Kalaman da shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi a jihar Benue mai cewa “ran dan-adam ya fi na saniya daraja” sun dauki hankalin ‘yan kasar, sakamakon yadda hakan ke nuna kamarin da rikici tsakanin makiyaya da manoma ya yi a wasu yankunan Nijeriya.
A daren Asabar 14 ga Yuni ne aka samu wani mummunan farmakin ‘yan bidinga a wasu garuruwan jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya. Kashe-kashen na baya-bayan nan sun auku ne a garuruwan Yelwata da Daudu da ke karamar hukumar Guma ta jihar.
Mabambantan rahotannin sun nuna cewa an rasa rayuka da suka kai 100, baya ga tarin wadanda aka raunata, da kuma gidajen da aka banka wa wuta. Sauran yankunan da rikicin kan shafa a jihar Benue sun hada da Naka, Apa, da Agatu.
Tun wayewar gari ranar Lahadi ne, wasu matasa suka shiga zanga-zanga kan neman a dauki mataki. An ga dandazon mutane a titunan Makurdi masu dauke da allunan da ke neman gwamnatin tarayya ta shiga lamarin da gaske don kare al’umma.
An samu karuwar zaman dar-dar a jihar ta Benue a shekarun nan, amma a baya-bayan nan rikicin tsakanin makiyaya da manoma da kuma tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai. Sannan akwai rikici tsakanin kabilar Tiv da Jukun akan iyaka da Taraba.
Shugaban darikar katolika ta duniya, Fafaroma Leo ya yi allah-wadai da rikicin, sannan ya yi addu’a ga rayukan da suka salwanta a Benue, yayin hudubarsa ta ranar Lahadi, inda ya ce abin ya shafi masu gudun hijira da ke neman mafaka a sansanin cocin Katolika na garin Yelwata.
Ita ma kungiyar makiyaya a Nijeriya ta Miyatti Allah, wato MACBAN ta yi tir da hare-haren da ke faruwa a Benue. Sai dai kungiyar ta nemi a guji dora alhakin rikicin kan Fulani makiyaya, da kuma munana wa kabilarsu zato.
Ziyarar Tinubu
Ranar Laraba kwana hudu da harin, shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar jaje jihar ta Benue, inda ya duba masu raunuka da ke jinya a asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Benue Makurdi
Yayin ziyarar tasa, Tinubu ya nemu Babban Hafsan sojin kasar, janar Christopher Musa da kuma dakarun kasar da su nemo maharan don a musu shari’a.
Ya kuma ba da umarnin gudanar da sulhu tsakanin bangarorin da ke artabu da juna, inda ya nemi gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia da ya kira taron tattaunawa da kafa kwamitin warware sabani da sasantawa don kawo karshen zubar da jini.
Shugaba Tinubu ya yi rokon zaman lafiya a jihar, kuma ya ja kunnen shugabannin al’umma da na siyasa su bar kalaman tunzuri,.
Sai dai da yake jawabi ga shugaba Tinubu, sarkin kabilar Tiv, Tor Tiv ya fada wa shugaba Tinubu cewa, harin ya wuce na jayayya, na “kisan kiyashi ne”.
Shi ma wani mai nazari da sharhi kan rikice-rikice a Nijeriya, malam Isa Sanusi, ya yi gargadin cewa ya kamata a yi bincike kafin a dora alhakin su waye suke kai hare-haren. Ya ce tabbas akwai rikici tsakanin makiyaya da manoma, amma yanzu abin ya wuce haka.
Matakan kai dauki
Wasu rahotannin sun ce shugaba Tinubu ya amince da kafa rigar shanu ta zamani a jihar ta Benue, don kawo karshen takun-saka tsakanin makiyaya da manoma, yana mai cewa Nijeriya na da isasshiyar kasar da za ta wadaci kowa da kowa, ba tare da an samu fadace-fadace ba.
Ita ma rundunar sojin Nijeriya ta sanar da fara amfani da jiragen sama don yin sintiri a samaniyar babban brnin jihar Benue, Makurdi da sauran sassan jihar.
Sannan a bangaren ‘yan sanda kasar, Babban Sufeton ‘Yan Sanda na kasa, Mr Kayode Egbetokun ya sanar da karbe ragamar kula da tsaro a jihar tare da tura runduna ta musamman don dakile rikicin.
Rashin hukuntawa
Sai dai sau da yawa, hukumomi da masu saka ido sukan dora alhakin hare-haren kan ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba. Sannan daga bisani ba za a ji labarin an hukunta wadanda aka zarga ba ko aka samu da laifi ba.
Wannan ya sa wasu masana da masharhanta kan tsaro a Nijeriya suna nuna damuwa kan rashin bin kadin wadanda aka zalunta. Har ta kai wasu na ganin dacewar gwamnati ta kafa dokar ta baci a yankunan da abin ya yi kamari.
Mal Isa Sanusi ya ce dole sai mahukunta da jami’an gwamnati sun fuskanci matsalar da gaske domin tabbatar da duk wadanda suke da hannu an hukuntasu, bisa doka. Ya ce “Ya kamata a saka sabbin dabarun kare kauyuka da inganta tsaro a karkara. Sannan a fuskanci matsalolin talauci da rashin adalci tsakanin al’umma”.
Da take yin tir da kashe-kashe a jihar Benue, Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN ta yi kira ga gwamnati ta dauki matakin gaggawa don dakile matsalar tsaro a yankunan kasar.
A wata sanarwar manema labarai da shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ya sanya wa hannu, kungiyar ta jajanta wa dangin wadanda abin ya shafa, inda ta ce hare-haren suna kassara iyalai da ta’azzara matsalar tsaro a kasa.
CAN ta kuma nemi gwamnati ta aike da dakarun da za su karfafi jami’an tsaro a yankin, domin kare al’umma da garuruwan da ke fama da rikicin, da maido da zaman lafiya mai dorewa.
Sa’annan ta yi da a yi bincike kan kashe-kashen, kuma sun jaddada bukatar yin adalci domin rusa kaurin sunan da masu aikata manyan laifuka suka yi, na kubuta daga hukuncin doka, wanda ke sanyawa suna ci gaba da cin karensu ba babbaka.