Waɗanne ƙasashe ne suka mallaki makaman nukiliya?
SIYASA
5 minti karatu
Waɗanne ƙasashe ne suka mallaki makaman nukiliya?Daga farkon 2025 akwai kimanin makamin nukiliya 12,241 a duniya, in ji ƙwararru, waɗanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce su ne makamai mafiya hatsari a bayan ƙasa.
Majalisar Dinkin Duniya na jagorantar kokarin hana yaduwar Nukiliya da gwada harba ta. / Getty
17 Yuni 2025

Makaman nukiliya na samun sabuwar kulawa a yayin da ake gwabza yaki tskaanin Isra’ila da Iran. hare-hare ta sama da isra’ila ke kai wa Iran sun janyo jin kiraye-kirayen raba yankuna da rikici da kawar da makaman nukiliya.

Isra’ila, ƙasar da ke da makaman nukiliya, ta kai wa Iran hari a lokacin da ake tattaunawa kan shirin nukiliyan Tehran. Iran ta sha nanata cewar ayyukanta na nukiliya na zaman lafiya ne da amfanin jama’a.

Mene ne makamin nukiliya?

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce makaman nukiliya ne makamai mafi hatsari a bayan ƙasa.

Manyan abubuwan fashewa ne da ƙarfin fashewarsu ke janyo rusau da yawa da ma tasiri mummuna na tswon lokaci.

Makaman nukiliya na samun ƙarfinsu ne daga lantarkin da ke fita daga bam din atom, waɗanda ake samarwa daga makamashin plutonium-239 da uranium-235, kamar yadda ƙwararru suka bayyana.

Fashewar nukiliya na fitar da wata iska da duk abin da ke kusa da ita ke iya rugujewa.

Makamin nukiliya guda daya kawai na iya kashe dubunnan daruruwan mutane, kamar yadda Kungiyar Kawar da Makaman Nukiliya ta Kasa da Kasa (CAN) da ta lashe kambin Nobel ta bayyana.

“Makaman nukiliya ne mafi hatsari a bayan kasa. Guda daya na iya ragargaza dukkan gari, tare da yiwuwar kashe miliyoyin rayuka, da lalata muhalli da makomar rayuwar jama’a a tsawon lokaci. Hatsarin da ke tattare da wadannan makaman shi ne wanzuwarsu a duniya.” in ji Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Mai Fatutukar Kawar da Makaman.

Makaman nukiliya nawa ake da su a duniya?

Sau biyu kawai a duniya aka taɓa amfani da makaman nukiliya a yayin gwabza yaki - yayin kai harin bam kan biranen Hiroshima da Nagaski na kasar Japan da Amurka ta yi a 1945.

Ƙananan bama-bamai na nukiliya na zamani suna da ƙarfin fashewa sau 20 fiye da bam da ya lalata Hiroshima, a cewar ICAN. Wannan bam din ya kashe mutane kusan 150,000 cikin 'yan watanni bayan tashinsa a birnin na Japan.

Manyan ƙasashe suna ɗaukar makaman nukiliya a matsayin matakin tsaro na ƙarshe. Ana ɗaukar mallakar irin waɗannan makamai a matsayin garkuwa saboda tsoron ta’adin da zai iya yi ga wanda ya aka kai wa harin da wanda ya kai harin.

Mafi kusancin lokacin da duniya ta kusa shaida amfani da nukiliya shi ne a 1961, bayan wata arangama tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet. Tun daga wancan lokaci, ƙasashen gaba ɗaya sun amince cewa yaɗuwar makaman nukiliya matsala ce.

Kimanin makaman kare dangi 12,000 zuwa 13,400 ne aka bayar da rahoton cewa akwai su a duniya a yau, kuma an gudanar da gwaje-gwaje sama da 2,000 na nukiliya zuwa yau, a cewar ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya na kwance ɗamara.

Kasashen da suka mallaki makaman nukiliya

A yanzu haka Ƙasashen duniya tara ne ke da makaman nukiliya. Sune Rasha (5,459), Amurka (5,117), China (600), Faransa (290), Birtaniya (225), Pakistan (170), India (180), Isra’ila (90) Koriya ta Arewa (50).

Sun mallaki makaman nukiliya 12,241 ya zuwa farkon 2025, in ji Tarayyar Masanan Kimiyya na Amurka (FAS), inda Amurka da Rasha suke da kashi 87 na makaman nukiliyar da ake da su a duniya.

Mafi yawan ƙasashen da ke da makaman ba sa bayar da cikakken bayanai kan yawa da ƙarfin makaman nasu.

Sai dai kuma, adadin nukiliyar da ake da su a duniya ya ragu sosai daga 70,000 da ake da su a lokacin yakin cacar baki.

Kokarin raba duniya da makaman nukiliya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi kawar da makaman nukiliya ta hanyar shirin karɓe makaman daga hannun ƙasashe, amma har yanzu ba ta yi nasara ba. An ƙulla yarjeniyoyi da dama don hana yaɗuwar makaman nukiliya da ma gwada su.

Waɗannan yarjeniyoyi sun haɗa da Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Makaman Nukiliya (NPT) wadda ke da manufar hana yaduwar nukiliya da neman hanyoyin raba ƙasashe da makaman.

Ana yi wa yarjejeniyar kallon muhimmiya wajen hana yaɗuwar makaman nukiliya inda ake bi don tabbatar da aiki da ita. Hukumar Kula da Makamashin Atom ta Kasa da Kasa (IAEA) na da alhakin tabbatar da an yi aiki da yarjejeniyar.

Yarjejeniyar, da aka fara sanya hannu a kanta a shekarar 1998, ta fara aiki a 1970. Ya zuwa yanzu, kasashen duniya 191 ne suka sanya hannu tare da yin alƙawarin aiki da ita.

Sai dai kuma, wasu daga ƙasashen da ke da makaman nukiliyar ba su sanya hannu a kan yarjejeniyar ba. Su ne: isra’ila, da India da Pakistan, inda Koriya ta Arewa da ta sanya hannu da fari, ta janye a 2003.

Kasashen da ke da Nukiliya kuma suka sanya hannu a kan yarjejeniyar su ne: Amurka, Rasha, China, Faransa da Birtaniya.

Ma’ajiyar makaman nukiliya na lamushe kuɗi sosai don kula da ita. Ana hasashen ƙasashen da ke da makamakn nukiliya na kashe kusan dala miliyan 225 a rana kan turakun nukiliyar, in ji ICAN.

Masu suka na nuni ga cewa za a iya amfani da kuɗeɗen wajen inganta rayuwar jama’a.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us