Ranar Yara ta Duniya a Nijeriya: Me take nufi, kuma ta yaya take taimakon yaran?
NIJERIYA
3 minti karatu
Ranar Yara ta Duniya a Nijeriya: Me take nufi, kuma ta yaya take taimakon yaran?A wannan rana ana duba wasu daga cikin manyan kalubalen da yara suke fuskanta, inda ake yin tarukan tattaunawa da masana da malamai da iyaye don lalubo hanyoyin da za su inganta rayuwar yaran, kamar yadda masu magana ke musu kira da manyan gobe.
Yara a Nijeriya / African Leadership
27 Mayu 2025

Ranar 27 ga watan Mayun kowace shekara rana ce da aka ware a Nijeriya don martaba yara da kuma kare hakkokinsu.

Sannan a wannan rana ana duba wasu daga cikin manyan kalubalen da yara suke fuskanta, inda ake yin tarukan tattaunawa da masana da malamai da iyaye don lalubo hanyoyin da za su inganta rayuwar yaran, kamar yadda masu magana ke musu kira da manyan gobe.

Kazalika masana da dama suna jan kunnen iyaye da malamai da shugabanni kan muhimmanci martaba yara da kuma kare hakkinsu saboda yadda hakan ke tasiri a rayuwar yaran lokacin da suke kanana da kuma bayan sun girma.

Albarkacin wannan rana mun duba wasu hanyoyin da yaro zai ci moriyar yarintarsa, wacce ita ce take samar masa da kyakkyawar makoma bayan ya zama babba.

Dokta Hauwa Babura wata kwararriya ce kan harkar ilimi da walwalar kwakwalwar yara kanana ta shaida wa TRT Afrika Hausa cewa abin farko da ya kamata iyaye da malamai da shugabanni su mayar da hankali a kai shi ne, samar da yanayi da zai taimaki kwakwalwar yara, wato yanayi na zaman lafiya da natsuwa da kuma annashuwa.

Dokta Hauwa ta ce idan har babu wannan yanayi, to duk ilimin da aka bai wa yaro da duk abin da za a koya masa, ba zai yi masa tasiri ba.

Ta ce abin farko da ya fi komai muhimmanci a wajen yaro shi ne ya samu kulawa ta musamman kuma bayan samun wannan ne ilimi yake saurin shiga kwakwalwar yaro kuma ya yi masa kyakkyawan tasiri a rayuwarsa.

Sannan masaniyar ta jaddada muhimmancin wasa a rayuwar yara da kuma yadda hakan yake taimaka wa ƙwaƙwalwarsu wajen ƙara kaifi da haɓaka.

Dokta Hauwa, wacce aka fi sani da Kaka, ta shawarci iyaye da malamai da su riƙa bai wa yara damar yin wasanni maimaikon yawan zama wuri daya don kallon shirye-shiryen talabijin, ko kuma yawan amfani da wayar salula.

Ta ce kasashen da suka ci gaba a duniya sun yi bincike mai zurfi, kuma sun gano cewa yawan amfani da wayar salalu da yawan kallon talabijin da wasu yara suke yi, yana dakushe kwakwalwarsu.

Sakamakon haka a yanzu manyan kasashen sun fito da hanyoyin da za su tilasta wa yara kanana rage amfani da waya da sauran abubuwa da ake kallo kamar talabijin.

Masaniyar ta ce muma a kasashen Afrika ya kamata iyaye da hukumomi su fara daukar wadannan matakai na rage ba yara kanana wayar salula saboda yaran su ci moriyar yarintarsu wacce za ta samar musu da makoma mai kyau bayan sun girma.

Sannan wasu masanan na cewa yana da kyau a fara nusar da yara muhimmancin aiki tuƙuru, da kwazo da juriya da son ci gaban al’umma da kuma dogaro da kai, domin hakan zai taimaka musu su zama jajirtattu nan gaba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us