Addadin waɗanda suka rasu dalilin mummunar ambaliyar da aka yi a wani garin kasuwanci a jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya ya kai 200 ranar Lahadi, in ji wani jami’in gwamnati.
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi da tsakar daren Alhamis ne ya janyo ambaliya mai muni a garin Mokwa, garin da ke da nisan kimanin kilomita 380 yamma da Abuja, wata matattarar kasuwanci da sufiri inda manoma a arewacin kasar ke sayar da wake da albasa da kuma sauran kayayyakin abinci ga ‘yan kasuwa daga kudu.
Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Mokwa, Musa Kimboku, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran AP sabon adadin waɗanda lamarin ya kashe ranar Lahadi.
Ya ce an dakatar da ayyukan ceto, saboda hukumomi ba sa jin za a sake samun ƙarin waɗanda suka tsira. Domin hana ɓarkewar cututtuka, jami’ai suna tona gawarwakin da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, in ji Kimboku.
Ambaliyar, wadda daya ce daga cikin mafi muni a tarihin Nijeriya cikin gomman shekaru, ta sa waɗanda suka tsira sun firgita kuma sun rasa yadda za su yi.
Tura mutane cikin kogi mai ƙarfi
Adamu Yusuf na shirin zuwa kasuwar Mokwa da safiyar Alhamis ne lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana ihun: ambaliyar ruwa.
Ruwa ya shafe kwanaki yana taruwa a bayan wani layin dogon da aka daina amfani da shi wanda ya bi gefen garin, kamar yadda mazauna garin suka shaida wa AFP.
Wannan ba shi ne karon farko da ruwan sama ke taruwa a bayan tudun lakar da layin dogon ke zaune a kai ba, amma zai kasance lokaci mafi hatsari cikin ‘yan shekarun nan.
Sauyin yanayi ya sa yadda yanayi ke sauya wa a Nijeriya ya yi muni sosai, amma a bayyane take cewa sauran wasu dalilai na mutane na da tasu rawar da suke takawa a matsalar.
Galibi dai ruwan ambaliya na bin magudanan ruwa ne ciki tuddai kuma su bi ta matsattun magudanai. Amma a wannan lokacin, shara ta toshe magudanan, lamarin da ya sa ruwa ya taru a bayan katangar lakar wanda daga baya ta faɗi.
Ambaliyar da ta biyo baya ta yi awon gaba da abubuwa a cikin garin, inda ta ɗaiɗaita garin cikin ‘yan sa’o’i. ‘Yan sa-kai da masu ba da taimakon gaggawa sun shafe kwanaki suna fama inda suka gano gawarwaki kimanin kilomita 10 daga wurin bayan ruwa ya tura mutane cikin kogin Kwara.
‘[Ban] taɓa ganin abu kamansa ba’
Yusuf na ƙoƙarin ceto iyalinsa ne kafin ambaliya ta kayar da shi, kuma ya suma. A lokacin da ya farka a asibiti, an sanar da shi cewa matarsa da ɗansa da mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwa – tara jumulla – [ruwa] ya share su. Gawa ɗaya kawai aka iya samowa. "Ban san wanda ya ceto ni ba," kamar yadda Yusuf, mai shekara 36, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.
Ya tsaya a inda gidansa yake a da yayin da mazauna garin ciki har da yara da ba su wuce shekara 10 ba suke tona ɓaraguzai domin neman gawarwaki.
Wari matsananci ya cika addabi wajen, warin da mazaunan garin ke cewa yana zuwa ne daga gawarwaki da ke ruɓewa a ƙarƙshin baraguzai. Gawarwaki da ƙududdufai sun cika da wurin.
Motar tonon ƙasa ɗaya tilo da ke aiki kusa da wurin ta mayar da hankali ne wajen tara manyan duwatsu domin ƙarfafa wata ƙaramar gada da ke wajen garin wadda ambaliyar ta lalata ta.
"Ban taɓa ganin abu kamar haka ba a rayuwa ta shekara 42 a duniya," in ji Adamu Usama, wani injiniya da ya ƙware a harkar gini wanda ya ce ya rasa surukai 10 a ambaliyar. Da ƙyar gidansa ya tsira.
"Mun ga ruwan na tafiya da mutane, amma ba mu iya ceto su ba, saboda ba mu iya ninƙaya ba."
‘Addadin waɗanda suka mutu zato ne kawai’
Kawanaki kafin bala’in ya afka wa Mokwa, Hukumar da ke Hasashen Yanayi ta Nijeriya ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambiliyar ruwa a jihohi 15 daga cikin jihohi 36 na Nigeria, tsakanin ranar Laraba zuwa ranar Juma’a ciki har da jihar Neja, .
Rashin isassun magudanan ruwa da gina gidaje kan hanyar ruwa da kuma zuba shara a magudanan ruwa na cikin abubuwan da ke ta’azara matsalar ambaliya a Nijeriya.
A shekarar 2024, ambaliya ta kashe mutum 321 a jihohi 34 daga cikin jihohi 36 na Nijeriya, in ji Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasar (NEMA). Ambaliyar Mokwa kaɗai a wannan shekarar tana barazanar janyo abinda ya haura wannan adadin mace-mace.
Zuwa ranar Lahadi Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Neja ta ce mutum 153 ne suka mutu, kuma an riga an binne dukkansu. Sai dai kuma mazauna garin sun jaddada cewa adadin mace-macen ya haura hakan, inda wasu bayanan ke cewa wadanda suka mutu sun haura 200.
"Duk wanda ya gaya maka cewa wannan shi ne adadin waɗanda suka mutu zato kawai yake yi," in ji wani mazuanin garin, Saliu Adamu, mai shekara 45.
Duk da cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce jami’ai tsaron suna ba da tallafi wajen ba da taimakon gaggawa, sojoji da ‘yan sanda ƙalilan ne aka gani a a wurin ranar Lahadi, kuma sun fi mayar da hankali ne kan rage cunkoson motoci da ya faru sakamakon lalacewar gadar.
Gadoji sun lalace
Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago, yana Saudiyya inda ya je aikin hajji. Mazauna garin sun ce mataimakin gwamnan, Yakubu Garba, ya ziyarci wurin. Mutane da yawa da suka rasa ‘yan uwansu da muhallansu har yanzu suna jiran taimako.
Ranar Asabar, mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja, Ibrahim Audu Husseini, ya ce an samu ƙarin mutum 11 da suka ji rauni tare da mutum 3,000 da suka rasa muhallansu a lamarin.
Ambaliyar mai ƙarfi wadda ta kankama cikin sa’o’i biyar ta shafi aƙalla iyalai 500 a cikin garuruwa uku a yankin, inda da ƙyar ake ganin rufin gidaje kuma ruwa ya kai kunkumin waɗanda suka tsira, kuma suke ƙoƙarin ceto duk abin da za su iya cetowa ko kuma su ceto wasu.
Husseini ya ƙara da cewa ruwa ya share hanyoyi biyu kuma gadoji biyu sun rufta. A wata sanarwar da ya fitar ranar Juma’a da daddare, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana ta’aziyyarsa kuma ya ba da umarnin ga masu ba da taimakin gaggawa su tallafa wa waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da matsa kaimi wajen ceto mutane.
Ana yawan samun ambaliyar ruwa a Nijeriya a lokacin damina. Wasu al’ummomi a arewacin Nijeriya suna fama da rashin ruwa na tsawon lokaci wanda sauyin yanayi ya ƙara muni, kuma ruwan sama mai yawa ya kan ja wo ambaliya a ɗan lokaci ƙalilan na damina. Amma wannan ambaliyar ta munanan a Mokwa, wani yanki na noma kusa da kogin Kwara.
Wani shugaban al’umma a Mokwa Aliki Musa ya ce garin bai saba da ambaliya ba.