Shekaru tara ke nan tun lokacin da tankokin soja suka ratsa gadar Bosphorus kuma jiragen yaƙi suka buɗe wuta kan fararen hula a Turkiyya. Ranar 15 ga Yuli tana tuna mana da ranar da aka yi yunƙurin juyin mulki wanda ya bar tabo mai girma a zukatan al’ummar Turkiyya, da siyasa da diflomasiyarta.
Mutane 253, yawancinsu fararen hula, sun rasa rayukansu, yayin da sama da 2,000 suka jikkata, lokacin da suka tsaya tsayin daka don dakile yunƙurin wasu sojoji da suka bi umarnin kungiyar ta’addanci ta FETO. Wadannan sojoji sun zo da motocin yaƙi, suna harbi da bindigogi masu karfi kan ‘yan uwansu ‘yan ƙasa.
Duk wanda ya ke a birnin Istanbul, birni mafi girma a Turkiyya wanda ke dauke da manyan fadojin Daular Usmaniyya da kyawawan masallatai, zai iya bayyana faragabara da jiragen F-16 da ke tashi ƙasa-ƙasa suka haddasa, yayin da suke mugun gudu suna ratsa iska.
Amma duk da wannan tsoro, dubban mutane sun fito kan titunan manyan birane, ciki har da babban birnin Ankara, a matsayin nuna adawa da juyin mulkin. Yayin da ta bayyana cewa wasu sojoji suna kokarin kifar da gwamnatin da aka zaba ta dimokuradiyya, dubban ‘yan Turkiyya sun fito daga gidajensu da tsakar dare don nuna rashin amincewarsu da wannan yunkuri.
Sun yi gwagwarmaya a wurare masu muhimmanci a Istanbul da Ankara, suna fuskantar sojojin da suka yi tawaye a kan gadoji, da wajen ginin majalisa, da sauran wurare masu muhimmanci. Masu zanga-zangar sun yi amfani da duk abin da suka samu a hannunsu — duwatsu, da sanduna, har ma da takalma.
Bidiyon da aka ɗauka da waya masu tayar da hankali sun yaɗu a kafafen sada zumunta: an murƙushe wani farar hula da tankar yaƙi yayin da yake tsaye a gabanta; an harbe wata mace har lahira; jami’an ‘yan sanda, ciki har da mata, sun rasa rayukansu yayin da suke kare wuraren aikinsu da hedikwatarsu.
Masu shirya juyin mulkin sun yi harbi a ginin majalisa a Ankara, kuma sun yi yunkurin kashe Shugaba Recep Tayyip Erdogan, wanda ya tsallake rijiya da baya daga abin da da dama suka dauka ko dai yunkurin kisan kai ne ko kuma sace shi.
A makonni da suka biyo yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, masushigar da ƙara a Turkiyya sun tattara hujjoji da suka tabbatar da cewa shugaban kungiyar FETO, Fetullah Gulen ne ya shirya wannan cin amanar . Gulen ya rasu a shekarar 2024 a Amurka, inda ya rayu cikin jin dadi da walwala.
Mutane sun sauya.
Tarihin siyasar Turkiyya ya sha fama da juyin mulki da dama. An kashe shugaban farko da aka zaba a dimokuradiyya, tsohon Firaminista Adnan Menderes a 1961 bayan juyin mulkin soja na farko a kasar.
A shekarar 2016, sojojin sun fuskanci wani sabon nau’in jama’a — wadanda suka yi gwagwarmaya don samun murya ta dimokuradiyya kuma suka ga amfanin hakan ta fuskar ci-gaban tattalin arziki, da gine-gine, da hanyoyin karkashin kasa, da inganta sufuri. Turkiyya tana da abubuwa da dama da za a iya rasawa a daren 15 ga Yuli.
Duk da haka, tsayin dakan Turkiyya a lokacin wannan ƙalubale bai samu yabo daga wasu daga cikin abokan kawancenta ba — gwamnatocin da ba sa gajiya da tunawa da Mutumin Tanki na Dandalin Tiananmen sun yi burus da sadaukarwar fararen hula na Turkiyya.
Abokan ƙawancen Turkiyya na yammacin duniya, ciki har da ƙawaye na NATO, sun yi jinkiri wajen yin Allah wadai da juyin mulkin — wani abu da Joe Biden, wanda a lokacin shi ne mataimakin shugaban Amurka, ya amince da shi yayin ziyararsa a Turkiyya wata daya bayan yunkurin juyin mulkin.
Ga Ankara, wadda ta taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi da Daesh (ISIS) kuma ta dauki nauyin kula da miliyoyin ‘yan gudun hijirar Siriya, wannan shiru kan juyin mulkin da ya ci tura ya zama kamar cin amanar kawance ne.
A watanni bayan da juyin mulkin da bai yi nasara ba, yayin da masu shigar da ƙara da kotuna a Turkiyya suka fara gurfanar da masu juyin mulkin, wasu ‘yan majalisar Turai sun fara nuna damuwa kan hakkokin wadanda ake zargi. Wannan ya kara fusata shugabannin Turkiyya.
Amurka, wadda ita ce abokiyar kawancen Turkiyya tun bayan yakin duniya na biyu, ba ta yi wani abu ba don binciken Gulen, wanda ya ci gaba da zama a jihar Pennsylvania har zuwa rasuwarsa, tare da cibiyoyin kasuwancinsa a Amurka, ba a taba kalubalantar su ba.
A nata bangaren, Turkiyya ta ce ta bayar da dukkan hujjojin da suka wajaba ga Washington don fara shari’a kan shugaban FETO.
Duk da rashin goyon baya daga abokan kawancen yammacin duniya, mutanen Turkiyya sun nuna kwazo mai ban mamaki wajen kare dimokuradiyyarsu.
Ga miliyoyin ‘yan Turkiyya da suka tashi tsaye cikin wannan yanayi da mashi da abin misali don fuskantar sojojin da suka yi tawaye, sun aika da sako daya: wanda ke cewa ba za a sake ba.
Wannan maƙala an fara wallafa ta a shekarar 2021 kuma an sabunta ta don tabbatar da sahihanci da dacewa.