Ƙaruwar zubar da jini da ɗaiɗaita al’ummomi a jihar Plateau wani batu ne da ke faruwa jifa-jifa a yankin tsakiyar Nijeriya tsawon shakaru. Mazauna yankunan suna kokawa kan lamarin “da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa”.
Mutum fiye da 50 aka halaka a wani hari guda da ya faru da duku-dukun safiyar Litinin, 14 ga Afrilu.
Mahara masu ɗauke da makamai ne suka kai mummunan harin, sai dai ba a san su wa ye ba, duk da ana zargin maƙota ne abokan gaba.
A cewar hukumar ‘yan sanda da majiyoyi a yankin, waɗanda suka tabbata da faruwan lamarin ga manema labarai, harin ya faru ne a garin Zike da ke ƙaramar hukumar Bassa da ke kusa da Jos, babban birnin jihar Filato.
Baya ga waɗanda suka halaka, mutane “sama da 1,000 aka raba da matsugunansu, a cewar Joseph Chudu Yonkpa, babban kakakin wata ƙungiyar matasa ta Irigwe Youth Movement” wanda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ambato.
Gwamnatocin tarayya da na jihar sun yi tir da wannan ta’asa, inda suka sha alwashin hukunta masu hannu a laifin.
Rashin yin hukunci
Da take yin tir da wannan hari, ƙungiyar Amnesty International ta tabbatar da cewa maharan sun “cinna wa ƙauyuka wuta, suka wawashe dukiyoyi, sannan suka lalata duk abin da suka tarar”.
A wata sanarwar yaɗa labarai, inda ta yi kiran a yi bincike tare da hukunta masu laifi, Amnesty ta ɗora alhakin abin kan “yawan gazawar hukumomi wajen hukunta waɗanda ake zargi da laifukan, wanda shi ke janyo cigaban lamarin”.
A wata tattaunawa da TRT Afrika, daraktan Amnesty a Nijeriya, Malam Isa Sanusi, ya jaddada buƙatar a hukunta masu aikatawa da masu hannu a rikicin, saboda kawo ƙarshen maimaituwarsa.
Isa Sanusi ya ce, “Dole gwamnati ta bincika su waye ke da hannu a wannan tarzoma da kuma maharar da ke aikata hare-haren. Akwai zalunci ga mazauna karkara da ake bari cikin haɗarin hare-haren ‘yan bindiga ba tare da hukunci ba”.
Baya ga ɓarnata rayuwa da dukiyoyi, rikicin yana daɗa ƙazancewa, inda yake haifar da hare-haren ramuwar gayya, wanda ke ƙara muzgunawa waɗanda abin ya shafa rai, da kuma makusantansu.
A mafi yawan lokuta, rahotannin na nuna cewa waɗanda ke kai hare-hare ba ƙungiyar ‘yan bindiga ba ce guda ɗaya wadda ke da tsari da jagoranci. Yawanci, ba a sanin maharan, kuma babu ƙungiyar da ke ɗaukar alhakin hare-haren.
Masu nazarin rikice-rikicen sun yi amanna cewa akwai alamun cewa shirya hare-haren ake yi cikin tsanaki da tsari. Sai dai ba lallai a ce mutane guda ne ke aikata ta’asar ba a koyaushe.
Shiryayyiyar tarzoma
Tun faruwar Rikicin Jos na 2001, wanda ƙazamin rikice ne da ya faru a babban birnin jihar Plateau a Satumban 2001, masana sun yi nuni da daɗaɗɗiyar gaba da da ke tsakanin al’ummomi masu hamayya kan wariya wajen cin moriyar siyasa da tattalin arziƙi.
A shekarun da suka biyo baya, ƙarin yankunan jihar Plateau sun fuskanci tarzoma, musamman yankunan karkara da ke ƙananan hukumomin Riyom, Barikin Ladi, Langtang North, Langtang South, Shendam, Mikang, Qua’an Pan, da Wase.
Duk da ƙalubalen da ke da tushe a tarihi dangane da rikicin, masu bibiyar lamarin, irin su Dr Emmanuel Ivorgba, suna hangen akwai wasu alamu na sabon salon tarzoma a hare-haren kwanan nan.
Dr Ivorgba mai nazari ne kan rikice-rikice wanda ya kafa ƙungiyar sa-kai ta Centre for Faith and Community Development, wadda ta yi ayyuka da dama a jihar Filato.
Masanin ya ce, “Hukumomi kan bayyana tarzomar a matsayin wani faɗa tsakanin ɓangarori biyu, amma su al’ummar yankin sukan bayyana cewa hari ne shiryayye”.
Dr Ivorgba ya yi gargaɗin cewa, “Akwai babban rashin daidaiton fahimta tsakanin yadda hukumomi ke kallon lamarin, da yadda waɗanda abin ya shafa suke kallonsa”.
Da yake zantawa da TRT Afrika, masanin ya yi kiran gaggawa kan buƙatar gwamnati ta binciko masu ɗaukar nauyin tarzomar, ko ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane da ke biya da kuma bai wa mutane makamai don su far wa abokan faɗansu.
Masu lura da lamuran suna ba da shawarar nemo mafita ta hanyar yin duba kan yanayin rikicin da abubuwan da ke haifar da shi. Wajibi a mayar da hankali kan aiki tare da shuwagabannin al’ummomin yankin don inganta zaman lafiya.
Assasa zaman lafiya
Da yake jawabi kan nazarin da ya yi a baya kan rikice-rikice, Dr Ivorgba ya yi tir da masu yaɗa kalaman da ke ƙasƙantar da ɗan-adamtakar wasu mutane ta hanyar wofintarwa, da kawo rikici tsakanin mabambantan mutane da ke zaman lumana.
Ya yi gargaɗin cewa, “Matuƙar ba a warware matsalolin ba, wannan rikici zai iya ci gaba tsawon lokaci, inda zai haifar da hare-hare da ramuwar gayya wadda ba a san ƙarshenta ba”.
Masu ayyukan gina zaman lafiya suna da babbar rawar takawa wajen kyautata fahimtar juna, da magance damuwar al’ummomin da abin ya shafa, da kuma samar da sauyi nagari ta hanyar sauya tunanin mutane.