Yadda makiyaya a Kenya ke gwagwarmayar rayuwa a yayin da ake fama da sauyin yanayi
AFIRKA
5 minti karatu
Yadda makiyaya a Kenya ke gwagwarmayar rayuwa a yayin da ake fama da sauyin yanayiKenya na sake farfado da kiwo don bayar da kariya ga rayuwa, ciyar da al’uma da dawo da dazukan da aka lalata, wanda ke janyo yankin na Afirka illatuwa daga sauyin yanayi.
Makiyaya a Kenya / AFP
10 Yuli 2025

Daga Pauline Odhiambo

Yayin da rana ke faɗuwa a wani yanki na arewacin Kenya, Lonyang'ata Ewoi na kallon yadda garken awakinsa ke yawo a kan ciyawa busasshiya da ba ta da ƙarfi.

Tsawon shekaru da dama, makiyayin mai shekaru 58 da iyalansa sun dogara kan dabbobi domin rayuwa.

A yanzu suna fuskantar al’amarin da kakanninsu ba su taba yin tunani zai afku ba; Ƙasar da ta rike rayuwarsu na lalacewa saboda tsanantar sauyin yanayi.

"Ba za a iya hasashen ruwan sama ba, ciyawa na bace wa, kuma cututtuka na kashe dabbobinmu." Ewoi ya fada wa TRT Afrika. "Idan babu abin da ya canza, 'ya'yanmu ba za su sami makoma a kiwo ba."

Halin da arewacin Kenya ke ciki ya yi kama da na sauran ƙasashe da yawa a nahiyar, inda mutane miliyan 270 ke dogaro kan dabbobi don abinci, samun kuɗi, da kuma raya al'adu.

A yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba kan filaye da gonaki da abubuwan more rayuwa, Kenya na bayyana a matsayin zakaran gwajin dafi wajen samun mafita mai dorewa.

A ranar 2 ga Yuli, wakilan kasashen Afirka 32 sun je Nairobi don halartar babban taro kan Shirin Samar da Abinci na Bai Daya.

Taron, wanda Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da Asusun Cigaban Aikin Noma na Duniya suka shirya, ya mayar da hankali ne kan sauya tsarin abinci wanda ake iya sabuntawa., mai inganci, mai juriya, mai tafiya tare da kowa kuma wanda ba ya gurbata yanayi.

Taron

Marialia Lucio Restrepo ta sashen samar da dabbobi da kiwon lafiya na FAO ta ce "Abincin da ake samu daga dabbobi na da matukar muhimmanci wajen gina jiki da jin dadin rayuwa, amma dole ne fannin ya bunkasa don samun daidaito tsakanin cigaba tare da dorewa, daidaito da kuma lafiya."

Ƙididdiga ta bayyana bukatar dake tilasta samar da sauyi cikin gaggawa.

Dabbobi ne ke fitar da kashi 62% na iskar gas din greenhouse a Afirka, musamman ma shanu. Cututtukan da ake dauka daga dabboi, karancin abincin dabbobi da rikice-rikicen d ake samu ne kan gaba wajen zama babbar barazana ga fannin.

Amma kamar yadda Kenya ke nunawa, ana iya samun akasin haka. Sassan da ba a kiwo a cikin su a kasar na sauƙaƙa matsin lamba kan a samar da filayen kiwo.

Michael Misiko, kwararre a fannin kare muhalli ya ce "Ya zama dole kayayyakin more rayuwa, kamar bishiyoyi, su hada kai da tsarin kiwon dabbobi don tabbatar da lafiyar muhalli."

"Kafa tsarin abinci mai juriya ta hanyar amfani da waɗannan hanyoyin na bai daya na iya zama mai sauƙi, amma suna da mahimmanci don dorewar tsarin," in ji shi.

Dabaru a fadin Afirka

A yayin da Kenya ta tsara hanyar neman mafita, wasu kasashe makota na neman hanyoyin yaki da wannan rikici na sauyin yanayi.

Tanzania na cakuda noma, kamun kifi da kiwon dabbobi, ta hanyar amfani da bawon shinkafa wajen samar da abincin dabbobi mai gina jiki.

"Irin wadannan hanyoyin na da muhimmanci wajen hada manoma da kasuwanni sayar da kayan gona da na dabbobi," in ji Ezekiel Petro Maro na Cibiyar Binciken Dabbobi ta Tanzania.

A gefen gabar kogin Neja, Najeriya na dawo da filaye da dazukan kiwo da cibiyoyin ciyayi na asali tare da karfafawa mata da matasa masu hannu a harkar noma gwiwa. Wannan wani bangare ne na manyan tsare-tsare da nufin dakile munanan tashe-tashen hankula da ake yawan samu a tsakanin makiyaya da manoma.

A yankin kudancin Afirka, Eswatini na maido da kadada 30,000 na ƙasar noman da aka watsar, inda ake samar da hanyoyin samar da abinci mai ɗorewa kuma da rahusa.

"Wannan aikin ba wai don samar da ingantaccen abincin dabbobi ne kawai ba, batu ne canza tsarin smar da da kuma daukaka drajar al'umomin karkara." in ji Thulani Owen Sibiya jami’i a ma'aikatar noma ta Eswatini.

Jigogin kawo sauyi

Matasa Masu Sana’o’in Cigaban Noma, wata kungiya mai zaman kanta da ke da manufar samar da tsarin noma bai bayar da abinci mai dorewa, na da ra’ayin cewa matakin da matasan ke dauka na iya kawo sauyi a fannin kiwon dabbobi.

“Manoma matasa na kawo sabon tunani da dabaru, daga kayan aiki na zamani zuwa ayyuka masu dorewa,” in ji kungiyar.

“Dole ne a saurare su saboda sun zama jigogin kawo sauyi wajen nusantar da duniya a kokarin nuna tirjiya, samar da tsarin kiwo bisa adalci da za a iya ingantawa.”

Mata ma na da muhimmiyar rawar takawa. A Ethiopia, mai samar da nonon shanu Alemnesh Teklu na fuskantar kalubale da ake samun irin sa a fadin yankin.

"Ba mu da abincin dabbobi mai inganci, kula da lafiyar dabbobi, da kasuwanni masu inganci. Mata kamar ni na aiki tukuru don ciyar da iyalanmu, amma muna bukatar tallafi mai kyau don ganin an samu dorewar kiwon dabbobi," in ji Teklu gyayin tattauna wa da TRT Afrika.

Ta gamsu da cewa matakan tallafin na iya yin tasiri. "Lokacin da ayyuka suka kai ga mata manoma, idan muka samu horo da tallafi, ba kawai tsira za mu yi ba. Muna bunƙasa. Dabbobinmu na iya ciyar da iyalanmu da kuma warkar da ƙasar."

Makiyaya irin su Lonyang'ata Ewoi na da kyakkawan fata ga alkwarin samar da cigaba mai dorewa a fannin kiwon dabbobi.

"Idan za mu iya maido da filyenmu da ke da ciyayi kuma mu nemo hanyoyin da za mu iya ciyar da dabbobinmu, yarana za su iya samun makoma a kyau a harkar kiwo," in ji ta.

Yayin da Kenya ke kan gaba tare da zama abin misali, sauye-sauyen tsarin kiwon dabbobi ba wai kawai game da dabbobi ko tattalin arziki ba ne; ya kuma shafi kiyaye hanyoyin rayuwa tare da saba wa da salon yanayi mara tabbas.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us