Nazari kan jam'iyyar da Rabi'u Kwankwaso zai iya komawa a siyasar Nijeriya
SIYASA
3 minti karatu
Nazari kan jam'iyyar da Rabi'u Kwankwaso zai iya komawa a siyasar NijeriyaWani abu da mutane da yawa a arewacin Nijeriya suka mayar da hankali kai shi ne ɓangaren da madugun siyasar Kwankwasiyya zai karkata, wato Dokta Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano.
Rabi'u Musa Kwankwaso
22 Yuli 2025

‘Yan siyasa a fadin Nijeriya na ci gaba da shirye-shirye, da ƙulle-ƙulle, da kitsa dabarun tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 a wani salon yaƙi na in-ba-ka-yi-ba-ni-wuri.

Bangaren jam’iyya mai mulki na APC suna zawarcin manyan ’yan siyasa masu kafasiti, ciki har da gwamnonin jihohin jam’iyyun adawa, don karfafa damar su ta ɗorewa a kan madafun iko.

Su ma jam’iyyun adawa suna ci gaba da ƙarfafa haɗakarsu a sabuwar jam’iyyar da suka yi wa dafifi, wato ADC, bayan da ake ta ƙaurace wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Wani abu da mutane da yawa a arewacin Nijeriya suka mayar da hankali kai shi ne ɓangaren da madugun siyasar Kwankwasiyya zai karkata, wato Dokta Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano.

A halin yanzu, wasu rahotanni na raɗe-raɗin Sanata Kwankwaso ya riga ma ya koma jam’iyyar APC, kawai lokaci ake jira a sanar da hakan.

Wannan ikirari ya ƙara ƙarfafa ne bayan da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan jam’iyyar NNPP kuma ɗan jam’iyyar APC, yayin da yake jawabi a wani taro da aka yi a baya bayan nan.

Sannan a makon nan tsohon gwamnan na jihar Kanon ya halarci wani taron kan Tattalin Arzikin Gandun Daji a Fadar Shugaban Ƙasa, inda har wasu kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ce daga bisani ya gana da Shugaba Bola Tinubu a ofishinsa.

Sai dai wani na kusa da Kwankwaso ya shaida wa TRT Afrika cewa ba a yi ganawa tsakanin Kwankwaso da Shugaban Tinubu ba tukuna.

Wani abu kuma da ya sa mutane suke ta raɗe-raɗin cewa Kwankwaso na gab da sauya sheka shi ne, saukar da Abdullahi Umar Ganduje, tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma babban abokin adawar Kwankwaso a siyasa ya yi daga shugabancin riƙo na jam’iyyar APC, lamarin da wasu ’yan siyasa suke ganin yana daga cikin sharuɗɗan da mai yiwuwa Kwankwason ya gindaya wa Shugaba Tinubu idan har yana so ya koma APC mai mulki.

Masana harkokin siyasa kamar su Malam Kabiru Sa’idu Sufi, wanda yake koyarwa a fannin Kimiyyar Siyasa a Kwalejin Ilimi da Share Fagen Shiga Jami’a da ke Kano, na ganin cewa duka ɓangarorin biyu suna zawarcin babban ɗan siyasar ne saboda duk bangaren da ya same shi yana ganin zai iya samun ƙuri’u kimanin miliyan biyu daga Jihar Kano a zaɓen da ke tafe.

Sannan masanin ya ce akwai hasashen da ake yi cewa, tana iya yiwuwa Kwankwason ya koma jam’iyyar PDP musamman ganin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar, wanda hakan zai iya bai wa irinsu Kwankwaso damar yin rawar gaban hantsi a cikinta.

Sai dai Malam Sufi ya ce idan har Kwankwaso ya koma PDP, to abu ne da zai yi wa APC daɗi sosai, saboda wata dama ce da jam’iyya mai mulkin za ta samu kaso mai tsoka daga ɗumbin ƙuri’un Jihar Kano, amma masanin ya ce APC ba za ta iya yin wani kataɓus ba a Kano a zaɓen 2027, idan Kwankwaso ya koma ADC.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us