A wannan makon, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aike da sako mai karfi game da girmamar barazanar gobarar daji, a gida da waje.
Da yake jawabi a Ankara, a wajen taron Jaruman Kasa da ke Bisa Aiki, ya jaddada alhakin da ke kan ‘yan’adam da su kawar da afkuwar gobarar daji, inda ya bayyana kananan halayen ko oho da ke janyo ibtila’in.
"Yanayin na ƙara zafi; danshi yana raguwa, kuma kadawar iska ya kara karfi. A cikin wadannan yanayi, kunna wuta ko da a budadden fili da ke kusa da daji babban kuskure ne.
“Wannan ba sakaci ba ne kawai. Idan bai zama rashin kulawa ba, to wannan cin amana ne karara," in ji Erdogan a wajen taron.
Kalaman nasa sun nuna gaskiyar rikicin sauyin yanayi a duniya. Tun daga Turkiyya zuwa California, Girka zuwa Portugal, ana ƙara samun gobarar daji sakamakon ƙananan kura-kurai na ɗan’adam wanda cikin sauri ke rikiɗewa zuwa mummunar gobara.
Ga warwara da bayanai kan kananan kura-kurai gama-gari da ke janyo manyan gobara a duniya:
1. Filtar taba sigari da ake jefarwa
Jefar da filtar sigari da take da wuta a jikinta cikin ciyayi na daga hanyoyi mafiya sauki, kuma masu hatsari, da ke janyo gobarar daji.
A yankunan da ba a cika samun ruwan sama ba irin su California da kudancin Turai, irin wannan abu na janyo gobara sosai.
Cibiyar Hana Afkuwar Gobara, da ke ayyukan bayar da kariya da kashe gobara ta Amurka, ta fitar da wani rahoto da ke cewa sakacin mutane ne ke janyo mafi yawan gobara a kasar.
2. Wutar da ake kunnawa a wuraren shaƙatawa ko gashin nama
Ramukan wasan wuta da na gasa nama, da ake bari suna cin wuta kuma ba tare da sanya idanu a kansu ba, na zama musabbabin tashin gobara.
Hukumar Kula da Gobarar Daji ta Turai (EFFIS), wadda ke sanya idanu kan gobara ta hanyar amfani da tauraron ɗan’adam, ta ce mafi yawan wutar da ke kamawa a lokacin bazara na farawa ne daga wuraren shakatawa.
Hukumar Kula da Filayen Shakatawa ta Amurka ta yi haashen cewa kimanin kashi 85 na gobarar daji a fadin kasar na kama wa ne musabbabin ayyukan mutrane, ciki har da wutar da aka kunna a wajen wasan wuta da jefar da totuwar taba sigari.
A Turkiyya, an yi duba ga me ke janyo gobarar daji inda aka gano kona roba a gona, bola da ayyukan farauta, da taba sigari da ake jefarwa ne a kan gaba cikin dalilan da ke janyo gobarar.
3. Kona lambuna da kiraren gonaki
A Amurka da Turai, kona kiraruwan gonaki ya zama babbar matsala.
Hukumar Kare Muhalli ta Amurka ta yi gargadin cewa busasshen yanayi mai iska na iya mayar da irin wannan gobara ta zama mummuna, ta dinga yada hayaki a wurare masu yawa.
Manoman da ke kona kiraren amfanin gonar da aka girbe ko masu lambu da ke kona shara ba tare da taka tsantsan ba na iya haifar da gobara mai girma, cikin sauƙi, musamman a lokacin busasshen yanayi da iska.
Hukumar Tarayyar Turai ta bayar da ƙarin haske kan cewa sauyin yanayi ya janyo karuwar bullar wutar daji a duk faɗin Turai.
Hukumomin biyu sun jaddada cewa kone-kone ba tare da ƙimantawa ba a lokacin yanayi mai tsananin hadari na haifar da hatsarin bullar wutar daji musamman a yankunan Bahar Rum da sassan tsakiyar yammacin Amurka.
4. Lalacewar injina da ababen hawa
Injina da ababan hawa masu daukar zafo sosai na iya haifar da wutar daji.
Hukumar Kula da Gandun Daji ta Amurka ta yi karin haske kan muhimmancin kulawa da samar da tsaro a yayin amfani da injina don rage afkuwar gobara, duk da cewa mafi yawan gobarar dajin ba sa afkuwa saboda amfani da injina.
A Turai, a yayin da babu isassun bayanai, jami’an kula da muhalli na gargadin cewa yanayin zafi busasshe tare da zafin ababan hawa ko injina, na kawo hatsarin wutar daji.
5. Bukukuwan wasannin wuta
Wasannin wuta na yawan janyo gobarar daji a Turai da Arewacin Amurka.
Hukumar Tarayyar Turai ta bayar da shawarar a daina ayyukan karafa masu fitar da wuta ko walda a lokutan da ake fama da tsananin zafi.
A 2023, gobarar daji ta shafi hekta 500,000 a fadin Turai.
A 2014, wani mummunan lamari ya faru a Girka, inda wani wasan wuta da aka yi daga cikin jirgin ruwa ya janyo afkuwar gobarar daji a tsibirin Hydra, an kama mutane 13.
Gwamnan yankin ya bayyana damuwa tare da cewa zai dauki matakin shari’a, wanda ke bayyana mummunan sakamakon gobarar.
Domin magance wannan hatsari, Hukumar Tarayyar Turai ta jibge ma’aikatan kashe gobara sama da 650 a iyakokin Faransa, Girka, Portugal, da Spaniya kafin shiga lokacin danwutar ke kama wa a 2025.
6. Sare bishiyu da dazuka ba bisa ka’ida ba
Rashin kulawa ba yadda ya kamata ba, da sare bishiyu ba bisa ka’ida ba na busar da dazuzzuka, yana fitar da dazuzzuka ga idanuwan rana a iska.
A cewar Hukumar Samar da Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya, sauye-sauyen amfani da gonaki a yankin tekun Bahar Rum daga fadada aikin gona, yawon bude ido, da ci gaban birane sun sa dazuzzuka na fuskantar hatsarin gobara.
Sare bishiyu ba bisa ka'ida ba, yin kiwo, da ayyukan cigaba a bakin teku na lalata dazuzzuka da kuma kara hatsarin yiwuwar samun gobara.
Magance wadannan batutuwa na bukatar gamayyar tsare-tsare da zuba hannun jari don daidaita dazuzzukan da sauyin yanayi, wadanda suka shafi bangarori kamar gandun daji, noma, raya birane, ruwa, muhalli, tsare-tsaren amfani da kasa, ilimi, da yawon bude ido.
7. Matsalar hanyoyin rarraba lantarki
Layukan wutar lantarki masu matsala ko suka fado kasa sun haifar da mummunar gobarar daji a baya bayan nan idan za a iya tuna wa.
Hukumar Kula da Amfani da Kadarorin Jama'a ta California (CPUC) ta rawaito cewa yayin da hanyoyin lantarki suka zama kasa da kashi 10 cikin dari na musabbabin kamawar gobarar daji, amma irin wannan gobarar ta zama musabbabin rabin gobarar da aka samu a California.
Wutar Sansani a 2018, gobarar daji mafi muni a tarihin California, ta faru ne sakamakon lalacewar hanyar dako da rarraba wutar lantarki a lokacin da ake yin iska mai ƙarfi. Kayan mallakin kamfanin Pacific Gas and Electric (PG&E) ne, babbar cibiyar lantarki da ke Oakland.
Irin wannan matsalar da ta faru ta bayar da gudumnmawa ga ga afkuwar gobarar Edgewood a 2022, wacce aka gano ta afku ne saboda rashin isasshiyar sahhalewa da tantancewar hanyoyin lantarki, batun da aka nuna bukatarsa tun farkon 2016 amma ba a magance shi ba.
Daga baya an ci tarar PG&E dalar Amurka miliyan 7 saboda take dokoki da hakan ya janyo afkuwar gobarar.
Me ya sa batun ke da muhimmanci
Tunatarwar ta Erdogan na fito gaskiya karara: ‘yan adam ne ke janyo kusan dukkan wutar dajin da ke kamawa.
Hukumar Tarayyar Turai ta yi hasashen cewa kashi 96 na wutar daji a nahiyar na samo asali daga ayyukan da mutane ke yi.
Wadannan gobara na barazana ga zamantakewa, suna gurbata ingancin iska, da lalata gidaje da kashe mutane.
Ibtila’in da aka shaida a California, Turkiyya, Girka, da ma wasu wurare, a mafi ywancin lokuta za a iya hana gobarar afkuwa. Mafitar na bukatar babban aikin hadin gwiwa.