Kwanaki bayan Amurka ta kai hare-hare kan manyan cibiyoyin ayukan nukiliyar Iran guda uku, rashin tabbas ya dabaibaye batun uranium mai nauyin kilogiram 400 da aka inganta kashi 60 ɗinsa kuma aka adana a wuraren da aka bayyana, amma yanzu ba a san inda aka kai shi ba.
Duk da cewa jami'an Amurka cikin sauri sun yi iƙirarin rage ƙarfin makamashin nukiliyar Iran, masu sanya idanu na ƙasa da ƙasa da kuma masu sharhi a yankin suna zargin cewa mai yiwuwa an kwashe muhimman kayayyakin kafin harin da aka kai ranar 22 ga watan Yuni.
Idan ta tabbata, matakin zai haifar da sabbin tambayoyi game da tasirin hare-haren da kuma tunanin da ke tattare da su.
Alamomin da ke nuna an ɗauki matakai da wuri
Hotunan tauraron dan adam da aka dauka kwanaki kafin a kai harin sun bayyana wani abu da ba a saba gani ba a kusa da cibiyar nukiliya ta Fordow, Waje a karkashin ƙasa da ake yi wa kallon matsayin ɗaya daga cikin ingantattun na'urorin nukiliya na Iran.
A cewar kamfanin ɗaukar hoto mai zaman kansa na Maxar, hotuna da aka ɗauka ranar Alhamis sun nuna manyan motocin ɗaukar kaya 16 a jere a kan titin da ke kan hanyar zuwa kofar cibiyar ƙarƙashin kasa ta Fordow, tare da mayar da mafi yawan su waje mai nisan kilomita guda washegari.
A ranar Juma'a, kwanaki biyu gabanin harin na Amurka, sabbin manyan motoci da buldoza da dama sun isa kusa da ramin kansa - wata babbar mota ta tsaya a kusa da kofar shiga Fordow.
Ba a tabbatar da ainihin me aka yi a wajen ba.
Amma kuma Gidan Rediyo da Talabijin na Iran, kafar Yaɗa Labarai ta Jumhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) ta bayar da rahoto a ranar Lahadin da ta gabata cewa, an kwashe kayayyaki daga wuraren da aka kai harin tun kafin a kai shi, inda aka kai kayan nukiliyar zuwa waje mai tsaro.
Wurare guda ukun da aka kai wa hare-harn su ne - Fordow, Natanz, da Isfahan - duka an jefa musu manyan bama-bamai.
Iƙirarin Amurka da sabanin da aka samu
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa, duk da cewar harin da Amurka ta kai na da manufar lalata kayayyakin nukiliyar Iran, amma bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ruguza baki dayan cibiyoyin, yana mai cewa a maimakon hakan ya sanya shirin nukiliyar zama “koma baya".
Ya kuma nuna cewa Iran ta yi nisa da shirin nukiliya a yau fiye da yadda take kusa da shi awanni 24 da suka gabata.
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta ƙasa da ƙkasa (IAEA) Rafael Grossi ya tabbatar da cewa tawagarsa ta ga sinadaran da aka tara waje guda a tsakanin ranakun 10 zuwa 13 ga watan Yuni - kwanaki kaɗan kafin harin na Amurka.
Tun daga wannan lokacin, an toshe hanyoyin shiga wajen sarrafa nukiliyar na Iran, kuma hukumar ta nemi Tehran a hukumance da ta bayyana wurin da sinadarin uranium ɗin yake a yanzu.
A wani taro a Vienna, Grossi ya buƙaci Iran da ta bayar da haɗin kai don gudanar da bincike kuma ta bai wa IAEA damar tabbatar da cewa kayan na ƙarƙashin kariya.
Sai dai wasu shugabannin ƙasashen duniya ciki har da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov, sun soki tsarin ayyukan hukumar.
"Mun bincika sosai, amma ba mu samu komai ba," in ji Lavrov, yana mai bayyana matsayin hukumar ta IAEA da cewa Iran na ɓoye wani abu ne kawai saboda ba a same shi ba.
"Yanzu suna neman, 'Nuna mana inda yake,' ba tare da wani garantin cewa irin wannan muhimman bayanai ba za su bazu a duniya ba."
Hanyar da wataƙilia Iran ta bi wajen kwashe sinadaran
Kwashe makamashin uranium kilo 400 da aka sarrafa kashi 60 dinsa abu ne mai wahala, ba wai wanda ba zai yiwu ba. An zuba sinadaran a manyan tukwanen ƙarfe kuma aka ɗauke su zuwa wani waje ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.
Ƙwararru sun ce gogewar da Iran ta yi tsawon shekaru aru-aru wajen kauce wa sanya idanu, tare da ɗimbin hanyoyin sadarwa na ƙarkashin ƙasa ya sa irin wannan aiki ya zo cikin sauƙi.
Wasu na ganin ayarin motocin da aka gani a kusa da Fordow na iya kasancewa wani ɓangare na wannan yunkurin sauya ma’ajiyar sinadaran. Wasu kuma suna nuni ga an kwashe su ne a hankali da kadan-kadan kuma ɗaya bayan ɗaya.
Abin da ya rage na rashin tabbas shi ne ko uranium ɗin a yanzu na ajiye a wani waje mai tsauri, an binne shi a karkashin kasa, ko kuma an rarraba su awurare daban-daban da aka ɓoye. Ba tare da bayar da dama ga IAEA ba, ba za a tabbatar da ingancin wannan batu ba.
Batun nasarar da ake iƙirarin samu
Duk da cewa Washington na bayyana hare-haren a matsayin wani mummunan kutufo, ɓacewar kayan nukiliya mafi mahimmanci na Iran na jefa shakku kan labarin nasarar da aka ce an samu.
Wataƙila dai an lalata gine-gine, amma ƙarfin haɓaka nukiliya na Tehran na da alaƙa da kokarinta na kare manta da fasaharta.
Wani babban mai bayar da shawara ga shugaban addini na Iran Ali Khamenei ya tabbatar a ranar Lahadin da ta gabata cewa tarin uranium na Iran har yanzu yana nan daram duk da hare-haren da Amurka ta kai kan wasu cibiyoyin nukiliya guda uku.
"Ko da an lalata wuraren nukiliya, wasan bai ƙare ba, sinadaran da aka sarrafa, da ilimin cikin gida, da aniyar shugabanni za su ci gaba da wanzuwa," in ji Ali Shamkhani a wani rubutu da ya yi a shafin X.
Ta hanyar hana shiga da kuma ƙin bayyana inda kayan suke, Tehran na nuna aniyar ta ta ci gaba da kula da shirinta ba tare da la'akari da matsin lambar soji ba.
Ko an ɓoye su a ƙarƙashin kasa ko an kai su wajen da ba za a iya ganin su ba, sinadaran uranium na Iran ba sa wajen da ake magana a kai, kuma ba wanda takamaimai ya san a ina suke.