Dukkan rai sai ta ɗanɗani mutuwa! A ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 ne al’ummar
Nijeriya suka shiga yammaci da mummunan labari na rasuwar tsohon Shugaban Ƙasar
Muhammadu Buhari.
Haƙiƙa wannan mutuwa ce da ta kaɗa duk wanda ya ji ta, walau masoyi ko maƙiyin Buhari, duk da cewa an ji labarin jinyarsa a asibiti a Birtaniya mako kusan biyu da suka wuce.
Iyalan marigayin ne suka sanar da rasuwarsa a shafukansa na sada zumunta a ranar Lahadin, kamar yadda mai taimaka masa a yaɗa labarai, Garba Shehu ya sanya hannu kan sanarwar.
Sai dai ba su riga sun bayyana yadda jana’izarsa za ta kasance ba tukunna.
A yayin da ake ci gaba da jimami da ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban, TRT Afrika Hausa ta yi nazari kan wasu fitattun abubuwa bakwai da suka danganci Muhammadu Buhari, waɗanda tsawon zamani ba zai manta da shi.
Yaƙin basasa
Ba a haife ni ba kuma wataƙila ba a haifi da yawan masu karanta wannan maƙala ba, amma mun karanta tarihin yaƙin basasar Nijeriya.
A matsayinsa na soja, Buhari na cikin dakarun da suka fafata da na ‘yan-a-waren Biafra.
Bayan kammala yaƙin kuma ya ci gaba da zama sojansa har ma ya yi ta zuwa samun ƙarin horo a ciki da wajen Nijeriya da ma samun girma.
Shugaban Kasa sau biyu
Muhammadu Buhari wanda aka haifa a ranar 17 ga watan Disamban 1942, ya fara yi wa ƙasarsa ta Nijeriya hidima ne a matsayin soja, inda ya samu damar zama Shugaban Ƙasa har sau biyu.
Karon faro ya yi shugabancin ne a matsayin Shugaban Ƙasa na mulkin soja, daga 31 ga Disamban 1983 zuwa 27 ga Agustan 1985.
A karo na biyu kuwa, ya karbi ragamar mulkin Nijeriya a ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya, shekara 30 bayan mulkin soja da ya yi.
An zaɓi Buhari ƙarƙashin jam’iyyar APC bayan da ya kayar da shugaba mai ci Goodluck Ebele Jonathan a 2015.
Wannan zaɓe yana daga cikin mafiya tarihi da aka yi a Nijeriya, musamman ganin irin guguwar zaɓen Buharin da aka yi da kuma tashin hankalin da aka shiga na fargabar abin da zai faru idan “aka murɗe” zaɓen ya faɗi kamar yadda da yawa suka yi ta zargin za a yi.
Sai dai a wa’adin farko na mulkin nasa na farar-hula, ya yi ta fama da jinya inda ya dinga tafiya Birtaniya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce mai yawa a ciki da wajen ƙasar.
Ya sake tsayawa takara a 2019 bayan kammala wa’adin farko, kuma ya yi nasarar hayewa inda ya ƙare wa’adi na biyu a watan Mayun 2023.
Tun sannan ne kuma ya koma mahaifarsa Daura da zama, har sai a farkon 2025 ne sannan ya sake komawa Kaduna, inda dama a can yake zama kafin ya zama Shugaban Ƙasa.
Buhari da Obasanjo ne kawai shugabannin Nijeriya da suka taɓa yin mulki sau biyu, kuma dukkansu a matsayin soja da farar-hula.
Juyin mulki
Wani lamari na tarihi da ba za a manta Buhari da shi ba shi ne lamarin juyin mulki da ya shafe shi har sau biyu.
Ɗaya shi ne ya yi, ɗayan kuma shi aka yi wa.A watan Disamban 1983, Manjo Janar Muhammadu Buhari ya kasance ɗaya daga cikin jagororin juyin mulkin da ya kifar da
gwamnatin Jamhuriyya ta biyu ta Shugaban Ƙasa Shehu Shagari.
Wannan nasara ce ta kai Buhari ga ɗarewa mulki.Sai dai shi ma a watan Agustan 1985, sai aka tumɓuke shi daga mulkin ƙasar bayan wani juyin mulki da Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi masa.
Bayan nan kuma Buhari ya shafe shekara uku a tsare lokacin da shi kuma Babangidan yake mulkin ƙasar.
Yaƙi da Rashin Ɗa’a’
Wataƙila babban abin da tarihi ba zai manta game da mulkin Janar Buhari ba a zamanin mulkinsa na farko shi ne yadda ya ɓullo da shirin ‘War Against Indiscipline’, wato ‘Yaƙi da Rashin Ɗa’a’.
An ƙaddamar da shirin ne a watan Maris ɗin 1984 har zuwa watan Satumban 1985.
Maƙasudin shirin shi ne gyara tarbiyyar ‘yan ƙasa ta zamantakewa da sauran mu’amaloli, kamar hana zuwa wajen aiki latti da cin amana da sauran munanan ayyuka.
Farin jini
Idan na ce ba a taɓa samun wani Shugaban Ƙasa ko kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa da ya yi irin farin jinin Buhari ba na tabbata ba a za musa ba.
Shugaba Buhari ya kasance mai tsananin farin jini a wajen al’ummar Nijeriya musamman ma talakawa.
Farin jinin nasa ma ya fi shahara ne a lokacin da ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa na farar-hula musamman daga 2011 zuwa na 2015.
Da ya faɗi zaɓe a 2011 har wata tarzoma sai da ta tashi a yankin arewacin ƙasar, inda mutane suka ƙi yarda da sakamakon zaɓen.
A 2015 kuwa da ya ci zaɓe, tsabar bikin murna da mutane suka dinga yi sai da aka samu waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon wasa da ababen hawa da suka dinga yi ba ji ba gani.
Shi ne kuma ɗan takara ɗaya tilo da har kuɗin yaƙin neman zaɓe sai da mutane suka dinga haɗa masa.
Takarar Shugaban Kasa sau huɗu
Idan jajircewa sunan mutum ce, to ya kamata Muhammadu Buhari ya dinga amsa wannan sunan.
Yana daga cikin mutane ƙalilan da suka dinga neman mulkin Nijeriya a ƙarƙashin mulkin farar hula suna faɗuwa. Amma Buhari bai sare ba sai da ya samu.
Ya fara tsayawa takara ƙarƙashin Jam’iyyar ANPP a shekarar 2003 inda ya kara da shugaba mai ci a lokacin Olusegun Obasanjo, amma
ya sha kaye.
Ya tsaya a 2007 a ANPP tare da Umaru Musa ‘Yar’adua na PDP, Buhari ya sake shan kaye.
Buhari ya jajircewa ya ƙi sallamawa, ya sake tsayawa a 2011 a Jam’iyyar CPC, a nan ma ya sha kaye a hannun Goodluck Ebele Jonathan.
A karo na huɗu na tsayarwa takara, sai Allah Ya bai wa Buhari nasara inda ya lashe zaɓen a 2015 ƙarƙashin Jamiyyar APC.
A dukkan waɗannan lokuta da ya fadi zaɓe, sau uku yana danganawa da kotu amma ba a taɓa rushe zaɓukan an ba shi ba.
Shaidar rashin cin hanci
Wata shaida da aka yi wa Buhari ita ce ta gaskiya da rashin cin hanci da rashawa.
Har wani take ake masa da har a waƙa sai da aka sa, wato “Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya, sannu Buhari kai muke so Nijeriya.”
A matsayina na ‘yar jarida, na sha ji a bakunan mutane ciki har da masu adawa da shi cewa “mutum ne da ba ya cin hanci da rashawa kuma ba ya almundahana.”
Sannan aƙidarsa ta yaƙi da cin hanci da ya kaddamar tun a zamaninsa na mulkin soja ta sake fito da wannan hali nasa.
A lokacin mulkin sa na soja, Buhari ya yi ƙaurin suna wajen aniyarsa ta yaƙi da cin hanci da rashawa, inda aka riƙa kama mutanen da duk ake zargi da yin cin hanci a gwamnatin hamɓararren Shugaba Shehu Shagari, tun daga kan ministocinsa da jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa har ma da sarakuna.
An yanke wa wasu hukuncin daurin rai da rai, wasu kuma daurin zaman gidan yari na shekaru da dama, da makamantansu.
An kuma sake yi masa irin wannan shaidar a lokacin da ya riƙe shugabancin hukumar Petroleum Trust Fund ta Nijeriya lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.
Kazalika, badaƙalar da aka bankaɗo a farkon hawa mulkinsa na farar-hula, har ta dala biliyan biyu ta kuɗaɗen makamai a gwamnatin Jonathan, sakamakon wani kwamiti da Buharin ya naɗa don yin bincike, ta sake kankaro masa “martaba da mutunci a idon ‘yan Nijeriya”.
‘Kwanta lafiya Buharin Daura’
Da wadannan da ma wasu da dama, haƙiƙa tarihin Nijeriya kanta ba zai taɓa kammala ba sai da sunan Muhammadu Buhari a ciki.
Kuma na san mutane da dama ba za su manta da wani saƙonsa na Ƙaramar Sallar 2023 ba, wacce ita ce sallah ta ƙarshe da ya yi a matsayin shugaban Nijeriya.
Wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasar a lokacin, ta ambato Shugaba Buhari yana cewa: “Allah ya ba ni wata dama ta musamman ta yi wa kasar nan hidima.
“Dukkanmu ‘yan’adam ne, idan na ɓata wa wani yayin da nake yi wa ƙasa hidima, ina neman a gafarce ni.”
Muhammadu Buhari ya rasu ya bar mace ɗaya da ‘ya’ya takwas da jikoki da dama.