Jerin taurarin ƙwallon ƙafa na duniya masu goyon bayan Falasɗinawa
WASANNI
3 minti karatu
Jerin taurarin ƙwallon ƙafa na duniya masu goyon bayan FalasɗinawaA baya-bayan nan a fagen ƙwallon ƙafa ba Guardiola ne  ya fara nuna rashin jin daɗinsa kan abin da ke faruwa a Gaza ba.
FILE PHOTO: Interview with Manchester City manager Pep Guardiola / Reuters
11 Yuni 2025

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya shiga jerin sanannun mutane a duniya da suka nuna ɓacin ransu a fili dangane da kashe-kashen da ke faruwa a Gaza.

Shahararren kocin, wanda ya taɓa lashe Kofin Premier League sau 6 da Kofin Champions League sau 3, ya ce hotunan da suke fitowa daga Gaza da Sudan da kuma Ukraine suna tayar masa da hankali matuƙa, sannan ya ce abin yana ba shi tsoro ainun.

Guardiola, wanda ya bayyana haka lokacin da aka ba shi digirin girmamawa a Jami’ar Manchester a farkon makon nan, ya ce yana jin ɓacin rai sosai duk lokacin da ya ga hotunan yaran da ake kashewa a Gaza.

Kocin ya ce ya kamata duniya ta yi magana kan wannan batu, maimakon ci gaba da yin shiru kan rashin adalcin da ake aikatawa a Gaza.

Ya ce watakila a zukatanmu muna cewa ai ba ’ya’yanmu ake kashewa a Gaza ba, sai dai kocin ya shawarci mutane da su sake tunani saboda nan gaba zai iya kasancewa ’ya’yanmu ne ake kashewa haka.

Guardiola, wanda ɗan asalin kasar Spain ne, ya ce tun bayan fara yaƙi a Gaza duk lokacin da ya kalli ’ya’yansa uku, yakan tuna masa da halin da yaran Gaza suke ciki da kuma jefa tsoro a ransa sosai.

A baya-bayan nan a fagen ƙwallon ƙafa ba Guardiola ne  ya fara nuna rashin jin daɗinsa kan abin da ke faruwa a Gaza ba.

Idan za a tuna tsohon ɗan wasan Manchester United da Real Madrid David Beckham ya taba yin kira kan a tsagaita wuta a shafinsa na Instagram, inda ya ce dole Isra’ila ta dakatar da kisan yara a Rafah.

Kazalika shi ma tsohon kyaftin din Manchester United Eric Cantona ya taɓa nuna damuwarsa kan yadda duniya ta kawar da idonta dangane da abin da Isra’ila take aikata wa Falasdinawa.

Haka tsohon shahararren dan wasan Faransa ma ya taba bayyana abin da ke faruwa da kisan kare dangi a shafinsa na Instagram.

Daga bangaren wasan tseren motoci ma, zakaran gasar tseren motoci ta Formula One Lewis Hamilton ya taba cewa ba zai yiwu a shiru a zuba wa Isra’ila ido ba. Sannan Hamilton, wanda ya taba lashe Gasar Formula One har sau bakwai a tarihi, ya ce halin da yara suke ciki a Gaza yana da tayar da hankali matuka.

Sauran taurarin wasan kwallon kafa da suka taba nuna goyon bayansu ga Falasdinawa sun hada da Ousmane Dembele na PSG da William Saliba na Arsenal da kuma tsohon dan wasan Arsenal da Real Madrid Mesut Ozil da sauransu.

Sannan akwai dan kungiyar Mainz ta kasar Jamus Anwar El Ghazi wanda kungiyar ta sallame shi a bara bayan ya wallafa wasu sakonni da suka bayyana goyon bayansa ga Falasdinawa.

Sai dai ko bayan sallamar sa daga kungiyar, dan wasan ya  wallafa wani bidiyo inda ya ce babu gudu, babu ja da baya kuma zai ci gaba da nuna goyon bayansa ga Falasdinawan.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us