Sabuwar dokar lantarki a Nijeriya: Jihohi 7 sun karɓe ragamar gudanarwa
NIJERIYA
3 minti karatu
Sabuwar dokar lantarki a Nijeriya: Jihohi 7 sun karɓe ragamar gudanarwaMatsalar rashin wadatar wutar lantarki a Nijeriya ta kama hanyar gushewa sakamakon sabuwar doka a kasar mai suna “Electricity Act 2023”, wadda ta bai wa jihohin kasar damar tafiyar da harkokin samar da wutar lantarki a jihohinsu.
/ Others
30 Yuni 2025

Ga dukkan alamu, haske na dab da bayyana ga ’yan Nijeriya masu fatan ganin karshen matsalar wutar lantarki a yankunansu.

A tarihin kasar, gwamnatoci da dama da aka yi a baya sun sha yin alkawarin ganin bayan wannan matsala, amma kuma sai abin ya ci tura.

Amma bayan yin sabuwar dokar harkokin lantarki a kasar mai suna “Electricity Act 2023”, jihohi sun fara karbar iko kacokan da harkokin sayar da wutar lantarki a jihohinsu.

A yanzu hukumar da ke kula da harkokin wutar lantarki a Nijeriya (NERC), wadda ke karkashin ikon gwamnatin tarayya ta ce tuni jihohi bakwai sun fara bin abin da dokar ta tanada.

Jihohin su ne, Enugu, da Ondo, da Ekiti, da Imo, da Oyo, da Edo, da kuma jihar Kogi.

Sannan hukumar ta NERC ta ce ana sa ran jihohin Legas da Ogun da Neja da kuma Filato za su kammala karbar ikon tafiyar da harkokin wutar lantarkin jihohinsu daga watan Yuni zuwa Satumban bana.

Sannan akwai Jihar Anambra wadda majalisar jihar ta yi sabuwar doka kan wutar lantarki, kuma ita ma tana kan hanyar karbar ragamar tafiyar da harkokin wutar jihar daga gwamnatin tarayya.

Tanadin doka

Kafin samar da sabuwar dokar wutar lantarkin a shekarar 2023, hukumar NERC ce kadai dokar kasar ta bai wa ikon sanya ido a duka harkokin wutar lantarki a kasar.

Wannan ya hada da samar da wutar, da dakon ta, da rarraba ta, da ma sauran abubuwa da suka shafi gudanar da harkokin lantarki.

Yanzu sabuwar dokar ta bai wa jihohi damar sanya ido da kula da harkokin wutar lantarki da ke jihohinsu, kuma hakan ya ba su damar samar da wutar da kansu, da yin dakonta da kuma rarraba ta.

Sannan za su iya ba da lasisi ga kamfanonin lantarki a jihohinsu.

Wannan sabon tsarin ya tanadi cewa jihohi za su rika tafiyar da harkokin wutar lantarkinsu da kansu, duk da hukumar za ta ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a jihohin.

Masana da dama sun yaba wa wannan sabon tsari musamman ganin cewa tsarin zai bai wa masu zuba jari daga ketare damar kafa kamfanonin lantarki a kasar.

Masana harkar makamashi na ganin wannan tsari zai iya silar magance matsalar wutar lantarki da kasar ta dade tana fama da ita.

Masu zuba jari

Kafin sabuwar dokar lantarkin, gwamnatin tarayyar kasar ce kadai take iya dakon lantarki cikin kasar ta hannun kamfaninta na Transmission Company of Nigeria (TCN).

Duk da cewa da ma an fara bai wa ’yan kasuwa damar kafa kamfanonin samarwa da rarraba wutar lantarki a kasar.

A zahiri, sabuwar dokar lantarkin na nufin yanzu gwamnatin kasar ta ci gaba da tsame hannunta daga harkokin wutar lantarki a kasar.

Ko da yake akwai wasu masana da suke ganin akwai jihohi da dama da ba za su iya sauke wannan nauyin ba/

Irin wadannan jihohin za su iya fuskantar kalubale da dama musamman a matakin farko na fara amfani da tsarin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us