Sansanin na taimaka wa ƙoƙarin samar da tsaro a wuraren bayar da horon, da musayar bayanan sirri, da kai kayan aiki a arewacin Iraƙi, kamar yadda rahoon Majalisar dokokin Amurka ya bayyana.

Saudiyya

Sojojin Amurka a Saudiyya - da yawan su ya kai 2,321 a 2024, kamar yadda White House ta bayyana - yana aiki tare da gwamnatin Saudiyya, na samar da tsaro ta sama da makamai masu linzami tare da agazawa ayyukan jiragen yaƙin Amurka.

An jibge wasu a nisan kilomita 60 kudu da babban birnin Riyadh, a Sansanin Sojin Sama na Yarima Sultan, wanda ke taimaka wa sojojin Amurka ta sama wajen samar da tsaro inda ake da garkuwar Patriot da tsarin tsaro na THAAD.

Jordan

Yana nan a Azraq, kilomita 100 arewa maso-gabashin babban birnin ƙasar Amman, Sansanin Sojan Sama na Muwaffaq al Salti na ɗauke da Rundunar Sojin Amurka ta 332, wadda ke ayyuka a yankin Levant, kamar yadda wani rahoto na Dakin Karatun Majalisar Dokokin Amurka ya bayyana.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us