Daga Mazhun Idris
Muhawara ta barke tsakanin masoya da masana kwallon kafa, kan batun kwallon fanaretin da aka soke a wasan Real Madrid da Atletico Madrid, wanda ya janyo cire Atletico daga gasar Zakarun Turai ta UEFA a bana.
Batutuwan da ake tafka musu kansu su ne, kalaman kocin Atletico cewa dan wasansu bai taba kwallo sau biyu ba balle a soke ta, da ikirarin golan Real Madrid cewa shi ya nemi soke kwallon, da batun cewa akwai wata na’ura a cikin kwallon da aka buga, da ma wasu batutuwa masu zafi da ake ta yin cecekuce.
Mafari
A maraicen ranar Laraba, 12 ga Maris ne Real Madrid ta je gidan makwabciyarta Atletico Madrid a karawarsu ta biyu cikin tagwayen wasan zagaye na ’yan-16 a gasar Zakarun Turai.
A karawar farko a makon da ya gabata a gidan Real Madrid, Rodrygo da Brahim Diaz sun ciyo wa Madrid kwallaye biyu, yayin da Julian Alvarez ya ciyo wa Atletico kwallo daya, inda aka tashi Real Madrid na da nasara da ci 2-1.
A wasan maimai din kuwa, Atletico ta samu nasarar zura wa Real Madrid kwallo tun a mintin farko na wasan, ta hannun Connor Gallagher. Sai a minti na 70 kuma, Madrid ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma sai Vinicius ya ɓarar musu.
Bayan nan, Madrid sun kasa ramawa har aka kare wasan, aka kuma cinye karin lokacin minti 30. Kasancewa jimillan sakamakon tagwayen wasan nasu ya kare ne da 2-2, an tafi bugun fenereti don fayyace wa zai wuce zagayen kwata-fainal.
Sai dai bayan bugun fanareti na biyu na Atletico, wanda dan wasansu dan asalin Argentina, Julian Alvarez ya dauka kuma ya ci, an samu takaddama kan cewa kafafuwansa biyu sun taba kwallon yayin buga ta.
Da’awar gola
Golan Real Madrid, Thibaut Courtois ya yi ikirarin cewa shi ya ankarar da alkalin wasa kan a binciki kwallon Alvarez. Kuma sai alkalan da ke duba kwallo a bidiyo, wato VAR suka shiga aiki. Bayan jinkirin dan lokaci, sai nan-take aka gano cewa kafafuwansa sun taba kwallon sau biyu.
Hakan ya sa aka soke kwallon, kuma a karshe aka kare fanaretin Real Madrid na da ci 4, Atletico da kwallo 2, wanda ya sa aka yi waje da Atletico, ita kuwa Real Madrid ta tsallaka gaba.
Daga bisani, Hukumar ƙwallo ta Turai, UEFA ta fayyace dalilan da ya sa alƙalan VAR suka soke ƙwallon da ɗan wasan Atletico ya ci. UEFA ta yi bayanin cewa ko da aka kalli bidiyon kwallon, ba a iya gane hakikanin abin da ya faru ba.
Amma da aka sake duba bidiyon da aka dauka daga bayan kafar Alvarez, an gano kafarsa ta hagu ta taba kwallo kafin kafar damansa ta buga, wanda ya sa shi zamewa kasa. Kuma an yi amfani da doka ta 14.1 ta UEFA wajen soke ƙwallon ta Julian Alvarez.
Sannan UEFA ta ce babu wata mitsitsiyar na’ura a cikin kwanson kwallon da aka buga a wasan (na’urar Chip), duk da cewa UEFA da ma FIFA suna amfani da wannan fasaha a gasannin Turai da na duniya. Wato dai VAR ne shi kadai ya janyo soke kwallon,
Da yake magana bayan wasan, golan Real Madrid, Courtois ya ce “Na lura da (Alvarez) ya taɓa kwallo sau biyu kuma na gaya wa alkali. Ba abu ne mai sauki ba ka gane hakan ba, kawai dai mummunar bakar kaddare ce ta hau su.”
Ƙorafin koci
Shi kuwa kocin Atletico, Diego Simeone ya hasala bayan wasan har yake korafin an zaluncie su, yana cewa, “Ban taɓa ganin sanda aka nemi VAR ya duba bugun fanareti ba,... Sam-sam! Kai ka ga sanda ya taɓa kwallon sau biyu?”
UEFA ta ce kyamarori 30 da ke filin wasan su ne suka taimaka wajen gano hakan.
Da ma dai an dade ana yi wa Real Madrid kallon mai ran-karfe a gasar Zakarun Turai, kasancewar da kankane gasar saboda ita ta fi kowa lashe kofin har sau 15.
Akwai wadanda kuma suke zargin hukumomin kwallon kafa da alkalan wasa suna Fifita Real Madrid a kan abokan karawarta, zargin da Madrid din ta sha musuntawa.
Sai dai kuma wasu suna ganin kawai kungiyar tana da yawan takar sa’a a gasar ne, inda take doke kungiyoyin da a zahirin sun fi ta ita taka leda.