Daga Pauline Odhiambo
Fatima Ahmed, ta goya ‘yarta mai shekara uku, muryarta na rawa a yayin da take bayanin mummunan halin da suka shiga wanda ya tilasta ta barin garinsu na El Fashir a ƙasa tare da tsallaka iyakar Chadi a kafa.
“Sun kona kauyenmu. Sun kashe mijina,” ta fada wa TRT Afrika. “Mun yi tafiya a kasa tsawon kwanaki, mai cike da tsoro.
Wannan ne abin da ake ta samu a rikicin Sudan tun bayan fara fadan tsakanin Sojojin Sudan da mayakan RSF da aka fara a watan Afrilun 2023.
Fatima, daya daga cikin kusan ‘yan Sudan 20,000 da ke neman mafaka, mafi yawan su mata da yara kanana, da suka yi tururuwa zuwa gabashin Chadi a makonni biyun da suka gabata, sun guje wa rikici a arewacin Darfur.
Kwararowar ba zatan ta janyo cikowar mutane a garuruwa irin su Tine, inda kusana awanni 48 da suka gabata mutane 6,000 suka isa cikin sa.
Irin hare-haren da aka dinga kai wa fararen hula a arewacin Darfur musamman ma a El fasher ne ya janyo wannan gudun hijira zuwa Chadi.
Masu neman mafaka na fadin yadda ake kashe mutane da dama a sansanoni, kamar Zamzam da Abu Shouk. An kona gidaje kurmus, an kashe mazaje, an dinga yi wa mata manya da kanana fyade. An dora alhakin mafi yawan hare-haren kan mayakan RSF.
Mohammed Ibrahim, manomi dan shekara 45, da dingishi ya shiga Chadi yana fama da harsashi a kafarsa.
“Sun harbe mu a lokacin da muke gudu,” in ji shi, a yayin da ma’aikaciyar jinya ta Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka ke duba kafar. “Na ga yara kanana na fadowa daga motocin a-kori-kura. Wasu ba su iya tashi ba.”
Tawagar bayar da kariya ta UNHCR ta ce kashi 76 na wadanda suka zo sun fuskanci kwace kudi ko kaya, sata ko cin zarafi.
Akalla yara kanana 22 ne suka zo da rauni, akwai daruruwa da suka zo babu iyaye, iyalansu sun bata ko sun mutu.
Chadi da aka cika da mutane
Jama’ar yankunan Chadi sun nuna tsagwaron goyon baya ga makotansu da ke shan wahala, sun karbi bakuncin masu neman mafaka miliyan 1.3. Amma karbar bakuncin wadannan mutane a kasar da ita ma ke fama da nata matsalolin ba karamin lamari ba ne.
Halima Youssouf, mahaifiyar yara biyar a Tine, ta bayyana tsananin damuwa a yayin da take kallon masu neman mafaka na bin layin karbar abinci.
“Wadannan mutane sun sha wahala sosai, ta yaya za mu juya musu baya? Amma a kowace rana, yaranmu na cin abinci kadan ta yadda za mu taimaka musu da hatsinmu. Ruwanmu na karewa. Asibitocinmu na cika da jama’a,” ta fada wa TRT Afrika, muryarta cike da gajiyawa da tausayi.
Kalaman Halima na dauke da irin radadi biyu da jama’ar gabashin Chadi ke fama da su. A yayin da jama’ar suka marabci ‘yan gudun hijirar Sudan da karamci da kyautatawa, sun kusa kai wa ga matakin karyewa.
“Dukkan mu iyaye ne mata, ‘yan uwan mata baki daya,” in ji Halima, tana kallon wata mata ‘yar Sudan dauke da jaririnta da ke fama da karancin cimaka. “Amma idan babu wanda ya taimaka mana nan da nan, to za a wayi gari babu abinda za mu dinga rabawa.”
Wannan kalami irin sa ne a dukkan garuruwan da ke kan iyakar wadanda ke fuskantar karancin kayayyaki, tashin farashin kayan abinci da cika cibiyoyin kula da lafiya.
Matsalar dandazon jama’a
Kungiyoyin bayar da agaji na ta kokarin sauya wa masu neman mafaka matsugunai kamar zuwa Iridimi, inda UNHCR ta kai mutane 1,850 tun watan Afrilun da ya gabata.
Amma tare da kashi 20 kawai na dala miliyan 409 da ake bukata ga masu neman mfaka a Chadi, ma’aikatan agajin sun yi gargadi kan hatsarin da ke tafe.
A asibitin kan iyaka, likita Saida Abubakar na kula da marasa lafiya da masu fama da rashin abinci - yara da ba su da cimaka, iyaye mata da babu isasshen ruwa a jikinsu, marasa lafiya tsofaffi da ke faduwa saboda gajiya da rauni - kuma ga rashin kayan aiki.
“Ba mu da magunguna. Muna bukatar ruwan da za a ƙara wa mutane a jikinsu, da magungunan yaƙar cututtuka da ma komai,” kamar yadda ta fada wa TRT Afrika.
UNHCR na kiran gaggawa ga goyon bayan kasa da kasa kan rashin bayar da tallafi yadda ya kamata.
“Dole a kawo karshen hare-Hare kan fararen hula a Sudan, sannan a tabbatar da samar da hanya mai tsaro don ficewar wadanda ke son yin hakan,” in ji Magatte Guisse, wakilin UNHCR a Chadi.
“Dole ne kasashen duniya su kara yawan goyon baya don kare wa da taimaka wa masu rauni. Wannan na bukatar faruwa yanzu.”
A yayin da rana ke faduwa a Tine, Fatima na kallon ‘yarta na bacci a kan tabarma.
“Ba mu da wani abu da ya yi saura,” ta fada. ‘Amma a kalla muna raye.”
*An sauya sunayen ‘yan gudun hijirar da ba su kariya