Masu fafutuka suna son a sauya tsarin TikTok saboda gazawar shafin daga kare yara
KIMIYYA DA FASAHA
4 minti karatu
Masu fafutuka suna son a sauya tsarin TikTok saboda gazawar shafin daga kare yaraManyan masu fafutuka da kungiyoyin hakkin dan'adam suna cewa TikTok ya gaza kare matasa tare da son a sauya tsarinsa a duniya.
The TikTok logo is displayed on a mobile phone. / AP
5 Yuni 2025

Yayin da ake ci gaba da duba tasirin TikTok akan matasa, masu fafutuka da kungiyoyin kare hakkin ɗan’adam kan sha’anin intanet suna kira da a yi gyare-gyare masu zurfi don magance abin da suka kira gazawar tsarin yadda dandalin ke kare matasa.

Kiran nasu ya zarce yin gyaran fuska kawai, suna bukatar daukar nauyin doka da bayyana yadda tsarin abubuwan da mutane ke cin karo da su a shafin wato algorithm ke aiki, da kuma sake fasalin yadda za a dinga bai wa yara kariya.

Muhimmancin yin duba ga wannan damuwar ya ƙaru bayan kisan Sana Yousaf, wata ‘yar TikTok 'yar shekara 17 daga Pakistan, wadda aka harbe a ranar haihuwarta a Islamabad.

Wannan kisan ya ta da hankula a kafafen sada zumunta, inda aka nuna yadda matasa masu amfani da shafukan — musamman mata — ke fuskantar barazana ba kawai a intanet ba har ma a rayuwa ta zahiri.

Duk da cewa wannan bala’i ba shi da alaka kai tsaye da tsarin TikTok, ya ƙara matsa lamba a kan kamfanin don magance manyan matsalolin tsaro ga masu amfani masu rauni.

“Ya zama wajibi TikTok ya sauya tsarinsa daga na mai sa mutane su dinga nacinsa zuwa mai ba su kariya,” in ji Teresa Barrio Traspaderne, mai fafutuka ta ƙungiyar Amnesty International a kan kare hakkin yara da matasa a intanet , yayin wata hira da TRT World.

‘Matsalar tana cikin tsarin algorithm ne’

Babban abin suka shi ne yadda tsarin abubuwan da mutane ke cin karo da su yake a TikTok, wato algorithm, ta yadda yake jefa wa mutum abubuwan da zai kalla daidai da irin waɗanda suka dace da ɗabi’un masu amfani — abin da suke kallo, tsawon lokacin da suke dauka suna kallo, da kuma abin da suke mu’amala da shi.

Binciken Amnesty International ya gano cewa a kan samu abubuwa masu illa har ma a shafin da aka kirkira don kwaikwayon yara ‘yan shekara 13 kawai — ciki har da bidiyo da ke nuna ko ƙarfafa damuwa da cutar dai kai, da kashe kai — bayan awa biyar zuwa shida kacal a kan TikTok.

Amnesty na kira ga TikTok da ya: haramta tallace-tallace da aka nufa ga masu amfani ‘yan kasa da shekara 18 a duniya baki daya, dakatar da tsarin nuna wa yara abun da ya kamata su kalla da kuma kafa matakan kariya don hana tsarin algorithm daga ƙara yaɗa abubuwa masu illa.

“TikTok har yanzu bai magance matsalar tsarin algorithm ba sosai. Matakan da ya dauka suna da alaka da gyaran fuska ne kawai,” in ji mai magana da yawun Amnesty International.

Masana fasaha sun goyi bayan wannan damuwar. Bibhu Pattnaik, wani masanin dabarun dijital daga Amurka, ya jaddada bukatar yin gyare-gyare a matakin dandamali.

“Dole ne a aiwatar da tsauraran matakan sirri don kare yara, tare da rage tasirin algorithm a kan abubuwa masu illa,” ya shaida wa TRT World.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan’adam a fannin dijital suna kira da a ba da “tsaro ta hanyar tsari, ba kawai samun riba ta hanyar tsari ba.”

Nighat Dad, shugabar Digital Rights Foundation a Pakistan, ta ce TikTok da sauran dandamali makamantansa suna bukatar sake fasalin yadda suke kula da tsaro, musamman ga matasa da masu rauni.

“TikTok dole ne ya daina daukar cin zarafin jinsi a matsayin abin da ba za a iya kauce masa ba,” in ji ta. “Tsaro ta hanyar tsari, musamman ga mata da matasa, ya zama ginshiƙi — ba gyara na lokaci ba.”

Ta kuma jaddada muhimmancin sanya ido a kan bidiyoyin da ake samarwa da harsunan gida da al’adu, tare da kafa tsarin amsawa cikin lokaci don magance kalaman kiyayya da cin zarafi.

A ƙarshe, Dad ta ce, “Dole ne a koma daga tsarin gyara zuwa tsarin kariya mai zurfi da tsari.”

A yayin da wasu kasashe ke kokarin haramta ko takaita amfani da kafafen sada zumunta ga matasa, masu fafutuka suna gargadi cewa irin wadannan matakai na iya haifar da matsaloli maimakon magance su.

Duk da haka, TikTok na ci gaba da samun karbuwa, inda a shekarar 2024 ya samu karin masu amfani miliyan 100, wanda ya kawo jimillar masu amfani da shi zuwa kusan biliyan 1.6 a duniya.

TRT World ta tuntubi kamfanin TikTok don jin ta bakinsu. A martaninsa, TikTok ya ce yana bayar da kariya mai tsauri ga matasa idan aka kwatanta da manya, amma bai magance wasu damuwowin da kungiyoyin kare hakkin suka gabatar ba kai=tsaye.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us