A lokacin da Aissatou Diop ta kai jaririnta na makonni shida, Amadou, zuwa wata cibiyar kula da lafiya a yankin Pikine na wajen birnin Dakar don karbar allurar riga-kafi ta farko, ta shirya fuskantar matsalar da ta saba da ita.
Sauran yaran matar duk suna yin kuka sosai a lokacin da ake tsikara musu allurar riga-kafi, wanda hakan ke sanya ta cikin fargabar sake koma wa.
Ba ta san cewa a wannan karon lamarin zai zama na daban ba. Inda tare da dauka daya na allurar, aka yi wa Amadou riga-kafin manyan cututtuka shida da ka iya kama shi.
“Na samu sauki da na ji ma’aikaciyar jinya na fadin cewa wannan sabuwar allurar riga-kafin ba za ta yi wa jaririna zafi ba,” Aissatou ta fada wa TRT Afrika a yayin da take rungume da jaririn nata. “A matsayin uwa, yana da sosa zuciya ka ga yaronka na tsala kuka saboda allura. A yanzu zai yi karfi saboda rashin ciwo ga kuma kariya.”
Saukin da Aissatou ta samu na bayyana irin iyaye a duk faɗin Senegal, inda gwamnati ta rungumi allurar riga-kafi ta hexavalent a cikin shirinta na riga-kafi na ƙasa a ranar 1 ga Yuli.
Gamayyar allurar, wanda ya maye gurbin allurori daban-daban na pentavalent da cutar shan inna da ake yi wa jarirai a baya, yana bayar da kariya daga cututtukan sarkewar numfashi, tetanus, tari, hepatitis B, Haemophilus influenzae type B (Hib) da kuma cutar shan inna.
Kwanciyar hankalin iyaye
Ga iyaye kamar Mamadou Fall, wanda 'yarsa a kwanan nan ta karbi allurar ta farko, canjin ba wai sauki da jin dadi ya kawo ba kawai, ya zama dadin rayuwa.
"A unguwarmu, mun ga yara suna fama da tari da cutar shan inna. Sanin jaririna ya samu aminci da ‘yar allura guda na kwantar min da hankali,” ya shaida wa TRT Afrika.
Maganin riga-kafi na hexavalent ya nuna wani ci gaba a cikin Shirin Faɗaɗɗen Tsarin riga-kafi na Senegal (EPI) saboda dalilai daban-daban, gami da kare jarirai da yawa da kuma rage damuwar iyayensu.
Yanzu haka jarirai za su karbi allurai uku na allurar riga-kafin cutar shan inna kafin watanni shida maimakon biyu, wanda zai karfafa garkuwar jiki sosai, duba ga bambance-bambancen cutar shan inna a Afirka.
Gabatar da magungunan kara kuzari a cikin watanni 15, bisa shawarwarin Hukumar Lafiya ta Duniya, yana tabbatar da kariya mai dorewa.
"Tun da farko, yara da yawa za su buƙaci asibiti don tsananin tari ko kamuwa da cutar Hib. Wannan riga-kafin na nufin ƙarancin ziyartar asibiti da rage yawan mace-mace," in ji Dr Fatoumata Fall, yayin tattaunwa da TRT Afrika. "Tana kawo sauyi sosai."
Shiri a tsanake
Gabatar da riga-kafin hexavalent na buƙatar shiri a sannu-sannu.
Kusan ma’aikatan kiwon lafiya 6,000 ne suka sami horo kan yadda ake sarrafa kwalaben da dole a ajje su a waje mai sanyi tsakanin darajar 2°C zuwa 8°C.
Marie Ndiaye, wata ma’aikaciyar jinya da ke bayar da alluran riga-kafi a gundumar Grand Yoff ta Dakar, inda ta ce ya zuwa yanzu sauyin na tafiya cikin sauki.
"Iyaye sun yi shakka da farko, suna tambayar dalilin da ya sa allurar riga-kafin ta zama ta daban," in ji Ndiaye.
"Amma da zarar mun bayyana cewa tana da aminci, mafi sauƙi kuma kamar yadda take da tasiri, sai su yarda da ita suna farin ciki. Yara suna kuka kadan, kuma iyaye mata na tafiya gida cikin murna."
Fitowar riga-kafin cutar hexavalent ta Senegal ya biyo bayan na Mauritania makwabciyarta. Gwamnatin Senegal ta bayar da gudunmawar kashi 20% na kudaden yayin da Gavi, the Vaccine Alliance kuma suka cika sauran kudin.
Tsarin yanki
Dr Ibrahima Sy, ministan lafiya da ayyukan jin dadin jama'a na Senegal, ya bayyana kaddamar allurar riga-kafin da wani muhimmin mataki.
"A tsawon watanni 18, ma’aikatanmu sun yi aiki tuƙuru don yin shirya wannan abu," in ji shi. "nan da shekarar 2030, muna sa ran kawar da kwantar da mutane2,300 a asibiti a kowace shekara, madalla ga wannan riga-kafin."
WHO da UNICEF sun taka muhimmiyar rawa a gangamin, suna bayar da horo, kayan aikin sanyaya alluran da kayan ilimantar da iyaye.
"Wannan ba kimiyya ba ce kawai; adalci ne. Kowane yaro, ko ma ina ne asalinsa, ya cancanci samun wannan kariya," in ji Dr Jean-Marie Vianny Yameogo, wakilin WHO a Senegal.
Tuni dai ayyukan na Senegal suka fara zaburar da sauran kasashe makwabta da suka hada da Cote d'Ivoire da Burkina Faso don amfani da irin wadannan sauye-sauye.
Amincewar da Aissatou ta yi cewa ana kare ɗanta ba tare da ya sha wahala sosai ba yana nuna amfanin da sabuwar allurar riga-kafi ta hexavalent ke yi ga lafiyar jarirai a yankin.
"Yanzu, zan iya gaya wa sauran iyaye mata: kada ku ji tsoro. Wannan allurar riga-kafi kyauta ce ga 'ya'yanmu," in ji ta.