Kwanan baya Isra'ila ta sanar da cewa za ta gina babbar hanyar ƙarƙashin ƙasa da za ta zama hanya ɗaya tilo da za ta haɗa Falasɗinawa miliyan 1.5 da ke kudancin Gaɓar Yamma da aka mamaye da yankin arewaci.
Aikin wani ɓangare ne na shirin faɗaɗa muhalli, mai suna "Fabric of Life", wanda zai haɓaka tsarin zirga zirga a cikin Gaɓar Yamma, amma tabbas ba don walwalar Falasɗinawa ba.
An shirya tsara hanyar ce yadda za ta kewaya gabashin wajen garin Birnin Ƙudus da aka mamaye ta cikin Hamadar Judean, a tilasta wa ababen hawan Falasɗinawa daga Bethlehem da Hebron su kasance ƙarƙashin ikon har zuwa Jericho a hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Jordan valley.
Za a kawar da shi ma wajen binciken ababen hawa na Az-zaim, a zamar da hanyar Road-1 hanyar Isra'ila kawai, yayin da kuma za a hana Falasɗinawa amfani da hanyar da ke tudun ɗungurungun.
"Wannan aikin gina hanyar ƙarƙashin ƙasar, wacce aka tallata ƙarƙashin suna na yaudara, yana ɗaya daga cikin shirye shiryen Isra'ila mafi haɗari," a cewar wani ɗan rajin kare haƙƙin siyasa na Falasɗinawa daga Eizariya, a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, wanda za a dinga kira Khaled a ɗaukacin wannan rubutun domin ɓoye ko shi wane ne.
Hanyar E-1(East -1) mai faɗin 12-square-kilometer zai matuƙar faɗaɗa iyakokin Birnin Ƙudus. Hanyar mai nisan km 35 bisa km 25 za ta ratsa faɗin West Bank, ana danƙa iko da ita a hannun Isra'ila.
A faɗar Khaled, wanda ya san yankin gaba da bayansa, aikin na laƙume dubban dunums (1,000 square metres) na fili daga garuruwa da ƙauyukan Al-Eizariya, Abu Dis, Al-Sawahra, da kuma Az-zaim.
"Gagarumin ƙwace fili ne. Hanyar ta ratsa Jabal Al-Baba tare kuma da katangar da ta raba har zuwa Az-zaim, sannan yana da hadafin tsaurara faɗaɗa matsugunan ƴan kama guri da kuma korar Falasɗinawa da ke zaune a can.
Duk da dala miliyan 90 da aikin gina hanyar zai lashe, amma ba da kuɗin masu biyan haraji na Isra'ila za a aiwatar da shi ba, a maimakon haka, za a samar da kuɗaɗen ne daga wata gidauniya maƙare da kuɗaɗen da aka samu daga kuɗaɗen shiga na hukumar kwastom, halastaccen kuɗin Falasɗinawa, wanda Isra'ila ke karɓa a madadin hukumar Falasɗinawa, amma a kodayaushe take hana su ko ta karkata akalarsu.
Yayin da kafofin watsa labarai na Isra'ila suka laƙaba wa shirin suna shirin bunƙasa sufuri, an tsara aikin gina hanyar ƙarƙashin ƙasar ne domin karfafa iko da Isra'ila ke da shi a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye ta hanyar taƙaita zirga-zirgar Falasɗinawa kacokan, wata majiya da ke da masaniya ta tabbatar da hakan.
"Yayin ƴan mamayar suka fara tsaurara shiga Al-Eizariya a baya bayan nan, iyalan Birnin Ƙudus da dama dole suka bar wajen. Wani mutum da na sani ya sheda mini cewa yana zuwa aiki a makare yanzu saboda da tsauraran matakan. Ƴan mamayar ba sa son mazauna Birnin Ƙudus su zauna.
Hadafin shi ne a kore mu kwatakwata daga Birnin Ƙudus," ya ƙara da cewa.
Har ila yau, Khaled ya yi nuni da cewa ƙaura daga Falasɗinu na ƙaruwa a kai a kai, abin da ya yi imani shiryayye ne.
A ra'ayinsa, ƙaruwar aikace aikacen haramtattun matsugunai da kuma ƙaruwar ɗaukar tsauraran matakan dukkansu wani ɓangare ne na wata kitsatstsiyar dabara ta matsa wa Falasɗinawa lamba su kama gabansu.
"A yanzu, ƴan kama wuri zauna na tafka ta'asa a kudancin West Bank da aka mamaye kuma sannu a hankali suna tunkarar Ramallah. Abin takaici, mutane ƙalilan ne suka lura cewa wannan kansa ce, mummunar ma kuwa."
Zuwa farkon shekarar 2025, OCHA ta gano abubuwa da ke yi wa zirga zirga tarnaƙi guda 849 a faɗin Gaɓar Yamma, da suka haɗa da Gabashin Birnin Ƙudus da Hebron, abin da ya taƙaita motsin Falasɗinawa miliyan 3.3.
Tare da shingaye masu nisan kilomita 712-km, waɗannan tsauraran matakan suna kassara ƴancin zirga zirga matuƙa, hana samun muhimman buƙatu, da kuma ta'azzara rarrabuwa ta zamantakewa da yankuna.
Ƙarin karɓe iko da "Ɗaukacin Birnin Ƙudus"
Gina hanyar ƙarƙashin ƙasar maganar gaskiya wani ɓangare ne na wani babban shirin Isra'ila na karɓe iko da "Ɗaukacin Birnin Ƙudus", wani muhimmin buri na haɗewa da Gabashin Birnin Ƙudus, wanda Isra'ila ta yi gaban kanta ta karɓe iko da shi a 1981, ya zama matsugunin Isra'ila da yake faɗaɗa zuwa gabashi, har zuwa Jordan valley.
Shirin da aka fara kitsa shi a ƙarƙashin mulkin firaministan Ariel Sharon a farko farkon shekarun 2000, shirin na buƙatar karɓe iko na har abada da yanki mafi girma na West Bank da aka mamaye ya zama abin da Isra'ila ta ɗauka a matsayin yankin babban birninta.
Muhimmin abu a wannan dabara shi ne mashigar E-1, yanki mai faɗin ƙasa 12-square-kilometer da ya kasance ginshiƙin shirin faɗaɗa zuwa Jordan valley ba bisa ƙa'ida ba.
"Mashigar Fabric of Life" ta ratsa wannan shiyyar, ta shata zirin da Isra'ila ke iko da shi daga Yamma zuwa Gabas da kuma yankunan Falasɗinawa a wurare daban daban.
Da ma akwai shirin kwatankwacin wannan da ke wanzuwa a “Sovereignty Road,” da ya haɗa da kewaye na ƙarƙashin ƙasa ƙarƙashin shirin Road-1 na Isra'ila.
Hakan na sauya akalar hanyoyin tafiye tafiyen Falasɗinawa, abin da ke ƙara ta'azzara nuna wariya. Idan aka haɗa waɗannan waje guda, ayyukan guda biyun ba su ba Falasɗinawa ƴancin zirga zirga ba a ciki da kewayen Gabashin Birnin Ƙudus.
"Bayan aikin na hanyar ƙarƙashin ƙasar, za a ƙwace dubban dunums daga Abu Dis, Al Sawahra, da Al-Zaim, suna raba mutane da filayensu da ƴancinsu," Khaled ya ce.
"Game da zirga zirga, idan ina son zuwa Ramallah yanzu,yana ɗaukar kimanin mintuna 30. Bayan an kammala wannan hanyar ƙarƙashin ƙasar, nisa tafiyar zai kwashe kimanin sa'o'i biyu idan aka bi ta Jericho. Zai zama jidali."
Kisan kiyashi da sunan Karɓe iko
Gaggauta waɗannan ayyukan karɓe ikon suna zuwa ne yayin da Isra'ila ke kaddamar da kisan kiyashi a Gaza, wanda ya halaka fiye da mutane dubu 58'000, duk da shirin gina hanyar ƙarƙashin ƙasar ya gabaci kisan ƙare dangin na yanzu.
A shekarar 2021, Isra'ila ta ware kimanin dala Miliyan $4.6 domin soma sashen farko na hanyar "Fabric of Life".
Sashen farkon ya mayar da hankali ne kan ware garuruwan Al-Eizariya da Abu Dis da suke gabashin Birnin Ƙudus.
A tarihince a haɗe suke da Birnin Ƙudus kansa, an kafa wa waɗannan birane ƙahon zuƙa ne domin a ware su saboda Isra'ila na da hadafin shafe duk wata nasaba da Falasɗinawa ke da ita a yankin.
Yanzu suna tsakanin ƴanci da kuma hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Fabric of Life; abubuwan da ke gaba gaba wajen rarraba yanki.
Sauya yankin ya kankama ne gwamman shekaru da suka shuɗe tare da gina Maale Adumim a ƙarshe ƙarshen shekarun 1970, yanzu ɗaya daga cikin matsugunan Yahudawa mafi girma da jawo ce-ce-ku-ce a yankin West Bank da aka mamaye.
An gina shi ba bisa ƙa'ida ba a kan filayen Falasɗinawa da aka ƙwace a gabashin Birnin Ƙudus, Maale Adumim na zaune a tsakiyar mashigar E-1 kuma yana taka muhimmiyar rawa dabarun faɗaɗa na Isra'ila.
Dawo da shi wajen yana barazanar yakice gabashin Birnin Ƙudus daga sauran yankunan West Bank, abin da ke kawo tarnaƙi ga yiwuwar Kafa ƙasar Falasɗinu.
Yanzu matsuguni ne ga Yahudawa ƴan kama wuri zauna fiye da dubu 400,000 kuma an tsara shi a matsayin birni ƙarƙashin dokokin Isra'ila a hukumance, duk da suka daga ƙasashen duniya.
A ƙarƙashin shirin "Fabric of Life,," cire wurin binciken ababan hawa na Az-Zaim zai tabbatar da zirga-zirgar Yahudawa ƴan kama wuri zauna a ciki da kewayen Maale Adumim ba tare da cikas ba.
Wuraren binciken ababan hawa da rufe hanyoyi a faɗin Gaɓar Yamma da aka mamaye sun zama wuraren take haƙƙi da suka yi ƙaurin suna, inda ake samun rahoton cin zarafi, tsarewa barkatai da ma mace mace akai akai, tun da kisan ƙare dangin Isra'ila ya kankama.
A cewar Khaled, tarin tsauraran matakan yau da kullum da ƴan mamaya suka ƙaƙaba da suka haɗa da wuraren binciken ababan hawa, toshe hanyoyi sun jefa rayuwar mutane cikin mawuyacin hali sosai, musamman a ɓangarorin ilimi da kiwon lafiya.
"A halin da ake ciki a Al-Eizariya da Abu Dis da kuma Al-Sawahra, inda sune hanyoyin gabashi na shiga babban birnin da aka mamaye, zirga zirga ta zamo jidali sosai bayan Isra'ila ta fara yi wa Falasɗinawa kisan kiyashi."
“Ƴan mamayar na rufe Wuraren binciken ababan hawa a kodayaushe, kuma ya fi shafar yaran makaranta.
Na ga yaran makaranta suna juyawa suna komawa gida saboda motocin safa ba za su iya shiga gari ba bayan an kulle duka hanyoyin," Khaled ya bayyana.
"Ko da motocin safa da suka nufi Birnin Ƙudus ba za su iya shiga Al-Eizariya ba yanzu saboda ƴan mamaya sun kulle mashigar ɗaya tilo. Saboda haka dalibai sai dai su koma gida, kuma muna asarar al'ummar wani zamani sukutum da ke ƙoƙarin samun ilimi."
Abin takaici, wahalar da Falasɗinawa ke jurewa ba ta taƙaita ga ilimi ba kaɗai.
Waɗanda ke kan babbar hanya da ta haɗa arewaci da kudancin yankunan Gaɓar Yamma.
Wuraren binciken ababan hawa na sunduƙin karfe sun zama wuraren take haƙƙi da suka yi ƙaurin suna, inda ake samun rahoton cin zarafi, tsarewa barkatai da ma mace mace akai akai, tun da kisan ƙare dangin Isra'ila ya kankama.
"Ni da kaina na san wata ɗalibar Jami'ar Birzeit wacce sojoji maza suka lakaɗawa duka kuma suka yi jifa da ita gefe.
Da na tattauna da ita,ta sheda mani cewa hatta matasa maza da ke kusa ba su isa su kawo ɗauki ba, saboda kowa ya sani cewa idan ka fita daga wajen binciken ababan hawa, babu makawa za a harbe ka."
Abin da wataƙila ya yi kama da mugun mafarki, ya zamo abin da Khaled ya bayyana da cewa, mummunan abin da ke faruwa kullum.
"Mutane da dama sun rasa rayukansu, har ma da mahaifiyata," ba bayyana, muryarsa na rawa yayin da yake bayyana yadda ta rasu a wani wajen binciken ababan hawa bayan ta kasa isa asibiti."