Shoshana Strook, wadda ‘ya ce ga Ministar Kula Filaye ta Isra’ila na zargin mahaifiyarta da cin zarafinta ta hanyar lalata da ita – haka kuma ta zargin mahaifinta da wani yayanta namiji da cin zarafin.
Shoshana ta yi wannan zargin ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, inda ta ce ta gabatar da ƙorafi a hukumance a ƙasar Italiya kuma tana jiran a yi mata adalci.
Bayan tsawon lokaci na shakku, matsanancin yanayi na tunani, da kuma tsarguwa, ina so na faɗi cewa na fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata daga duka iyayena da kuma ɗaya daga cikin ‘yan’uwana maza,” kamar yadda Shoshana ta rubuta.
Ta kuma yi iƙirarin cewa iyayenta sun yi wa ƙannenta uku maza lahani a jiki, kamar yadda ta bayyana: “Bayan shafe shekaru ina shan duka da kuma zama cikin tsarguwa, a ƙarshe na yi magana. Tuna hakan na da ciwo, amma ina buƙatar adalci.”
Yayin da Orit Strook ta shahara wajen yaɗa labaran ƙarya da kuma ikirarin da ba a tabbatar da shi ba na cewa kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi wa mutane fyaɗe a ranar 7 ga watan Oktoba, a yanzu tana fuskantar zarge-zarge na cin zarafin 'ya'yanta.
Ba a san Shoshana sosai ba, sakamakon rashin bayanzi game da ita a shafukan sada zumunta. Haka kuma ba a san dalilin da ya sa take son shigar da ƙararta a Italiya ba.
An taɓa ce-ce-ku-ce kan batun iyalin Strook a baya. A shekarar 2007, an taɓa zargin ɗan Orit Strook, Zviki Strook da yin garkuwa da wani ƙaramin yaro da kuma cin zalinsa.
Wace ce Orit Strook?
Mahaifiyar Shoshana, Orit Strook, an haife ta a cikin dangin Yahudawa na lauyoyin Hungary. Ta auri Avraham Strook, dalibin malamin addinin Yahudanci, kuma ma'auratan sun zabi zama a matsugunan da aka yi ba bisa ƙa'ida ba a kasar Falasdinu.
Gidansu na farko shi ne a unguwar Yamit da ke yankin Sinai. Duk da haka, bayan ƙaura daga Yamit a 1982 bayan da aka mayar da Sinai zuwa Masar a ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiya ta 1979, dangin Strok sun sake ƙaura zuwa Hebron-kuma, suna zaune ba bisa ƙa'ida ba.
Sakamakon daɗewa da suka yi a cikin harkokin ‘yan-kama-wuri-zauna, Orit Strook ta yi fice a matsayin shugabar matsugunan Yahudawa a Hebron.
Ta kuma kafa wata kungiya mai zaman kanta da ke tallafa wa matsugunan ba bisa ƙa'ida ba a Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, inda ta jagoranci kungiyar daga 2004 zuwa 2012.
Tun 2013, ta ci gaba da zama a mazaunin Avraham Avinu a Hebron.
Strook mamba ce a jam'iyyar Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi, ta kumaa ce manufarsu ita ce 'yantar da Isra'ilawa da ke tsare, da wargaza Hamas, da kuma kawar da Gaza a matsayin barazana ga Isra'ila.
Ita mamba ce ta Knesset mai wakiltar wata jam’iyya ta Yahudawa kuma mai goyon bayan matsugunan da suke ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar Falasdinu. Tsattsauran ra'ayinta ya ƙara fitowa fili, musamman bayan harin nan na ranar 7 ga Oktoba.
A cikin 2024, Strook ta bayyana cewa ya kamata Isra'ila ta ci gaba da kasancewa da "tsarin soji na dogon lokaci a Gaza tare da mamaye Yammacin Kogin Jordan". Ta kuma yi nuni da cewa bai kamata a kawo shirye-shiryen ficewa daga Gaza ba.
Strook ta jawo ce-ce-ku-ce bayan ta wallafa wani bidiyo a shafinta na sada zumunta daga zaman da aka yi na Knesset inda a nan ne ta ayyana cewa:
"Babu wani abu da ake kira al'ummar Falasdinu… Ba za a taba samun kasar Falasdinu a kasar Isra'ila ba, duk wani mutumin da ya san al’ada a duniya ya san cewa wannan kasa tamu ce, ta al'ummar Isra'ila kuma ta mu kadai."
Strook ta ƙara da cewa kafa ƙasar Isra’ila za ta kasance kamar “ƙarin barazana” ga Isra’ila da kuma barazana ga “zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.”
A watan Mayun 2024, ta yi adawa da shawarar da aka bayar ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wanda ya haɗa da musayar fursunoni.
Haka kuma Stook ta caccaki Amurka kan yunƙurin da take yi na diflomasiyya domin samar da zaman lafiya, inda ta ce “bai kamata a rinƙa kiran Amurka ƙawar Isra’ila ba”.
Tarihin cin zarafi a cikin iyali
Strook na da ƴaƴa 11 da kuma jikoki 12. A shekarar 2007, an gano wani yaro Bafalasdine jina-jina bayan an yi masa dukan tsiya inda ya gudo daga wurin da ake azabtar da si.
Sai daga baya aka gano cewa Zviki Strook da abokansa sun afka wata unguwa ta Yahudawa inda suka kama yaro mai shekara 15, suka buga masa ankwa tare da masa dukan tsiya inda ake zargin sun yi amfai da babbar mota domin kaɗe shi kafin suka bar shi a kwance.
Haka kuma ana zargin Zviki da kashe wata akuya sabuwar haihuwa ta hanyar amfani da ƙafa domin ƙwallo da ita. An same shi da laifi kan kai harin inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari a Israi’ila na kwanaki 30.
Bayan samunsa da laifi, Orit Strook ta kare ɗanta inda bayyana cewa:
“Ba kamar kotu ba, wadda ta yanke hukunci ta hanyar amincewa da shaidar da Larabawa suka bayar, muna da tabbacin cewa Zvi ba shi da laifi.”
Saƙon da Shoshana ta wallafa bai yi ƙarin haske kan ko wane ɗan uwanta take zargi da cin zarafinta, inda ta bar jama’a cikin duhu kan o Zviki ne ake nufi.