Zanga-zangar da tsofaffin ’yan sanda a Nijeriya suka gudanar a Abuja a farkon makon nan game da batun biyansu hakkokinsu bayan barinsu aiki ta kara fito da girman matsalar tsarin fansho na kananan ’yan sanda da ma wasu ma’aikatan kasar ke fuskanta.
Tsofaffin ’yan sanda suna korafin cewa abin da ake ba su a matsayin fansho da kuma giratuti bai taka kara ya karya ba.
Tsoffin ƴan sandan wadanda suka haɗu daga sassa daban-daban na kasar sun yi zanga-zangar ne a Abuja, inda suke buƙatar a tsame su daga tsarin fansho na karo-karo.
Yawancin tsofaffin jami’an tsaron da suka yi magana da manema labarai sun ce an biya su tsakanin naira miliyan daya zuwa kusan miliyan biyu a matsayin kudin giratuti kuma suna karbar tsakanin naira 20,000 zuwa 40,000 a matsayin kudin fansho bayan sun kwashe shekara 35 suna bauta wa kasar.
Masana da dama suna ganin babbar hanyar da za a inganta aikin dan sanda da tsarin fansho da giratutinsu shi ne gyara tsarin albashi, wato kamata ya yi ‘yan sanda su koma karbar albashi mai tsoka kuma giratutinsu da fanshonsu su zama suna da tsoka.
Masana na ganin ta hake ne kawai za a karfafa gwiwar wadanda suke aikin ta yadda hakan zai sa a ƙara sanya wa masu sha’awar aiki son aikin.
Sannan akwai wasu ma da suke ganin gyara albashi da fanshon ’yan sanda zai taimaka wajen rage matsalar cin hanci da karbar rashawa.
Masani kan harkokin tsaro Awwal Abdullahi Aliyu ya ce babbar hanyar gyara tsarin fanshon ’yan sanda ita ce ta hanyar bayar da fansho karkashin Police Pension Board kamar yadda ake da shi a fannin tsofaffin sojojin kasar da ake da Military Pension Board wannan tsarin yana biyan tsofaffin sojoji kai-tsaye ne.
Ya ce tsarin da ake da shi yanzu a bangaren tsofaffin ’yan sanda shi ne Pension Fund Administration, suna da irin nasu tsare-tsare ciki har da cewa sai mutum ya kai shekara kaza kafin zai karbi cikakken kudi ko da kuwa kudin nasa.
Sannan wannan tsarin ba ya biyan tsofaffin ’yan sanda kai-tsaye.