Daga Millicent Akeyo
Ku kalli wannan, a ce kana can gefen Tanzania a gangare, kana daga kai kana kallon babban Tsaunin Kilimanjaro da tarin dusar kankararsa da ta baibaye samansa tana jan hankalin mai kallo.
Idan abinci ne kake so, ku yi tunanin shinkafa dafa-duka ta Nijeriya dauke da kayan kamshi.
Watakila yin gaggawar zuwa wasa a kewayen Dalar Gyadar Pyramid na Masar ne abin da kake son yi da gani.
Ga ‘yan Afirka da dama, irin wannan dama ta gagare su, saboda wahalar neman bizar zuwa wata kasa a cikin nahiyar.
A yayin da Afirka ke fuskantar wahakar hada takardu, biyan kudade, da zaman jiran visa, matafiya da dama daga wajen nahiyar na samun damar zuwa Afirka babu visa saboda karfin fasfonsu.
Wannan rashin daidaito na nufin babban batu na ‘yancin yawo a Afirka, nahiyar da dokokin da suke tun mulkin mallaka suka dabaibaye.
Jan layin diflomasiyya
A 2013, Tarayyar Afirka ta fitar da wata manufa da shiri na shekaru 50; daga ciki akwai janye visa ga juna tsakanin kasashen nahiyar nan da shekarar 2018.
Idan wannan wa’adi buri ne da ake son cim ma, kokarin tabbatar da hakan ya ci tira. ‘Yan kasashe kadan - Kenya, Rwanda, Sychelles, Gambia da Benin - ne suka bude kofofinsu ga ‘yan Afirka ba tare da visa ba.
“Zai zama tilas ga wani ko waye daga kowanne sashe na duniya ya nemi bizar zuwa Kenya ba. Sannun ku da zuwa gida,” Shugaban Kasar Kenya WIlliam Ruto ya bayyana a yayin Bikin Ranar Jumhuriya a watan Disamban 2023.
Shugaban Rwanda Paul Kagame ya goyi bayan takwaransa na kenya a wajen Taron Biashara na Afirka a Kigali a watan Oktoban bara, inda ya yi kira da a bude iyakoki a matsayin jigon hadewar nahiyar waje guda.
“Me ya sa mutanen wata kasa ba za su je su shiga wata kasar babu visa ba a nahiyar? Meye matsalar? A karshe, mun amince mu ‘yan uwan juna ne kuma al’umma daya da ke da bukata iri guda,” in ji shi.
Tushen matsalolin
Batun kira ga janye biza ga juna a tsakanin kasashen Afirka na koma wa ga Babban Taron Berlin a tsakanin 1884 da 1885, a lokacin da ‘yan mulkin mallaka suka fitar da iyakokin kasashen Afirka, suka zana iyakoki ta ci barkatai da suka raba ‘yalai da al’ummu da juna.
Kusan karni guda da rabi baya, wadannan iyakoki na samun kulawa daga gwamnatocin Afirka fiye da koyaushe.
Masu nazari na cewa ya zma tilas kasashen Afirka suka rushe iyakokin da ‘yan mulkin mallaka suka zana tare da bayar da izinin kai komo gaba-gadi.
Hanyar samun alfanu
Kwararru sun ce rusa wadannan iyakoki na ‘yan mulkin mallaka ba wai alfanu yake da shi kawai ba - na da muhimmanci wajen samar da tattalin arziki marar iyaka inda kudi, basira da tunani mai kyau za su dinga kai komo ba tare da tsaiko ba.
“Wanzuwar biza a tsakaninmu na kassara mu ne,“ in ji Ruto a yayin da yake sanar da matakin Kenya na zama kasar da ‘yan Afirka ba sa bukatar visa idan za su ziyarce ta.
A yayin da mutane ba sa iya tafiye-tafiye, masu sana’o’i ba za su iya tafiye-tafiye ba, dukkan mu ne za mu yi rashi.”
Matakin Kenya na 2024 ya kawo daduwar masu yawon bude ido, inda adadin maziyarta da kudin shiga ya dadu sosai.
Cibiyar Binciken Yawon Bude Ido ta kenya ta bayar da rahoton cewa kudaden shigar da ake samu sun karu daga dala miliyan 620 zuwa dala biliyan 3.4.
Kasar ta Gabashin Afirka na da manufar jan hankalin ‘yan yawon bude ido miliyan biyar na da 2027, sama da miliyan 2.4 da suka je kasar a 2024, manufar da ke tilasta inganta kayan more rayuwa da saukaka hanyar shiga kasar.
A yayin da janye biza a tsakanin kasashen Afirka zai kawo hadin kai da habakar tattalin arziki, akwai kuma kalubalen da za a iya fuskanta.
Wasu kasashen za su yi gwagwarmayar fuskantar masu gudun hijira inda ma’aikata ke tafiya zuwa inda ya fi maiko.
Sai dai kuma, kwararru na cewa manufar janye biza na da muhimmanci da kyawu da za a ci gaba da kokarin dabbaka ta ta hanyar tattaunawa mai dorewa da tsare-tsare masu kyau.