Daga Pauline Odhiambo
Muryar Kadzo Mweu na rawa tana tuna mummunan yanayin da ta shiga a lokacin da take da ciki na biyu.
“Na kusa mutuwa fa,” mahaifiyar ‘yar shekara 32 ‘yar kasar Kenya ta fada wa TRT Afrika. “Bayan na haifi yarona na biyu, sai na fara zubar da jini sosai.
Ma’aikatan jiyyar duk suna kai komo, kuma ina iya ganin damuwarsu. Ban sani ba ko zan rayu na ga jaririna ya girma.”
A wajen Bayo Godwin, mahaifi mai shekaru 28 dan Nijeriya, har yanzu yana jimamin yadda matarsa ta mutu a hannayensa bayan ta haihu.
“Mun zaku sosai don marabtar jaririnmu na farko,” ya tuna da hakan. “Bayan haihuwar, matata ta fara zubar da jini sosai.
Asibitin ba su da isassun kayan aiki ko ajiyayyen jini don kubutar da rayuwarta. Ta mutu a lokacin da na ke rike da ita a hannayena ita kuma tana rike da jaririnmu. Na zama uba kuma bazawari a lokaci guda.”
Bayo da Kadzo ba su kadai ke jin radadin ba. Miliyoyin mata d aiyalansu a Afu=irka da wasu yankunan ma na shan wahala, da fuskantar rashin tabbas saboda matsalolin da ke zuwa tare da juna biyu musamman idan an zo gabar haihuwa.
Wani sabon bincike da aka gudanar a karkashin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya bayyana cewa tsananin zubar da jini da hawan jini ke suka fi jany mutuwar mata yayin haihuwa.
A 2020 kadai, zubar da jini da yawa da hawan jini kadai sun yi ajalin mutane 80,000 da 50,000.
Binciken da aka buga a mujallar The Lancet Global Health, an bayyana bukatar daukar matakan kare asarar rayuka da kula d amata masu ciki yadda ya kamata.
Rasa rayukan da za a iya kawarwa
Dr Pascale Allotey, daraktan sashen bincike kan jima’i d ahaihuwa a WHO, na da ra’ayin cewa ya kamata a kawo karshen mutuwar da ke da alaka da juna biyu, maimakon a ce tana ta afkuwa a duniya.
“Na fahimci me ya sa yake da muhimmanci a magance matsalar mutuwar mata da iyaye masu juna biyu,” in ji ta a wata sanarwar manema labarai a Ranar Mata ta Duniya ta 8 ga Maris.
“Wannan ba batu ne na lafiya kawai ba, batu ne na daidaito. Kowace mace, a ko’ina, na da hakkin samun kyakkyawan kula da lafiya, kafin haihuwa, yayin haihuwa da bayan ta haihu.”
A 2020, kimanin mata 287,000 ne suka mutu sakamakon cututtukan da ke da alaka da juna biyu, wand ake nufin duk minti biyu mutum guda na mutuwa. Zubar da jini ne musabbabin mutuwar kashi 27 na mutuwar, inda hawan jini kuma ya yi musabbabin mutuwar kashi 16.
Dalilan da suke janyo mutuwar
Binciken WHO ya yi karin haske da cewa kimanin daya bisa hudu (kashi 23) na mutuwa yayin haihuwa na da alaka da wasu cututtuka irin su HIV/AIDS, zazabin cizon sauro, karancin jini da ciwon suga.
Wadannan yanayi na kasancewa ta yadda ba a gan su ko kuma ba a maganinsu, sai su sake ta’azzara hatsarin da ake fuskanta a lokacin juna biyu.
Dr Jenny Cresswell, jami’ar kimiyya a WHO kuma daya daga wadanda suka rubuta rahitin binciken, ta yi karin haske kan alakar matsalolin da hatsarinsu.
“Yanayi irin na hawan jini ba iya hatsarin zubar jini yake janyo wa ba, yana kuma iya janyo ciwukan da ma suka wuce haihuwar. Domin tabbatar da cewa mata sun kubuta kuma sun samu lafiya, dole ne mu rungumi matakin kula da lafiyar mata masu ciki,” in ji ta.
Gibin kula da lafiya bayan haihuwa
Duk da irin muhimmancin da kula da lafiya bayan an haihu ke da shi, kimanin kashi daya bisa uku na mata a kasashe matalauta ba sa samun kulawar da ta kamata a kwanakin bayan haihuwa.
Wannan gibi na da ban tsoro matuka, saboda mafi yawancin rasa rayukan na afkuwa ne a wannan lokaci ko jim kadan bayan an haihu.
“Bayan na haifi jaririyata, na mayar da hankali kanta ta adda har na manta da lafiyata,” in ji Chiedza Chimbiri, wata uwa mai shekaru 25 ‘yar kasar Zimbabwe da ta fuskanci jijjiga bayan haihuwa. “Har sai bayan watanni na nemi taimako. Ya zuwa wannan lokacin na ji kamar na dilmiye.”
Taimakon lafiyar kwakwalwa abu ne da ake yawan mantawa da a wajen kula da lafiyar mata masu ciki ko bayan sun haihu.
Binciken WHO ya kuma bayyana cewa alkaluman kashe kai da mata masu ciki ke yi ya afku a kasashe 12 kawai a duniya, yana mai karin haske kan gibin ilmantarwa.
Dadin dadawa, ba kasafai aka cika samun mutuwa bayan haihuwa ba, irin a ce bayan shekara guda, duk da hatsari mai dogon lokaci da mata ke fuskanta.
Kira da a dauki mataki
A yayin martani ga wadannan kalubale, WHO ta kaddamar da wani kundi don aiki da shi a dukkan duniya, wanda ke dauke da tsare-tsaren da za a bi wajen kawar da dalilan da ke janyo mutuwa, inda kasashe 194 mambobin Gamayyar Lafiya na Duniya suka tabbatar da za su yi aiki don kula da lafiyar mata yayin haihuwa da bayan an haihu.
A yayin da ake jiran zuwan Ranar Lafiya ta Duniya ta 2025, da za a yi bikinta a ranar 7 ga Afrilu, gangamin da ake yi na kara haske kan lafiyar mata masu ciki da jarirai, wanda ya zo daidai da wa’adin shekaru biyar na shirin Dorewar Manufofin Cigaba.
Gangamin na bukatara dauki mataki a dukkan duniya don tabbatar da an samu ingantaccen kula da lafiya, musamman a kasashe matalauta da yankunan da ke fama da rikice-rikice.
“Muna bukatar kara zage dantse don kare rayuka,” in ji Dr Allotey. “Muna bukatar tabbatar da mata na iya tsira bayan haihuwa, tare da samar da damar kula da lafiya da za ta kawar da cututttukan kwakwalwa da gangar jiki.”
Sauyin da ake sa ran samu
Ga mata irin su Kadzo da Chiedza, hanyar samun waraka na tattare da kalubale da dama, amma labaran da suke bayyanawa na faranta rai.
“Ina son kowace mace ta samu damar rike jaririnta har ta ga girman sa,” Kadzo ta fada wa TRT Afrika. “Iyaye mata da dama na fuskantar hatsari, kuma na yi amanna da cewa bai kamata a ce wata ta rasa ranta ba yayin haihuwa a duniya.”
A wajen Bayo, yaki don lafiyar mata masu ciki abu ne da aiki kai. “Ba na son wani iyali su shiga yanayin da na shiga,” in shi. “Za a iya kawar da mutuwar matata. Da a ce asibitin na da kayan aikin da suka kamata, da tuni tana nan da rai. Muna bukatar kara zage dantse - don kula da iyaye mata.”