Miliyoyin ’yan Afirka sun tafka asarar makuɗan kuɗaɗe a wajen neman bizar shiga ƙasashe a nahiyar Turai a shekarar 2024, ba tare da samun bizar ba?
Jimillar kasashen Afirka 45 sun yi asarar yuro miliyan 60 wato kimanin dala miliyan 68 saboda yadda aka yi watsi da bukatar ba su biza ta neman shiga kasashen Turai.
Galibi ƙasashen Turai da ke ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) suna da tsarin biza ta bai-ɗaya da ake kira Schengen, wato bizaa guda ɗaya da ke bayar da damar shiga kusan galibin ƙasashen Turai.
Wani rahoto na State of Schengen Report na shekarar 2024 ya gano cewa kaso 41 cikin 100 na kudin shigar da nahiyar Turai ta samu daga buƙatocin biza ne da aka yi watsi da su.
Ba a mayar wa mutum kudin biza
Galibi kasashe ba sa dawo wa mutum kudin da ya kashe wajen neman biza, bayan sun yi watsi da bukatar neman neman bizar mutum, wato hakan yana nufin mutum ya yi asarar duka kudin da ya kashe kenan.
‘Yan kasar Aljeriya ne suka fi fuskantar matsalar rashin samun bizar Schengen, inda hukumomi a Turai suka yi watsi da bukatocin neman bizar ’yan kasar sau 185,000 cikin bukatocin neman biza 529,000 da aka nema.
Sauran ƙasashen da suka tafka asara mai yawa bayan da aka yi watsi da buƙatocin neman bizar ‘yan ƙasashensu su ne: Morocco da Masar da Nijeriya da Tunusiya da Senegal da Côte d’Ivoire da Ghana da Kamaru da kuma Kenya.
Laberiya ce kasar da za a ce wannan matsala ta ƙin bayar da bizar zuwa Turai bai shafa ba sosai, saboda cikin bukatoci 123 da aka gabatar na neman bizar, biza daya ce kadai ba ta tsallake ba wato aka yi watsi da ita.
Sannan akwai wasu kasashen Afirka da aka yi watsi da bukatar neman bizar Turai ta ’yan kasarsu wadanda duka-duka ba su kai guda 100 ba.
Kasashen su ne Mauritius da Sao Tome and Principe.
Kusan rabin adadin bukatocin neman bizar Schengen da aka nema daga kasashen Senegal da Nijeriya da Ghana an yi watsi da su ne. Kuma kowace daga cikin wadannan kasashe uku an nemi bizar Schengen sau 55,000.
Kungiyar Tarayyar Turai ta samu fiye da yuro 145 miliyan ko kuma dala miliyan 165 — daga bukatocin neman biza daga aka yi watsi da su daga sassan duniya daban-daban.
Mutum miliyan 2.6 daga Afirka
Akwai mutum kimanin miliyan 11.7 da suka miƙa bukatar neman bizar Schengen a duniya gaba daya a shekarar 2024, kuma mutum miliyan 2.6 ne suka yi hakan daga Afirka wato kaso 22 cikin 100 ke nan.
Daga cikin bukatocin neman bizar Schengen miliyan 1.7 da aka yi watsi da su a duniya gaba daya, 700,000 daga nahiyar Afirka ne.
Bizar Schengen tana bai wa mutanen da suka fito daga kasashe wadanda ba sa cikin Kungiyar Tarayyar Turai damar shiga kasashen kungiyar kuma mutum zai iya zama a Turai har tsawon kwana 90 a cikin watanni shida.
Kamar yadda EU ta bayyana akwai kasashe 29 da ke karkashin tsarin bizar Schengen.
Sannan yana da kyau a fahimci cewa ba a dawo wa mutum kuɗin da ya kashe wajen neman bizar Schengen idan bai samu ba.
‘Yan Aljeriya sun yi asarar kimanin dala miliyan 18 saboda da rashin samun bizar Schengen, daga nan sai kasar Morocco wacce ta yi asarar dala miliyan 11, sai kasar Masar wacce ta yi asarar dala miliyan biyar, sai kuma Nijeriya wacce ta yi asarar dala miliyan 4.9 da kuma Tunusiya wacce ita dala miliyan 3.6 ta yi asara.
Ghana ta yi asarar dala miliyan 2.4 ne yayin da ita kuma Kenya ta yi asarar dala miliyan 1.8.
Afirka ta Kudu ta yi asarar dala miliyan ɗaya, sai Uganda da ta yi asarar dala 621,000.
EU ta ce manyan dalilan da suke sanya ake hana mutane bizar Schengen su ne gabatar da takardu wadanda ba sahihai ba da rashin bayyana ainihin dalilin neman bizar da rashin isassun kuɗaɗe da takardun haihuwa ko na aure, waɗanda ba a tantance su ba, da kuma idan sun taɓa aikata wani laifi a baya.
Sannan sai kuma rashin nuna shaidar wurin da za su sauka a ƙasar da suke son zuwa.