FIFA 2026: Abin da ya jefa Nijeriya cikin barazanar rashin buga Gasar Kofin Duniya
WASANNI
4 minti karatu
FIFA 2026: Abin da ya jefa Nijeriya cikin barazanar rashin buga Gasar Kofin DuniyaTana kasa tana dabo ga tawagar Super Eagles ta Nijeriya, wadda ke neman damar zuwa Gasar Kofin Kwallon Kafa na Duniya na FIFA 2026, bayan kasar ta ƙare a mataki na huɗu a Rukunin C bayan buga wasanni shida.
A 2022 ma tawagar Nijeriya ta Super Eagles ba ta sama damar zuwa gasar Kofin Duniya ta FIFA ba da aka yi a Qatar. / Others
29 Maris 2025

A ranar 25 ga Maris tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke neman damar zuwa Gasar Kofin Kwallon Kafa na Duniya na FIFA 2026, ta yi canjaras da 1-1 a gida da kasar Zimbabwe.

Bayan wannan wasan da aka buga a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a Nijeriya, tawagar Super Eagles ta kare da maki 7, kuma tana mataki na hudu a rukunin C mai kasashe 6.

A rukunin, Afirka ta Kudu ce kangaba da maki 13, sai Rwanda mai biye mata mai maki 8. Kazalika ita ma Jamhuriyar Benin tana matsayi na uku da maki 8. Wannan ne ya sa Nijeriya ke matsayin na 4 da maki 7.

Cikin wasannin 6 da tawagar Super Eagles ta buga tun fara wasannin neman tikitin Gasar Kofin Duniyan, a wasa daya tal ta yi nasara, yayin da ta buga kunnen-doki a wasanni hudu, sannan ta yi rashin nasara a wasa daya.

Akwai tababa

Wasu masana harkokin wasanni suna ganin akwai tababa kan damar Nijeriya na kai bantenta a wannan rukuni, ganin cewa ban da wasan da kasar ta doke Rwanda da ci 2-0 a makon jiya, duka sauran wasanni biyar da ta yi ba ta yi abin a zo a gani ba.

Masana suna ganin idan kasar ba ta sake taku ba, to shakka babu tarihi zai sake maimata kansa.

Wato za a yi Gasar Kofin Duniya na 2026 a Amurka da Mexico da kuma Kanada, ba tare da tawagar Super Eagles ba, kamar yadda aka yi na shekarar 2022 a Qatar ba da ita ba.

Wani dan jarida kuma masanin harkokin wasanni, Malam Mansur Abubakar ya shaida wa TRT Afrika cewa tabbas yana da kamar-wuya Nijeriya ta samu damar zuwa wannan babbar gasa ta kwallon kafa wadda za a yi a badi.

Ya ce a halin yanzu akwai tazarar maki 6 tsakaninta da mai jan ragamar rukunin, wato Afirka ta Kudu.

Ko da yake masanin ya ce kai-tsaye ba za ka iya cewa kwata-kwata Nijeriya ba za ta samu cancantar zuwa gasar ba, saboda a yanzu nahiyar Afirka tana da gurabe 10 ne a gasar, sabanin gurabe biyar da ake ba ta a baya.

Hakan ya samo asali ne saboda yadda aka fadada gasar zuwa kasashe 48, maimakon kasashe 32 da aka saba yi da su a baya.

An faɗaɗa gasar FIFA

Malam Mansur ya ce daga Afirka idan aka dauki kasa daya wadda ta fi yawan maki daga kowane rukuni, zai zama ana da kasashe tara kenan da za su wakilci nahiyar a gasar. Saura gurbin kasa daya Kenan zai rage.

Daga nan, ya ce za a zabo wasu kasashe hudu wadanda suka fi yawan maki daga duka rukunnai 9, sai a hada su wasa kuma wadda ta fi yawan maki za ta samu gurbi daya tal da ya rage daga nahiyar.

A nan ne wasu suke ganin watakila Nijeriya za ta iya samun damar shiga gasar. Amma shi ma kafin ta samu wannan damar , sai ta sake gwada sa’arta ta zamo ta biyu a rukunin C, idan makinta ya karu.

Mataimakin Sakatare na Kungiyar Marubuta Labarin Wasanni reshen jihar Kano, Muzzammil Dalha Yola ya ce bai kamata Nijeriya ta fid da rai daga zuwa Gasar Kofin Duniya ba.

Sai dai masanin ya ce Super Eagles sai ta yi da gaske idan tana so ta je gasar a badi. Ko da yake ya ce idan ’yan wasan suka ci gaba da yin irin salon wasan da suka buga da Zimbabwe, to gaskiya yana da matukar wahala su kai labari.

Ya ce hakan zai zama wani abin kunya, saboda zai zama an yi gasar kofin duniya sau biyu kenan a jere, ba tare da Nijeriya ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us